Kakakin Majalisa da Mambobi 15 Sun Shiga Gaban Gwamnan Taraba, Sun Fice daga PDP zuwa APC

Kakakin Majalisa da Mambobi 15 Sun Shiga Gaban Gwamnan Taraba, Sun Fice daga PDP zuwa APC

  • Jam'iyyar APC ta karbe ragamar shugabanci a Majalisar Dokokin Jihar Taraba bayan sauya shekar mambobi 16 a yau Litinin
  • Kakakin majalisar Taraba, Rt Hon. Kizito Bonzena, mataimakinsa, shugaban masu rinjaye da wasu yan majalisa 13 sun sauya sheka zuwa APC
  • Hakan dai ma zuwa ne kwanaki biyu kafin sauya shekar Gwamma Agbu Kefas, wanda zai bar PDP zuwa APC ranar Laraba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Taraba, Nigeria - Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba, Rt Hon. Kizito Bonzena, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulkin kasar nan.

Hakan dai na zuwa ne yayin da Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya gama shirin sauya sheka zuwa APC a hukumance ranar Laraba mai zuwa, 19 ga watan Nuwamba, 2025.

Majalisar Taraba.
Hoton kakakin Majalisar Dokokin Taraba, Rt Hon. Kizito Bonzena lokacin da ake sa masa hula mai tambarin Tinubu Hoto: Alex Anthony
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa sa'o'i 48 kafin wannan lokaci, shugaban Majalisar Taraba ya jagoranci yan Majalisa 15 zuwa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Sauya sheka: Sanata Ndume ya hango matsalar da za ta samu jam'iyyar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin 'yan majalisa 15 da suka shiga APC

Saura yan majalisar dokokin Taraba da suka bar PDP zuwa APC su ne:

1. Mataimakin kakakin majalisar dokokin Taraba, Hon. Hamman Adama Abdullai, mai wakiltar mazabar Bali 2

2. Shugaban masu rinjaye a majalisa, Hon. Jethro Yakubu, mai wakiltar mazabar Wukari 1

3. Hon. Tafarki Eneme, mai wakiltar mazabar Kurmi

4. Hon. Akila Nuhu, mai wakiltar mazabar Lau

5. Hon. Musa Chul, mai wakiltar mazabar Gassol 1

6. Hon. Josiah Yaro, mai wakiltar mazabar Wukari 2

7. Hon. Tanko Yusuf, mai wakiltar mazabar Takum 1

8. Hon. Veronica Alhassan, mai wakiltar mazabar Mazana Bali 1

9. Hon. Anas Shuaibu, mai wakiltar mazabar Karim Lamido 2

10. Hon. Nelson Len, mai wakiltar mazabar Nguroje

11. Hon. Umar Adamu, mai wakiltar mazabar Jalingo 1

12. Hon. Joseph Kassong, mai wakiltar mazabar Yorro

13. Hon. John Lamba, mai wakiltar mazabar Takum 2

14. Hon. Happy Shonruba, mai wakiltar Ardo-Kola

Kara karanta wannan

Nentawe: Shugaban APC ya fadi jihar da jam'iyyar za ta kwace a zaben 2207

15. Hon. Zakari Sanusi, mai wakiltar mazabar Ibi

Jaridar Leadership ta tattaro cewa duka 'yan majalisar sun mika takardar sauya sheka a hukumance a zaman majalisar dokokin na yau Litinin a Jalingo.

Me yasa suka bar PDP zuwa APC?

Kakakin majalisar Taraba ya bayyana cewa ya fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC ba don wata manufa ta kashin kansa ba, sai don maslahar jihar Taraba.

Hon. Bonzena ya roƙi magoya bayansa da kada su fassara matakin da wani tunani mara kyau, domin an dauke shi ne da niyyar gyaran jihar.

Tutar APC.
Hoton tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Getty Images

Ya bayyana cewa da wannan sabon ci gaban, dukkan ‘yan majalisar 24 yanzu sun koma inuwar jam’iyyar APC.

Tsohon Kakakin Majalisar kuma dan majalisa mai wakiltar Mazabar Mbamnga, Peter Diah, ya tarbi kakakin majalisar da sauran mambobin zuwa jam’iyyarsa, APC.

Gwamna ya sa lokacin komawa APC

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya kammala duk wasu shirye-shirya na sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Taron siyasa: Ƴan takarar gwamna, ƴan majalisun tarayya sun sauya sheka zuwa APC

Gwamna Kefas ya sanar da cewa zai fita daga PDP tare da shiga APC a hukumance ranar Laraba, 19 ga Nuwamba, 2025.

A cewar Agbu Kefas, wannan mataki da ya dauka na komawa APC ba don wani buri na kansa ba ne, sai don makomar al’ummar Taraba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262