PDP Ta Ƙaryata Shirin Kai wa Matawalle Hari, Ta Gargaɗi APC Ta Shiga Taitayinta
- Jam’iyya PDP mai mulki a Zamfara ta karyata zargin cewa tana shirin kai hari ga tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle
- Jam’iyyar ta ce labarin ƙarya ne da aka kirkira don tada hankalin jama’a da haifar da rikici yayin da Matawalle ke shirin ziyartar mahaifarsa
- PDP ta ce hankalinta yanzu yana kan babban taron zaben shugabanninta na kasa da za a yi a Ibadan, har ta zargi APC da shirya makarkashiya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara – Jam’iyyar PDP ta Jihar Zamfara ta karyata wani labari da ke yawo cewa tana shirin kai hari ga tsohon gwamnan jihar, Bello Mohammed Matawalle, yayin ziyararsa a Zamfara.
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Halliru Andi, ya fitar a ranar 13 ga Nuwamba, 2025.

Source: Original
Sanarwar da Halliru Andi ya wallafa a shafinsa na Facebook ta ce PDP ta bayyana cewa labarin ƙarya ne, kuma an kirkire shi ne da gangan domin rikita al’umma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta caccaki APC a Zamfara
A cikin sanarwar, PDP ta zargi APC da kokarin jawo rudanin da zai kawo tashin hankali da rashin zaman lafiya a jihar Zamfara.
Sanarwar ta ce:
“Jam’iyyar PDP ba ta da wani shiri ko niyya na kai hari ga kowa. Wannan zargi ƙarya ne tsagwaronsa da ake yadawa don bata sunan gwamnati da jam’iyyar."
Jam’iyyar ta bayyana cewa tun bayan hawansa mulki, Gwamna Dauda Lawal ya rushe duk wasu kungiyoyin ‘yan tawayen siyasa da tsohuwar gwamnati ta APC ta bari.
Haka kuma ta samu nasarar tsaftace siyasa tare da dawo da zaman lafiya da natsuwa a fadin jihar.
Kiran PDP ga APC da jami'an tsaro
Sanarwar ta ci gaba da cewa jam’iyyar PDP ta mayar da hankali kan babban taron zaben shugabanninta na kasa da za a gudanar a Ibadan a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, 2025.
Ta bayyana cewa shugabanni da wakilai daga Zamfara sun riga sun fara tafiya zuwa wajen taron domin a tabbatar da nasarar PDP.

Source: Original
Sanarwar ta kara da cewa:
“Maimakon yada jita-jita, ya kamata jam’iyyar APC ta kasance masu bin doka yayin tarbar shugabansu. Gwamnatin PDP ta jajirce wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar, kuma ba za ta lamunci komai da zai mayar da Zamfara baya ba."
Jam’iyyar ta kuma yi kira ga magoya bayanta da su guji daukar doka a hannu, su kasance masu bin doka da mutunta hukumomi.
Sai dai PDP ta bayyana cewa tana da sahihan bayanai cewa wasu daga cikin jam’iyyar APC suna shirin tura ‘yan daba don kai hari ga magoya bayan PDP a hanyoyin da za su bi zuwa Ibadan.
Saboda haka, PDP ta bukaci hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa don hana rikici ko barna.
Matawalle zai ziyarci Zamfara
A baya, mun wallafa cewa jam'iyyar APC ta yi wa PDP raddi mai zafi kan yadda ta nuna rashin jin daɗi game da ziyarar da ƙaramin ministan tsaro, Dr. Bello Mohammed Matawalle.
A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar APC a jihar, Malam Yusuf Idris, ya fitar a ranar Litinin a Gusau, ya zargi jam’iyyar PDP mai mulki a jihar da rikicewa saboda ziyarar.
Yusuf Idris ya yi watsi da bayanin da aka danganta wa mai magana da yawun PDP na jihar, Halliru Andi, wanda ya ce ya kamata Matawalle ya soke ziyarar tasa ya zauna a Abuja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


