APC Ta Samu Koma Baya, Magoya Bayanta Sun Koma NNPP a Kano

APC Ta Samu Koma Baya, Magoya Bayanta Sun Koma NNPP a Kano

  • Jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano ta samu tagomashi bayan wasu mambobin APC mai adawa sun sauya sheka zuwa cikinta
  • Mambobin na APC sun tattara komatsansu zuwa jam'iyyar APC ne a karamar hukumar Kibiya ta jihar Kano
  • Masu sauya shekar zuwa NNPP sun kuma bayyana dalilin da ya ja hankalinsu suka rabu da jam'iyyar APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Kwamishinan ma’aikatar jin kai da rage talauci na jihar Kano, Alhaji Adamu Kibiya, ya karbi mambobin jam'iyyar APC da suka sauya sheka zuwa NNPP.

Kwamishin ya karbi mambobin ne sama da 50 daga gundumar Kibiya da ke cikin karamar hukumar Kibiya, waɗanda suka bar APC zuwa NNPP.

Mambobin APC sun koma NNPP a Kano
Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda da Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Prof Nentawe Yilwatda, Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar jin kai, Balarabe Kiru, ya fitar a ranar Laraba a Kano.

Kara karanta wannan

Gwamna Caleb ya kammala shirin komawa APC, an ji abin da ya tattauna da Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishina ya tarbi mambobin APC zuwa NNPP

Alhaji Adamu Kibiya ya yi musu maraba zuwa NNPP, inda ya yi nuni da irin jajircewar Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen gudanar da jagoranci mai kyau.

Kwamishinan ya bayyana cewa Gwamna Abba ya aiwatar da muhimman ayyuka a fannin, lafiya, ilimi, ababen more rayuwa da noma domin amfanar mutanen Kano.

“Gwamna Abba Yusuf yana gudanar da ayyuka masu tasiri a fannoni daban-daban da ke amfanar da al’ummar Kano."
"Ku tabbata jam’iyyar NNPP za ta ba ku cikakken goyon baya, kuma ku ci gaba da jajircewa domin cigaban wannan gwamnati."

- Alhaji Adamu Kibiya

Meyasa suka fice daga APC?

Shugaban masu sauya sheka zuwa NNPP, Yakubu Alhaji, ya bayyana cewa sun koma jam’iyyar ne saboda gamsuwa da irin shugabancin da gwamnatin Gwamna Abba ke nunawa.

Ya kara da cewa APC ta kasa kawo ci gaba a yankin nasu tsawon shekaru takwas, inda ya zargi gwamnatin da ta gabata da yin siyasa ta son kai maimakon ta fifita bukatun jama’a.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Matakin da jam'iyyar PDP ke shirin dauka kan Nyesom Wike

Hakazalika, Kansilan gundumar Kibiya, Auwalu Sarki, ya bayyana cewa wasu kungiyoyi da dama suna shirin shigowa jam'iyyar NNPP.

Ya yabawa kokarin kwamishina Kibiya wajen tallata jam'iyyar da yada manufofin Gwamna Abba Yusuf a yankin.

Auwalu Sarki ya ce ayyukan da kwamishina Kibiya ke yi sun taimaka matuka wajen jawo sababbin magoya baya zuwa jam’iyyar NNPP.

Mambobin APC sun koma NNPP a Kano
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan siyasae Kano

'Yan NNP sun koma APC a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan jam'iyyar da ke cikin tafiyar Kwankwasiyya ne suka sauya sheƙa daga jam’iyyarsu zuwa APC a jihar Kano.

Masu sauya shekar sun ce dalilan komawarsu APC sun hada da nasarorin shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin wajen ciyar da kasa gaba.

Kara karanta wannan

Ziyarar Matawalle zuwa Zamfara ta tayar da kura tsakanin jam'iyyun APC da PDP

Hakazalika, sun bayyana cewa sun yanke shawarar rungumar APC ganin yadda jam'iyyar ke kara samun karɓuwa sosai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng