Bayan Komawa APC, Gwamna Diri Ya Magantu kan Tilastawa Mataimakinsa Dawowa Jam'iyyar

Bayan Komawa APC, Gwamna Diri Ya Magantu kan Tilastawa Mataimakinsa Dawowa Jam'iyyar

  • Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya yi tsokaci kan yiwuwar jawo mataimakinsa ya koma jam'iyyar APC
  • Douye Diri ya bayyana cewa yana tattaunawa da mataimakin nasa domin fahimtar da shi dalilinsa na komawa APC mai mulki
  • Gwamna Douye Diri ya bayyana cewa babu dadi yadda yanzu da shi da mataimakin nasa suka kasance a cikin jam'iyyu daban-daban

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya yi magana kan jawo mataimakinsa zuwa jam'iyyar APC.

Gwamna Diri ya bayyana cewa ba zai tilasta wa, Lawrence Ewhrudjakpo, ya koma jam’iyyar APC ba, duk da cewa shi ya bar PDP.

Gwamna Diri ya ce ba zai tilastawa mataimakinsa ba
Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri Hoto: Douye Diri
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron majalisar zartarwa ta jihar da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Yenagoa, a ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Gwamna Caleb ya kammala shirin komawa APC, an ji abin da ya tattauna da Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin gwamnan ya samu halartar taron majalisar zartarwar, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da labarin.

Diri na tattaunawa da mataimakinsa

Gwamna Diri ya ce duk da cewa abu ne mai wuya su kasance cikin jam’iyyu daban-daban, yana da tabbacin tattaunawar da suke yi za ta haifar da sakamako mai kyau.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Daniel Alabrah, ya fitar bayan taron, ya ambato gwamnan na cewa Ewhrudjakpo ya janye karar da ya kai a babbar kotun tarayya da ke Abuja don hana yunkurin tsige shi.

“A matsayina na wanda ke son zaman lafiya, na fi ganin tattaunawa da fahimtar juna fiye da rikici. Ba zan tilasta kowa ya shiga APC ba, amma zan rokesu su ga dalilin da ya sa muka yi hakan. Ina da iko yau, amma wata rana babu shi."

- Gwamna Douye Diri

Diri ya ba 'yan siyasa shawara

Gwamna Diri, wanda ya fice daga PDP a ranar 15 ga Oktoba, sannan ya shiga APC a hukumance a ranar 3 ga Nuwamba, ya bukaci ‘yan siyasa a jihar da su fifita hadin kai da ci gaban jihar Bayelsa maimakon rarrabuwar kai da gaba.

Kara karanta wannan

Kalu: Dalilin wasu 'yan majalisa na yunkurin tsige Akpabio daga shugabanci

Gwamna Diri ya yi kira ga 'yan siyasar Bayelsa
Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa Hoto: Douye Diri
Source: Twitter
“Lallai abu ne mai wuya gwamna ya kasance a gefe guda, mataimakinsa kuma a wani gefe daban. Amma za mu ci gaba da tattaunawa, wata kila mu hadu a jam’iyya ɗaya a gobe."
"Ba mu bukatar tada hankali a siyasar Bayelsa. Mun gama da tashin hankali. Mu ‘yan uwa ne, mu ɗaya ne. Ya kamata siyasa ta zama hanyar ci gaban jihar mu, ba hanyar gaba ba."

- Gwamna Douye Diri

Ya kuma gode wa jama’ar jihar Bayelsa bisa yadda suka yi tururuwa wajen taron shigar APC, yana mai cewa wannan goyon baya ya nuna cewa mutane suna tare da sabuwar tafiyar gwamnati.

Gwamna Diri ya yi wa Tinubu alkawari

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya yi wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, alkawari kan zaben 2027.

Sanata Douye Diri, ya yi wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu alkawarin samun kashi 99 cikin 100 na ƙuri’un jiharsa a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Matakin da jam'iyyar PDP ke shirin dauka kan Nyesom Wike

Hakazalika, Gwamna Diri ya ce burinsa shi ne haɗa kan ’ya’yan jam’iyyar APC a jihar domin aiki tare da gwamnatin tarayya wajen kawo cigaba ga mutanen Bayelsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng