'PDP Ta Mutu,' Fayose Ya Fadi Sunan Gwamnan PDP da Zai Koma Jam'iyyar APC a Arewa

'PDP Ta Mutu,' Fayose Ya Fadi Sunan Gwamnan PDP da Zai Koma Jam'iyyar APC a Arewa

  • Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce jam’iyyar adawa ta PDP “ta mutu murus” saboda rikicin cikin gida
  • Fayose ya zargi jam’iyyar da rashin shugabanci da hadin kai, inda ya ce manyan jagororin PDP sun tsere sun barta
  • Tsohon gwamnan ya kuma fadi sunan wani gwamnan PDP a Arewacin Najeriya da ya ce zai koma APC kwanan nan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana cewa babbar jam’iyyar adawa ta PDP “ta mutu” saboda tsananin rikicin cikin gida da rashin shugabanci nagari.

Fayose ya kuma yi hasashen cewa akwai gwamnan PDP a Arewacin Najeriya da zai sauya sheka zuwa jam'iyyar APC kwanan nan.

Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya ce PDP ta mutu, kuma ba za ta farfado ba.
Hoton tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose. Hoto: @GovAyoFayose
Source: Facebook

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a hirarsa da gidan talabijin din Channels a shirin 'Siyasa a yau' a ranar Talata, 11 ga Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

Amaechi ya ba 'yan adawa shawarar da za ta iya kawo karshen mulkin Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"PDP ta mutu yanzu,' - Ayodele Fayose

A yayin da ya ce jam'iyyar PDP ta shiga halin koma-baya tun da ta kasa warware matsalolinta na cikin gida, Fayose ya kuma ce:

“Shekara guda da ta gabata na ce PDP tana cikin matsala, kuma idan ba su nemi mafita ba da wuri, jam’iyyar za ta mutu.
"Yanzu jam’iyyar ta mutu murus. Tana ci gaba da fuskantar koma-baya, ba ta da rai kuma babu tsarin da zai iya ceto ta."

Ya kara da cewa ficewar manyan ‘ya’ya daga jam’iyyar da kuma rashin daidaito sun tabbatar da cewa PDP ta rasa karfi da tasirinta a siyasar kasar.

Gwamnan Filato zai koma APC

Rahoto ya nuna cewa jam’iyyar PDP na fama da rikicin shugabanci, ficewar gwamnoni, da rikicin rassa tun farkon shekarar 2025.

A bana kadai, jam’iyyar ta rasa gwamnoni hudu — Sheriff Oborevwori (Delta), Umo Eno (Akwa Ibom), Douye Diri (Bayelsa), da Peter Mbah (Enugu) — wadanda suka koma APC gabanin zaben 2027.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Matakin da jam'iyyar PDP ke shirin dauka kan Nyesom Wike

Fayose ya ce akwai gwamnonin PDP da za su koma APC kwanan nan
Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya gana da Shugaba Bola Tinubu a Abuja. Hoto: @GovAyoFayose
Source: Twitter

A kan wannan gabar, Fayose ya bayyana cewa:

"Shugaba Bola Tinubu ya mika gwamnan jihar Taraba ga shugaban APC na kasa. Gwamnan Filato zai fice daga PDP kwanan nan, bayan shi, wani gwamnan ma zai bar jam'iyyar."

Haka kuma rikicin tsakanin mukaddashin shugaban PDP na kasa, Umar Damagum da sakataren jam'iyyar, Samuel Anyanwu ya tsananta, inda kowanne daga cikinsu ke dakatar da magoya bayansa.

A watan Yuli, tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya fice daga PDP saboda rashin jituwa, kuma yanzu yana jagorantar hadakar 'yan adawa, karkashin ADC.

Fayose ya kuma yi tsokaci kan rikicin shari’a da ke rufe batun taron kasa na PDP, wanda kotun tarayya ta hana gudanawa a ranar 15 da 16 ga Nuwamba a Ibadan.

Fayose ya soki hukuncin kotun Oyo

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Mai shari’a Peter Lifu na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya dakatar da taron PDP a hukuncin da ya yanke kan karar da Sule Lamido ya shigar.

Kara karanta wannan

Damagum: Shugaban PDP ya fadi dalilin kin hukunta masu kawo cikas a jam'iyyar

A cikin karar, tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya koka kan cewa PDP ta hana shi damar sayen fom din neman shugabanci na jam’iyyar, wanda hakan ya saba wa doka.

Da yake yanke hukunci, Mai shari'a Lifu ya ce ya ce PDP ta karya dokokin da suka tsara yadda ake gudanar da irin wannan taro, tare da kin bin sharuɗɗan da doka ta tanada.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com