Amaechi Ya ba 'Yan Adawa Shawarar da Za Ta Iya Kawo Karshen Mulkin Tinubu a 2027

Amaechi Ya ba 'Yan Adawa Shawarar da Za Ta Iya Kawo Karshen Mulkin Tinubu a 2027

  • Tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi ya bukaci jam’iyyun adawa su tashi tsaye su shirya kafin babban zabe na 2027
  • Ya ce za a iya doke Shugaba Bola Tinubu a zaben mai zuwa, amma dole sai idan ‘yan ƙasa sun fito kwansu da kwarkwata
  • Amaechi ya ce NLC, ASUU ko NANS kadai ba za su iya ba, dole sai jama'a sun dauki nauyin kare dimokuradiyya da kansu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon ministan sufuri kuma tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, ya yi kira ga jam’iyyun adawa da su tashi tsaye kafin zaben 2027.

Rotimi Amaechi ya ce akwai bukatar 'yan adawa su jagoranci shirye-shiryen siyasa tun kafin zaben 2027, yana mai jaddada cewa za a iya kayar da Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun tarwatsa yunkurin sace jami'ansu da limamin addini a Abuja

Amaechi ya ce za a iya kayar da Tinubu a zaben 2027
Hoton tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da na Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Hoto: @ChibuikeAmaechi, @officialABAT
Source: Twitter

"Tinubu bai fi karfin a kayar da shi ba" - Amaechi

Tsohon ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a taron gyaran harkar zabe ta kasa da aka gudanar a Abuja ranar Talata, in ji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rotimi Amaechi ya ya yi gargadi kan rashin sha’awar siyasa da kuma raunin ƙungiyoyin farar hula da ake samu a tsakanin 'yan Najeriya.

“Cewa wai ba za a iya kayar da shugaban kasa ba, ba gaskiya ba ne. Na taba yin aiki da shi, kuma na san halinsa.
"Wasu na yayata jita-jitar cewa an riga an rubuta sakamakon zabe kawai don hana mutane su kada kuri'a. Amma a zahiri, idan mutane suka fito da yawa, babu wanda zai iya canja sakamakon zabe."

- Rotimi Amaechi.

Amaechi ya zargi 'yan siyasar Najeriya

Amaechi, wanda ya taba zama daraktan yakin neman zaben shugabancin APC, ya ce ‘yan siyasa da hukumomin gwamnati ne suka lalata tsarin dimokuradiyya a kasar nan.

Kara karanta wannan

"Za a iya kifar da shi": Amaechi ya hango hanyar kifar da Tinubu a zaben 2027

Ya bayyana cewa gyaran tsarin siyasa ba zai taba zuwa daga gwamnati kai tsaye ba, sai dai idan ‘yan ƙasa ne suka tashi tsaye suka nemi canji.

“Kada ku jira NLC — babu NLC yanzu. Haka ma ASUU da NANS, babu su. Idan kuna jiran gwamnati ta fara wani gyara, kuna bata lokacinku ne. Dole ne ‘yan ƙasa su jagoranci wannan tafiya."

- Rotimi Amaechi.

Ya kuma bayyana cewa, dole ne ‘yan Najeriya su tashi tsaye su nuna adawa ga duk wanda ba ya son tsarin zabe mai gaskiya da adalci, tun kafin zaben ya zo.

Amaechi ya ce za a iya doke Bola Tinubu idan 'yan adawa sun fara shiri tun yanzu.
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi. Hoto: @ChibuikeAmaechi
Source: Twitter

Tsohon ministan ya koka da yunwa

Amaechi ya nuna damuwarsa kan tashin farashin kayayyaki da karancin abinci, yana mai cewa talauci da yunwa sun zama gama gari tsakanin masu kudi da talakawa.

Ya ce:

“Na taba cewa ‘yan Najeriya suna cikin yunwa. Idan ba su da yunwa, ni ina da yunwa. Amma shin ba kowa ne ke fama da yunwa yanzu ba, a fadi gaskiya fa?”

Jawabin Amaechi ya biyo bayan maganar tsohon gwamnan Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, wanda ya ce Tinubu ba zai fuskanci babban kalubale a 2027 ba.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi arangama da 'yan ta'adda a Borno, an kubutar da mutane 86

Burin Amaechi na yin takara na nan

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan burinsa na yin takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ba gudu ba ja da baya, a yunkurinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027 karkashin inuwar jam’iyyar ADC.

Ya jaddada cewa dole ne zaben fidda gwani na ADC ya kasance an ba kowa dama, inda ya kara da cewa ba zai janye wa kowanne ɗan takara ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com