Reshe Zai Juye da Mujiya, Gwamna Mai Ci Ya Zargi ’Yan Adawa da Sake Kudi a Zabe
- Gwamna Charles Soludo ya yi magana yayin da ake gudanar da zaben jihar Anambra a yau Asabar 8 ga wata Nuwambar 2026
- Soludo ya zargi wata jam’iyyar adawa da sayen ƙuri’u da makudan kudi, yayin da yake nuna kwarin gwiwa kan nasarar APGA
- Farfesa Soludo ya ce an samu ƙalubale da na’urar BVAS a wasu wurare kamar Olumbanasa da Nnewi ta Kudu a Anambra
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Awka, Anambra - Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya zargi wata jam’iyyar adawa da sayen ƙuri’u a zaɓen gwamna.
Gwamna Soludo ya nuna damuwa kan matsalar a zaben da ake gudanarwa a jihar yau Asabar, 8 ga Nuwamba, 2025.

Source: Facebook
Gwamna Soludo ya koka kan sayan kuri'u
Soludo ya bayyana hakan ne bayan ya kada ƙuri’arsa tare da matarsa a mazabarsa ta 'Ofiyi Square', Isuofia, cikin karamar hukumar Aguata da misalin ƙarfe 1:25 na rana, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana kwarin gwiwa cewa zai lashe zaɓen idan aka bi dokokin zaɓe da ka’idojin INEC, yana mai cewa rahotanni daga wurare daban-daban sun nuna cewa APGA na kan gaba a ƙananan hukumomi 21 na jihar.
Gwamnan ya ce an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali, sai dai wasu matsaloli sun taso a wurare kamar Olumbanasa.
Ya tabbatar da cewa na'urar BVAS ta samu tangarda a Nnewi ta Kudu, inda ake zargin ana sayen ƙuri’u tsakanin ₦15,000 zuwa ₦20,000 ga kowanne mai zaɓe.
Soludo ya kuma zargi wani ɗan takara da yin ƙoƙarin sayen jami’an zaɓe, domin kada su tura sakamakon kai tsaye, a maimakon haka su musanya da rubutaccen sakamakon ƙirƙira.

Source: Twitter
Obi ya fusata da sayan kuri'u
A gefe guda, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya nuna bacin rai kan yadda ake sayen ƙuri’u a zaɓen, yana cewa ana sayen ƙuri’u tsakanin ₦20,000 zuwa ₦30,000 a wasu wurare.
Obi, wanda ya kada ƙuri’arsa da misalin ƙarfe 11:50 na safe a Umudim/Akasi, ya ce wannan dabi’a tana lalata dimokuraɗiyyar ƙasar, cewar rahoton Punch.
Ya ce:
“Idan mutum ya sayar da ƙur’arsa ₦30,000, me za a biya shi a wata mai zuwa? Sayar da ƙuri’arka na nufin babu makaranta, babu asibiti, babu aiki – ka sayar da makomarka.”
Ya ce a wasu ƙasashen Afrika da yake lura da zaɓe, bai taɓa ganin irin wannan halin ba, yana roƙon ‘yan jarida da su taimaka wajen kare mutuncin tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar.
Obi ya ƙara da cewa ko da yake yana goyon bayan ɗan takarar LP, amma duk masu fafatawa ‘yan uwansa ne, yana mai fatan wanda ya yi nasara zai yi aiki tukuru domin jama’a.
Gwamna Soludo ya cika baki kan zabe
Mun ba ku labarin cewa Farfesa Charles Soludo ya kada kuri'arsa a zaben gwamnan jihar Anambra da ake gudanarwa a ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamban 2025.
Gwamnan wanda yana daga daga cikin 'yan takara ya nuna kwarin gwiwar samun nasara kan abokan hamayyarsa da suke fafatawa a zaben.
Sai dai, Gwamna Soludo ya bayyana cewa sun bankado wani shiri na shirya rashin gaskiya wajen fitar da sakamakon zaben.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


