Anambra 2025: APGA Ta Lallasa APC, PDP, Ta Lashe Zabe a Rumfar Dan Takarar LP
- Gwamna Charles Soludo ya doke dan takarar jam'iyyar LP, George Moghalu, a rumfar zabensa da kuri’u 57 bisa 22
- Rahotanni sun nuna ƙarancin fitowar masu kada kuri’a da kuma zarge-zargen sayen kuri’a a sassa da dama na Anambra
- A hannu daya, jam’iyyar APC ta yi nasara a rumfar da tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya kada kuri’arsa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra — Dan takarar gwamna na jam’iyyar LP a zaben gwamnan Anambra da ke gudana, George Moghalu, ya sha kaye a rumfar zaben sa.
An rahoto cewa Gwamna Charles Soludo na jam'iyyar APGA ne ya lashe zabe a rumfar zaben ta Uruagu Ward 1, da ke karamar hukumar Nnewi ta Arewa.

Source: Original
'Dan takarar LP ya fadi a rumfar zabensa
Sakamakon da jami’in kula da rumfar zaben, Okonkwo Ebere, ya bayyana da misalin karfe 2:50 na rana ya nuna cewa Soludo ya samu kuri’u 57, in ji rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan Soludo ya yi nasara da kuri'u 57, an ce Moghalu ya samu kuri'u 22, yayin da dan takarar APC, Nicholas Ukachukwu, ya samu kuri'u 5 kacal.
Jimillar kuri’un da aka kada a rumfar ta kai 85, kasa da kashi 20 cikin 100 na masu kada kuri’a 463 da aka yi wa rajista a wurin.
Yadda aka gudanar da zabe a rumfar Moghalu
Moghalu ya kada kuri’arsa a mazabar Uruagu Ward 1, Nnewi ta Arewa da misalin karfe 11:40 na safe, tare da iyalansa da magoya bayansa.
Bayan ya kada kuri’a, Moghalu ya bayyana takaici kan karancin fitowar masu kada kuri’a da kuma cin hanci da rashawa da ake zargin ya faru a sassa daban-daban na jihar.
“Mutane suna cewa sai mun basu kuɗi kafin su kada kuri’a,” in ji wani jami’in LP da ke lura da zabe a Nnewi yayin da yake magana da manema labarai.
Rahotanni sun nuna cewa an samu jinkirin fara zabe a rumfar zaben saboda makarar kayan zabe da kuma jinkirin isowar masu kada kuri’a.
Zargin sayen kuri’a a zaben Anambra
A rumfa mai lamba PU 012, da ke Cooperative Centre, Uruagu Ward 1, an lura cewa har zuwa karfe 10:58 na safe, masu kada kuri'a ba su fito ba, sai wasu tsiraru.
Rahotanni daga yankuna daban-daban na Uruagu da Nnewi ta Arewa sun nuna cewa an samu zarge-zargen sayen kuri’a daga wakilan jam’iyyu daban-daban.
Sai dai jami’an tsaro da masu lura da zabe sun tabbatar da cewa ba a samu wani tashin hankali ba, sai dai raunin halartar masu zabe a yawancin rumfunan.

Source: Twitter
APC ta yi nasara a rumfar zaben Peter Obi
Haka kuma, The Nation ta rahoto cewa, jam’iyyar APC ta yi nasara a rumfar da Peter Obi, ya kada kuri’arsa, a kauyen Amatutu, Agulu, karamar hukumar Anaocha.
A rumfar zabe ta 019, Umudimakasi, inda Obi ya kada kuri’a, APC ta samu kuri’u 73, LP ta samu 57, yayin da APGA ta samu 38. Sauran jam’iyyu kamar YPP, ZLP, APM, ADC da AAC sun samu kuri’a guda daya kowanne.
Anambra: An kama wakilan gwamnati da kudi?
A wani labarin, mun ruwaito cewa, cibiyar CDD ta fitar da rahoto na binciken da ta gudanar game da zarge-zarge uku da aka samu a zaben Anambra.
Bincike na farko ya ta'allaka ne kan wani rahoto da ka yada cewa an kama wakilan Gwamna Soludo da Naira biliyan 1.5.
Cibiyar CDD ta kuma bayyana sakamakon bincikenta kan zargin cewa wani ciyaman ya tura 'yan snada sun hana a gudanar a zabe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


