Zaben Anambra 2025: An Kama Wakilan Gwamna da Tsabar Kudi N1.5bn? An Ji Gaskiya

Zaben Anambra 2025: An Kama Wakilan Gwamna da Tsabar Kudi N1.5bn? An Ji Gaskiya

  • Cibiyar CDD ta fitar da rahoto na binciken da ta gudanar game da zarge-zarge uku da aka samu a zaben gwamnan Anambra
  • Bincike na farko ya ta'allaka ne kan wani rahoto da ka yada cewa an kama wakilan Gwamna Charles Soludo da N1.5bn
  • CDD ta kuma bayyana sakamakon binciken ta kan zargin cewa wani ciyaman ya tura 'yan sanda sun hana a gudanar a zabe

Anambra — Cibiyar Nazarin Dimokuraɗiyya ta CDD ta gano gaskiya game da zargin da ake yi na an kama wasu wakilan gwamnan Anambra da kudi ranar zabe.

CDD ta ce rahotannin da ake yadawa a kafafen sada zumunta na cewa an kama wakilan Gwamna Chukwuma Soludo biyu da N750m kowane, ba gaskiya ba ne.

An gudanar da bincike game da zargin cewa an kama wakilan gwamnan Anambra da kudi a ranar zabe.
Hoton Gwamna Charles Soludo a lokacin da ya je kada kuri'a a zaben gwamnan Anambra. Hoto: @CCSoludo
Source: Original

An kama wakilan gwamna da N1.5bn?

Rahoton ƙaryar, wanda aka yada ta dandalin Facebook mai suna Onitsha Square, ya yi zargin cewa an kama wakilan dauke da zabar kuɗin a lokacin da ake gudanar da zaben gwamna na yau, Asabar, 8 ga Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

Ana cikin kada kuri'a, Gwamna Soludo ya cika baki kan zaben Anambra

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani Michael Chibuzo, ya wallafa a dandalin cewa:

“An kama wakilai biyu na Soludo da N750m kowanne. Amuneke ya lalata baitulmalin Anambra!”

Sai dai, binciken da CDD ta gudanar ya tabbatar cewa babu wata sahihiyar hujja da ke tabbatar da wannan zargi.

Sannan ba a samu rahoto daga hukumomin tsaro, hukumar zabe, ko wani ingantacciyar kafar labarai da ke nuna cewa an kama jami’an gwamnati da kuɗin ba.

Bidiyon makudan kuɗi a zaben Anambra

Wani faifan bidiyo da ya bazu a Facebook yana nuna sunki sunki na takardun Naira, dauke da rubutun da ke cewa "an shigar da makudan kuɗi a Anambra" kafin zabe, shima ƙarya ne.

Binciken CDD War Room ya gano cewa an fara wallafa bidiyon ne a shafin TikTok na Pulse TV tun ranar 14 ga Afrilu, 2025, tare da taken:

“₦50m na bikin cika shekaru 50 da haihuwa, lallai kudi masu gidan rana."

Kara karanta wannan

INEC na fuskantar matsin lamba kan zaben Anambra, hukumar ta yi magana kan BVAS

Bidiyon ya nuna wani taron murnar cika shekaru 50, ba wani lamari da ya shafi zaben gwamna ba. Ba a samu wata hujja da ta nuna cewa kuɗin na da alaƙa da jam’iyyun siyasa ko Anambra ba.

Rahoto ya nuna cewa an samu wasu makudan kudi a ranar zaben Anambra.
Jami'an hukumar INEC na tantance masu kada kuri'a a zaben Najeriya. Hoto: @SituationRoomNg
Source: Twitter

Ciyaman ya tayar da rikici a zaben Anambra?

Haka kuma, an samu wani rahoto daga kungiyar Soldiers of Mouth (SOM) da ta ya zargin cewa wani ciyaman a Anambra ya tura ‘yan sanda don hana zaɓe gudana.

Sai dai, bayan tantance hotuna da bidiyon da aka turo ta dandalin Check by Meedan, CDD ta bayyana cewa babu wata shaida ta tashin hankali ko katsalandan na ciyaman din.

Bidiyon ya nuna wata motar ‘yan sanda da Hilux kawai a wani wuri, ba tare da wata hujja ta nuna an hana zabe ko tashin hankali ba.

Bugu da ƙari, ba a bayyana sunan shugaban karamar hukumar, yankin da abin ya faru, ko rumfar da abin ya shafa ba. Babu wata kafar labarai ko rahoton hukuma da ya tabbatar da zargin.

CDD ta shawarci ‘yan Najeriya da su guji yada labaran da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, musamman a lokacin zabe.

Kara karanta wannan

Tsakanin APC, APGA: Ƴan Najeriya sun hango wanda zai lashe zaben gwamnan Anambra

Zaben gwamna: EFCC ta dura rumfunan Anambra

A wani labari, mun ruwaito cewa, jami’an EFCC sun isa Anambra domin sa ido kan yiwuwar sayen kuri’u da kuma tabbatar da gaskiya zaben gwamna.

An rahoto cewa jami’an EFCC sun isa makarantar firamare ta CPS da ke Amawbia, karamar hukumar Awka ta Kudu domin sa ido kan zaben da kuma hana sayen kuri’a.

Dimma Nwobi, ta bayyana cewa sayen kuri’a na gudana a wasu yankuna, musamman a Nnewi ta Arewa, inda ta ce jami’an INEC da ‘yan sanda ba su kai kayan zabe wurin cikin lokaci ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com