Tsakanin APC, APGA: Ƴan Najeriya Sun Hango Wanda Zai Lashe Zaben Gwamnan Anambra

Tsakanin APC, APGA: Ƴan Najeriya Sun Hango Wanda Zai Lashe Zaben Gwamnan Anambra

  • 'Yan takara 16 ne za su fafata a zaben gwamnan jihar Anambra na yau Asabar, ciki har da Gwamna Charles Soludo na APGA
  • Kashi 53.5 na wadanda suka kada zaben ra'ayi da Legit.ng ta gudanar a soshiyal midiya su na ganin Soludo ne zai ci zaben
  • Masana siyasa sun ce karfin mulki da tasirin jam’iyyar APGA na iya tabbatar da tazarcen Gwamna Soludo a zaben yau

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra – Gwamna Charles Soludo, wanda ke neman wa’adi na biyu, zai san makomarsa yau Asabar yayin da ‘yan Anambra za su kada kuri'ar zaben sabon gwamna.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa jam’iyyu da ‘yan takara 16 ne za su fafata a wannan zaɓen da ake gudanarwa ba a cikin sauran manyan zabuka ba.

Kara karanta wannan

INEC na fuskantar matsin lamba kan zaben Anambra, hukumar ta yi magana kan BVAS

Ana hasashen cewa Gwamna Charles Soludo ne zai lashe zaben gwamnan Anambra
Hoton Gwamna Charles Soludo, Nicholas Ukachukwu da Moghalu Nnadubem. Hoto: @CCSoludo,@Dr_N_Ukachu_MFR
Source: Facebook

Sai dai wani rahoto na BBC ya nuna cewa 'yan takara hudu ne ido ya koma kansu, kasancewar su ne ke da karfi a siyasar Anambra.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaben Anambra: ‘Yan takara 4 da suka fi fice

‘Yan takarar da ake gani za su taka rawa sosai sun haɗa da:

  • Charles Soludo na jam’iyyar APGA.
  • Nicholas Ukachukwu na jam'iyyar APC.
  • Moghalu Nnadubem na jam'iyyar LP.
  • Ezenwafor Jude na jam'iyyar PDP.

Sai dai, ana ganin Gwamna Soludo, wanda aka zaɓa a 2021, yana da karfi sosai saboda shi ke rike da madafun iko, sannan ita kanta jam’iyyarsa ta APGA na da tasiri a siyasar jihar Anambra.

Amma ‘yan adawa suna ganin cewa rashin gamsuwa daga jama’a da goyon bayan matasa za su iya ba APGA da Soludo matsala a kokarin neman tazarce.

'Soludo zai sake yin nasara' - Zaben Legit

Kafin a shiga rumfunan zaɓe, Legit.ng ta gudanar da zaɓen ra’ayi a shafinta na X domin ganin yadda jama’a ke hasashensu game da zaɓen na Anambra.

Kara karanta wannan

INEC ta dauki matasa 24000 aikin zabe, Yiaga ta hango abin da zai faru a Anambra

Sakamakon ya nuna cewa; 53.5% na wadanda suka ba da amsa sun yi hasashen cewa Gwamna Soludo zai sake yin nasara a ƙarƙashin jam’iyyar APGA.

Sannan 33.8% sun ce Moghalu Nnadubem na LP ne zai yi nasara, yayin da 7% suka nuna Nicholas Ukachukwu na APC zai ci zaben. Ezenwafor Jude na PDP ya samu kuri'a 5.6% kawai.

Sai dai Legit.ng ta bayyana cewa wannan zaɓe ne ra’ayi kawai, ba shi da tasiri a dokance, domin INEC ce kaɗai za ta tabbatar da wanda ya yi nasara bayan kirga ƙuri’u daga ƙananan hukumomi 21 na jihar.

Masana sun yi hasashen cewa Gwamna Charles Soludo ne yake da karfin lashe zaben gwamnan Anambra
Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya karbi kambun 'gwarzon shugaba'. Hoto: @CCSoludo
Source: Facebook

Masanin siyasa ya hango nasarar Soludo

Ɗaya daga cikin masana harkokin siyasa, Donald Okwuosa, ya yi hasashen cewa Gwamna Soludo zai sake cin zabe cikin sauƙi saboda kwarewarsa da tasirin mulkinsa.

A zantawarsa da Legit.ng, Donald Okwuosa ya ce babu wani ɗan takara da ke da ƙarfin da zai iya kwace mulki daga hannun Soludo a yanzu.

A cewarsa, nasarar Soludo za ta ta’allaka ne kan:

  1. Kyakkyawan tsari da tsabtace tattalin arziki a lokacin mulkinsa.
  2. Shi ke da madafun iko kuma tsarin tsaron jihar na ƙarƙashinsa.
  3. Tasirin sa a matakin ƙananan hukumomi 21 na jihar.
  4. Ƙarfi da kudi da gwamna ke da su a matsayinsa na mai mulki.
  5. Goyon bayan jama’a da matasa a faɗin jihar.

Kara karanta wannan

Abubuwa 8 da ba ku sani ba game da jihar Anambra da ake shirin zaben gwamna

Yayin da ‘yan Anambra ke fitowa domin kada ƙuri’a yau, idon duniya na kan Awka, inda INEC za ta bayyana wanda ya lashe zaben gwamnan jihar – wanda hakan ka iya sauya taswirar siyasar jihar gaba ɗaya.

Anambra: INEC ta dauki ma'aikatan zabe 24,000

A wani labarin, mun ruwaito cewa, INEC ta tabbatar da cewa ta tura jami’ai 24,000 da na’urorin BVAS 6,879 domin gudanar da zaben jihar Anambra.

Kungiyar Yiaga Africa ta yi gargadin cewa ba lallai a samu yawan masu kada kuri’a ba saboda rashin amincewa da tsarin zabe.

Hukumar INEC dai ta tabbatar da cewa an samar da motocin jigilar kaya fiye da 3,000 da jiragen ruwa 83 domin gudanar da sahihin zabe.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com