INEC Ta Dauki Matasa 24000 Aikin Zabe, Yiaga Ta Hango abin da Zai Faru a Anambra

INEC Ta Dauki Matasa 24000 Aikin Zabe, Yiaga Ta Hango abin da Zai Faru a Anambra

  • Hukumar INEC ta tabbatar da cewa ta tura jami’ai 24,000 da na’urorin BVAS 6,879 domin gudanar da zaben jihar Anambra
  • Kungiyar Yiaga Africa ta yi gargadin cewa ba lallai a samu yawan masu kada kuri’a ba saboda rashin amincewa da tsarin zabe
  • INEC dai ta tabbatar da cewa an samar da motocin jigilar kaya fiye da 3,000 da jiragen ruwa 83 domin gudanar da sahihin zabe

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce ta kammala duk shirye-shirye don gudanar da zaben gwamna a Anambra ranar Asabar mai zuwa.

Hukumar ta bayyana cewa ta kammala horas da jami’an zabe 24,000, tare da tantance kungiyoyi 114 na sa ido daga cikin gida da ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

Anambra 2025: Manyan laifuffukan zabe a Najeriya da hukuncin da doka ta tanada

INEC.
Wata dattijuwa tana kada kuri'arta a lokacin zabe. Hoto: @inecnigeria
Source: Getty Images

INEC ta gama shirin zaben Anambra

Haka kuma, kafafen watsa labarai 76 da aka ba lasisi za su ruwaito zabukan kai tsaye daga sassan jihar, a cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

INEC ta bayyana cewa an shirya na’urorin BVAS guda 6,879 don tabbatar da tantancewa da kada kuri’a cikin gaskiya.

Rahoton hukumar ya nuna cewa akwai rumfunan zabe 5,718 da kuma ƙarin wuraren zabe 183 a fadin ƙananan hukumomi 21 na jihar.

Hukumar zaben, ta kuma bayyana cewa an kafa RAC 45 domin saukaka jigilar kayan aiki da ma’aikata a ranar zabe.

Rarraba kayan zabe a fadin Anambra

INEC ta ce an samar da motoci 3,000 da jiragen ruwa 83 domin isar da kayan zabe zuwa yankunan da ruwa ya mamaye.

Hukumar ta kuma tabbatar da cewa fiye da kashi 98 cikin 100 na na’urorin BVAS suna aiki bayan gwajin da aka gudanar.

Kara karanta wannan

Zaben 2025: Jerin gwamnonin da suka mulki jihar Anambra daga 1999 zuwa yau

Rahoto ya nuna cewa Anambra tana da masu kada kuri’a 2,802,790, yayin da kashi 63.9 cikin 100 suka karɓi katin zabensu.

Haka kuma, jam’iyyun siyasa 16 ne suka shiga takara a zaben gwamnan jihar na bana, kamar yadda rahoton shafin INEC ya nuna.

INEC ta ce an ɗauki matakan tsaro masu ƙarfi sre da haɗin gwiwar jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya kafin, lokacin, da bayan zaben.

INEC ta ce ta kammala shiri na rarraba kayan zabe a lungu da sakunan jihar Anambra
Sabon shugaban INEC, Joash Amupitan, ya na jawabi a ofishin hukumar a Abuja. Hoto: @inecnigeria
Source: Twitter

Yiaga Africa ta yi gargadi a zaben Anambra

Sai dai a wani rahoto na daban, ƙungiyar Yiaga Africa ta yi gargadin cewa fitowar masu kada kuri’a a zaben Anambra na 2025 na iya yin ƙasa sosai.

Kungiyar ta bayyana cewa yawancin mazauna jihar, musamman matasa, ba su da sha’awar shiga tsarin zabe saboda rashin amincewa da sakamakon zabuka a baya.

A cikin sanarwar da suka fitar a shafin Yiaga na X, Asmau Maikudi da Samson Itodo, shugabannin kungiyar, sun ce yanayin siyasa a jihar ya kasance cikin sanyi, mutane na nuna rashin sha’awar shiga harkokin zabe.

Kara karanta wannan

Anambra 2025: Dalilai 4 da za su sanya dan takarar APGA ya lashe zaben gwamna

Kungiyar ta bukaci jam’iyyun siyasa, INEC, da jami’an tsaro su dauki matakai cikin gaggawa domin dawo da amincewar jama’a kan zabukan jihar.

Abubuwa 4 da za su iya ba APGA nasara

A wani labarin, mun ruwaito cewa, al'ummar Anambra za su fita ranar Asabar domin zaben wanda zai shugabance su na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Yayin da 'yan takara 16 ne za su kara a zaben, ana ganin APGA da dan takararta, Gwamna Charles Soludo ne za su lashe wannan zaben saboda wasu dalilai.

Daga cikin dalilan akwai karfin APGA da ta nuna a watan Satumba 2024, lokacin da ta lashe dukkan mukaman ciyamomi da kansiloli na Anambra.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com