Rikicin PDP: Shugabanni a Jihohi 36 Sun Raba Gardama tsakanin Damagum da Tsagin Wike

Rikicin PDP: Shugabanni a Jihohi 36 Sun Raba Gardama tsakanin Damagum da Tsagin Wike

  • Masu ruwa da tsakin PDP na ci gaba da kokarin warware rikicin da ya dade yana addabar babban jam'iyyar adawa a Najeriya
  • A jiya Alhamis, shugabannin PDP na jihohi 36 da Abuja suka yi taro kan rikicin shugabanci da ya barke a jam'iyyar
  • Sun yi fatali da tsagin Mohammed Abdulrahman da ke goyon bayan ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike a rikicin shugabancin PDP

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugabannin jam’iyyar PDP na jihohi 36 da Abuja sun bayyana cikakken goyon bayansu ga kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) ƙarƙashin Umar Damagum.

Wannan matsaya ta ciyamomin PDP na jihohin Najeriya na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin shugabanci ya kai ga darewar jam’iyyar gida biyu.

Shugaban PDP na kasa, Umar Damagum.
Hoton shugaban PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum Hoto: @OfficialPDP
Source: Twitter

Tribune Nigeria ta ruwaito cewa shugabannin PDP na jihohi sun goyi bayan Damagum ne a taron da suka gudanar a Abuja ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da batun barazanar Trump, Tinubu ya gana da shugaban kasar Saliyo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin PDP sun yabawa kotun Oyo

Sun kuma yaba wa Mai Shari’a Ladiran Akintola na Babbar Kotun Jihar Oyo bisa ba da izinin ci gaba da shirin gudanar da babban taron PDP na kasa wanda aka shirya a Ibadan ranar 15 ga Nuwamba, 2025.

Da yake karanta sanarwar bayan taron, Shugaban Ƙungiyar kuma shugaban PDP na Jihar Edo, Honourable Tony Aziegbemi, ya jaddada bukatar tabbatar da da’a a cikin jam’iyya.

A cewarsa, akwai bukatar haɗin kai da jajircewar mambobi wajen kare martabar jam’iyyar adawa mafi girma a ƙasar nan.

Damagum ya kara samun goyon baya

Sanarwar da PDP ta wallafa a shafin X, ta ce:

“Ƙungiyar shugabannin PDP na jihohi ta jaddada goyon baya, amincewa da biyayya ga shugaban jam’iyya na kasa, Ambasada Umar Damagum, da dukkan mambobin Kwamitin gudanarwa (NWC).
“Ƙungiyar ta yaba da hukuncin da Mai Shari’a Akintola ya yanke, wanda ya buɗe ƙofar gudanar da babban taron PDP da aka tsara a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, 2025, a Ibadan, Jihar Oyo.

Kara karanta wannan

BoT: PDP ta dare gida 2, tsagin Abdulrahman ya kafa sabon kwamiti a gidan Wike

“Ta kuma yi kira ga dukkan ‘yan takara da aka tantance bisa tsarin kundin PDP su fara shirye-shiryen halartar taron domin zaɓar sababbin shugabanni jam'iyya, masu ƙwarewa da aminci.”
Shugabannin PDP na jihohi.
Hoton shugabannin PDP na jihohin Najeriya yayin da suka ziyarci shugaban jam'iyya na kasa, Umar Damagum Hoto: @OfficialPDP
Source: Twitter

An yi fatali da tsagin Wike

Ƙungiyar ta kuma nesanta kanta daga tsagin ministan Abuja, Nyesom Wike, wanda ke goyon bayan Mohammed Abdulrahman a matsayin mukaddashin shugaban PDP na kasa, tana mai cewa:

"Shugaban jam'iyyar PDP na kasa guda daya ne kuma shi ne Umar Damagum, babu wani bayan shi a yanzu," in ji sanarwar.

Wani dan PDP a jihar Katsina, Sulaiman Abdullahi ya shaida wa Legit Hausa cewa alamu sun nuna babu ranar da shugabannin mu za su ajiye son rai, su hada kansu.

A cewarsa, wannan rikici da ya raba kan kwamitin gudanarwa na kasa ya kara tabbatar da mutuwar PDP a siyasar Najeriya.

A cewarsa:

"Dole mu fada wa kanmu gaskiya, PDP ta ruguje har na fara cire rai da fargadowarta, wannan abun da ke faruwa ya wuce tunani.
"Na fada zan kara fada, matukar PDP ba ta rufe ido ta kori duk wadanda ke jawo wannan rigima ba, to ba za ta taba gyaruwa ba. Kowa ya san Wike ke jawo matsalar nan, amma an kasa masa komai."

Kara karanta wannan

Damagum: Shugaban PDP ya fadi dalilin kin hukunta masu kawo cikas a jam'iyyar

Damagum ya kare kansa a rikicin PDP

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum, ya ce kokarin kare martabar jam'iyya ne ya hana shi ladabtar da wasu mambobi da suka karya doka.

Damagum ya bayyana ya zabi bin matakan yin sulhu don warware rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar PDP domina ganinsa hakan shi ne maslaha.

Ya kuma tabbatar da cewa ya san akwai wadanda ke jin haushinsa ko suke zarginsa da hannu a rigimar PDP saboda ya ki daukar mataki kan mambobin da suka saba doka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262