Anambra 2025: Manyan Laifuffukan Zabe a Najeriya da Hukuncin da Doka Ta Tanada
Abuja – A tsarin dimokuradiyya, kada kuri'a ce hanyar da 'yan kasa ke zabar shugabannin da suke so. Saboda haka, Najeriya ta tanadi dokoki masu tsauri domin kare tsarin zabe daga masu son yin magudi ko karya doka.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Wadannan dokoki suna cikin Dokar Zabe ta 2022, wacce ta amince da hukuncin tarar kudi ko zaman gidan yari, ko duka biyun ga duk wanda ya karya tanade-tanaden ta.

Source: Twitter
Rahoton hukumar INEC ya nuna cewa laifuffukan zabe suna da hadari sosai ga tsarin dimokuraɗiyya, saboda suna iya rage amincewar jama’a ga sakamakon zabe.
Laifuffukan zabe da hukuncinsu a Najeriya
Saboda haka ne hukumar INEC da hukumomin tsaro ke yawan jan hankalin ‘yan kasa su guji aikata wadannan laifuffukan zaben da ke iya jefa su gidan yari na tsawon lokaci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Laifin rijistar zabe sau 2 ko jabun katin zabe
Sashe na 114 na Dokar Zabe ya fayyace laifuffukan da suka shafi rijistar masu kada kuri’a, kamar yadda Legit Hausa ta gani a shafin intanet na ofishin lauyoyi na M.A Banire & Associates.
Wadannan laifuffuka sun haɗa da yin rijista fiye da sau ɗaya, yin jabun katin zabe, amfani da sunan jami’in rijista domin yin magudi, da kuma yin rijista da sunan wani mutum.
Doka ta ce duk wanda aka kama yana da hannu a irin wannan laifi zai fuskanci hukuncin tarar N1,000,000 ko zaman gidan yari na watanni 12 ko duka biyun.
Hakan na nufin cewa idan mutum ya taimaka wajen yin wannan laifi, ba lallai sai shi ne ya yi da kansa ba, to doka za ta hukunta shi kamar wanda ya aikata da hannunsa.
Masu lura da harkokin zabe sun ce wannan doka ta zama wajibi ne domin rage yawan mutanen da ke amfani da katin bogi ko rijistar jabu don yin magudi a ranar zabe.
2. Jabun takardun takara ko sakomakon zabe
Sashe na 115 ya nuna irin laifuffukan da dan takara zai iya aikatawa wajen neman mukami. Wadannan sun haɗa da buga jabun takardar neman takara, takardar sakamako, ko takardar kada kuri’a, da kuma lalata ko mallakar takardar kuri’a ba bisa ka’ida ba.
Wanda aka samu da laifi a wannan sashe zai fuskanci tara ta N50,000,000 ko zaman gidan yari na shekaru 10 ko duka biyun.
Hukuncin yana da tsauri saboda yana shafar gaskiya da amincin sakamakon zabe gaba ɗaya.
Masana sun bayyana cewa wannan sashe ya taimaka wajen tabbatar da cewa kowane dan takara ya tsaya zabe ne bisa gaskiya, ba tare da amfani da takardu ko sakamako na karya ba.
3. Haddasa tarzoma a taron siyasa
Sashe na 116 na Dokar Zabe ya haramta duk wanda zai yi ko ya haddasa tarzoma a wajen taron siyasa, musamman idan manufarsa ita ce tayar da zaune tsaye ko hana gudanuwar taron.
Doka ta ce duk wanda aka kama yana da makami ko abin tayar da hankali a wajen taron siyasa zai fuskanci hukuncin tara na N500,000 ko zaman gidan yari na watanni 12 ko duka biyun.
Wannan sashe ya ba da kariya a lokacin yakin neman zabe, inda wasu jam’iyyun ke amfani da ‘yan daba don hana abokan hamayya gudanar da taruka cikin lumana.
4. Amfani da katin zabe na wani
Sashe na 117 ya tanadi hukunci ga duk wanda ke amfani da katin zabe na wani mutum ko wanda yake da katin zabe fiye da guda daya.
Hakanan, duk wanda ya sayar da katin zabe, ya siya, ko ya karɓa ba bisa doka ba, to ya aikata babban laifi a karkashin wannan sashe.
Hukuncin irin wannan laifi shi ne tara har ta N1,000,000 ko zaman gidan yari na watanni 12 ko duka biyun.
INEC ta sha gargadin jama’a da su daina ba da katin zabensu ga wasu, ko karɓar na wani, saboda hakan yana iya kai su ga daurin shekara guda.
5. Jefa kuri’a sau 2 ko sojan gona da wani
Sashe na 119 ya haramta kada kuri’a fiye da sau ɗaya a zabe guda, ko yin amfani da sunan wani dan kasa domin kada kuri’a.
Wanda ya aikata haka zai fuskanci tara ta N500,000 ko zaman gidan yari na watanni 12 ko duka biyun.
Wannan doka tana tabbatar da adalci wajen zabe, saboda tana hana mutane suyi amfani da katin jabu ko su kada kuri’a a wurare fiye da daya.
INEC ta bullo da amfani da na'urar BVAS domin tabbatar da cewa kowane mutum ya kada kuri’a sau ɗaya kawai a kowanne zabe.
6. Sauran manyan laifuffukan zabe
Baya ga waɗancan laifuffukan zabe da aka zayyano a sama, akwai sauran laifuffuka masu tsanani da doka ta ambata, ciki har da:
- Kin yin aiki yadda ya dace (sashe na 120): Duk jami’in zabe da ya gaza yin aikinsa yadda doka ta tanada zai iya fuskantar hukunci.
- Cin hanci da hadin baki (sashe na 121): Duk wanda ya bayar ko ya karɓi kuɗi domin sauya sakamakon zabe ya aikata babban laifi.
- Boye sirrin kada kuri’a (sashe na 122): An haramta nuna yadda mutum ya kada kuri’arsa domin kare sirrin zabe.
- Rudani a ranar zabe (sashe na 125): Duk wanda ya haddasa rudani ko tashin hankali a wajen kada kuri’a zai fuskanci hukunci.
- Tursasawa ko barazana (sashe na 128): Doka ta hana duk wanda zai tsoratar da masu kada kuri’a ko jami’an zabe.
Haka kuma, doka ta tanadi hukunci ga wanda ya kada kuri’a ba tare da rajista ba (karkashin sashe na 124) ko wanda ya ƙaryata bayanan zabe (karkashin sashe na 123).

Source: Twitter
Kira ga masu kada kuri'a da 'yan takara
Masu ruwa da tsaki a harkar zabe sun yi kira ga ‘yan siyasa, jami’an gwamnati da ‘yan kasa gaba ɗaya da su mutunta dokokin zabe domin tabbatar da gaskiya da kwanciyar hankali a zabubbuka.
A cewar rahoton hukumar INEC, aikata laifin zabe ba wai kawai yana haifar da hukunci bane, yana kuma taba amincewar jama’a ga tsarin dimokuraɗiyya.
Hukumar ta jaddada cewa tana da hadin kai da EFCC, DSS, da 'yan sanda wajen kamo da gurfanar da duk wanda aka samu da laifin zabe.
INEC za ta gudanar da zaben Anambra
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta shirya gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra a ranar Asabar.
Zaben, wanda zai gudana ranar 8 ga watan Nuwamba, 2025, zai kunshi jam'iyyun kusan 16 da suka hada da APGA (mai mulki), APC, PDP, LP da sauransu.

Kara karanta wannan
Kano: 'Yan bindiga sun hallaka mutane bayan sace da dama, an 'gano' inda suka fito
Tun a farkon shirye-shiryen zaben, INEC ta sanar da cewa jam'iyyu za su gudanar da zabukan fitar da gwani na daga ranar 20 ga Maris 2025 zuwa 10 ga Afrilu, 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng




