Daga Obi zuwa Soludo: Yadda APGA Ta Rike Wuta, Ta Mulki Anambra na Tsawon Shekaru 20

Daga Obi zuwa Soludo: Yadda APGA Ta Rike Wuta, Ta Mulki Anambra na Tsawon Shekaru 20

Tun bayan komawar Najeriya zuwa tsarin dimokuradiyya a shekarar 1999, jihar Anambra ta samar da gwamnoni guda biyar.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Anambra – Gwamnonin da suka mulki Anambra daga 1999 zuwa yau sun hada da Chinwoke Mbadinuju, Chris Ngige, Peter Obi, Virginia Etiaba, Willie Obiano da wanda ke kan mulki a yanzu, Charles Soludo.

APGA ta shekara 20 tana mulki a Anambra
Charles Soludo, Virginia Etiaba da Peter Obi, tsofaffin gwamnoni a Anambra Hoto: Charles Chukwuma Solodu/Nonso Smart Okafor/Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Tsawon wadannan shekaru kusan 20, an fafata a neman kujerar gwamnatin Anambra ne a tsakanin jam'iyyun APGA da PDP, wadanda su ka fi farin jini a yankin.

Amma APGA ta samu nasarar ci gaba da rike ragamar siyasar jihar, inda ta samar da gwamnoni da suka yi nasara ko a dai a filin zabe kai tsaye, ko kuma bayan an je kotu.

Kara karanta wannan

'Da gaske ne ana kisan kiyashi a Najeriya,' Jigon APC ya goyi bayan Donald Trump

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wannan labarin, za a karanta gwamnonin APGA da su ka yi mulki a Anambra da nasarar fara wa da 'dan takarar shugaban kasa a 2023, Peter Obi.

1. Peter Obi

A zaben gwamnan Anambra na shekarar 2003, INEC ta bayyana Chris Ngige na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zabe bayan ya samu kuri’u 452,820, yayin da Peter Obi na APGA ya zo na biyu.

Peter Obi ya mulki Anambra sau biyu
Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Twitter

The Cable ta wallafa cewa Obi ya ki amincewa da sakamakon, yana zargin an murde zaben bayan tafka magudi a wasu kananan hukumomi.

Ya kai kara gaban Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Anambra, inda aka shafe kusan shekaru uku ana buga wa a tsakanin Ngige da Obi.

A watan Agusta 2005, kotun ta soke zaben Ngige, tana cewa Obi ne ya lashe kuri’un da suka halatta, wanda ke nufin shi ne halastaccen gwamna.

Ngige ya daukaka kara zuwa kotun daukaka kara a Enugu, amma a ranar 15 ga Maris, 2006, kotun ta tabbatar da hukuncin farko, ta ayyana Obi a matsayin halastaccen wanda ya ci zaben 2003.

Kara karanta wannan

Anambra 2025: Dalilai 4 da za su sanya dan takarar APGA ya lashe zaben gwamna

An rantsar da Obi a ranar 17 ga Maris, 2006, bayan kusan shekaru uku da takaddama, wannan nasarar ta bude sabon babi a tarihin siyasar Najeriya tare da kafa APGA a Anambra.

2. Virginia Etiaba

Bayan Obi ya hau mulki, majalisar dokokin jihar ta tsige shi a ranar 2 ga Nuwamba, 2006, bisa zargin rashin da’a, inda ta nada Virginia Etiaba a matsayin mukaddashin gwamna.

Dame Virginia Etiaba, ta yi rikon gwamnan Anambra
Hoton gwamna mace ta farko a Najeriya Virginia Etiaba Hoto: Nonso Smart Okafor/ George Udom
Source: Facebook

Businessday ta wallafa cewa wannan tsari ya bai wa Virgina Etiaba damar zama mace ta farko da ta zama mukaddashin gwamna a Najeriya.

Sai dai a ranar 9 ga Fabrairu, 2007, kotun daukaka kara ta soke tsige shin, ta dawo da Obi bisa hujjar cewa matakin majalisar ya saba wa kundin tsarin mulki.

Daga baya, INEC ta gudanar da wani sabon zabe a watan Afrilu 2007 amma Obi bai tsaya takara ba, yana cewa wa’adinsa ya fara ne daga Maris 2006.

A ranar 14 ga Yuni, 2007, kotun koli ta yanke hukunci da ya tabbatar cewa wa’adin Obi bai kare ba, kamata ya yi ya zo karshe a watan Maris 2010.

3. Peter Obi

Kara karanta wannan

Jihohin da APC da PDP ke mulki a Najeriya kafin zaben gwamnan Anambra na 2025

Yayin da wa’adin Obi na farko ke karewa, INEC ta shirya sabon zaben gwamna a ranar 6 ga Fabrairu, 2010.

Jaridar Sahara reporters ta wallafa cewa Obi, wanda ya sake tsayawa takara karkashin APGA ne ya samu nasarar zama gwamnan Anambra.

Peter Obi ya fafata da Ngige (ACN), Andy Uba (LP), da Charles Soludo (PDP). Obi ya samu kuri’a 97,833, yayin da Ngige ya samu 60,240, Soludo kuma 59,355.

Obi ya kammala wa’adinsa a Maris 2014, inda ya mika mulki ga Willie Obiano, wanda shi ma dan APGA ne.

4. Willie Obiano

Kafin zaben 2014, APGA ta fuskanci kalubale na maye gurbin Obi wanda ke barin kujerar bayan wa’adin sa na biyu.

Willie Obiano ya zama gwamna daga 2014 zuwa 2017
Hoton Willie Obiano, 'dan APGA da ya mulki Anambra Hoto: Chief Willie Obiano
Source: Facebook

Willie Obiano, tsohon ma’aikacin banki, ya lashe zaben fitar da gwani a ranar 26 ga Agusta, 2013.

A zaben da aka gudanar a ranar 6 ga Nuwamba, 2013 wanda aka kara wasu yankuna zuwa 30 ga Nuwamba, INEC ta ce Obiano ne ya yi nasara, kamar yadda Premium Times ta wallafa.

Ta ce Obiano ya samu kuri’a 180,178, inda ya doke Tony Nwoye na PDP, wanda ya samu 97,700 da Ngige na APC da ya samu kuri'a 95,963, an rantsar da shi a ranar 17 ga Maris, 2014.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ba ku sani ba game da Zohran Mamdani, sabon magajin garin New York

5. Wilie Obiano

A ranar 18 ga Nuwamba, 2017, an sake zaben gwamnan Anambra. Obiano ya sake tsayawa takara inda ya kara da Nwoye (APC), Oseloka Obaze (PDP), da Osita Chidoka (UPP).

Daily Post ta wallafa cewa Obiano ya amu rinjaye sosai da kuri’a 234,071, yayin da Nwoye ya samu 98,752, Obaze kuma ya samu 70,293.

Willie Obiano ya zama gwamna na farko da ya lashe dukkan kananan hukumomi 21 a zabe guda.

6. Charles Soludo

Yayin da wa’adin Obiano ke karewa, APGA ta sake neman dan takara mai karfi, inda a zaben fitar da gwani na 3 ga Yuni, 2021 Chukwuma Charles Soludo ya zama 'dan takararta.

BBC Pidgin ta wallafa cewa a zaben gwamna na 6 ga Nuwamba, 2021, wanda aka jinkirta a wasu wurare zuwa 9 ga Nuwamba saboda tsaro, INEC ta ayyana Soludo a matsayin gwamna.

Charles Solodu na kara neman takarar gwamna
Charles Soludo, gwamnan Anambra na yanzu Hoto: Charles Soludo
Source: Facebook

Hukumar zaben ta tabbaya cewa Charles Soludo, wanda ya taba zama gwamnan babban bankin kasa, CBN ya samu kuri’a 112,229.

Kara karanta wannan

Charles Soludo da 'yan takara 3 da za su gwabza a zaben gwamnan Anambra

An rantsar da Soludo a ranar 17 ga Maris, 2022, yana ci gaba da mulkin jihar a yayin da ake shirin gudanar da sabon zabe a ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamba, 2025.

An bayar da hutun zaben Anambra

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Anambra ta ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan gwamnati kafin zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar Asabar.

A wata sanarwa da aka fitar a birnin Awka, babban birnin jihar, shugabar ma’aikatan jihar, Theodora Igwegbe, ta ce an yanke wannan hukunci ne bisa umarnin gwamna Charles Soludo.

Ta kara da cewa zabe hakki ne da ke rataya a wuyan ‘yan kasa kuma ma’aikatan gwamnati suna da rawar da za su taka wajen tabbatar da cewa tsarin dimokuradiyya ya samu karfafa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng