Jihohin da APC da PDP ke Mulki a Najeriya kafin Zaben Gwamnan Anambra na 2025

Jihohin da APC da PDP ke Mulki a Najeriya kafin Zaben Gwamnan Anambra na 2025

  • Gwamna Charles Chukwuma Soludo na jam'iyyar APGA na neman tazarcen wa’adi a zaben gwamnan jihar Anambra
  • Hukumar INEC ta tabbatar da cewa za a gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra a ranar Asabar, 8, Nuwamba, 2025
  • A wannan rahoton, Legit Hausa ta bayyana jihohin da APC da PDP ke rike da mulki yayin da ake shirin zaben Anambra

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Anambra – Mutanen jihar Anambra za su fita cikin jerin gwanon jama’a zuwa rumfunan kada kuri’a a fadin jihar domin zaben gwamna a ranar Asabar, 8, Nuwamba, 2025.

APC za ta yi yunkurin lashe jihar ta hanyar dan takararta, Nicholas Ukachukwu, domin mayar da ita ta zama jiha ta 26 da ke karkashin ikon jam’iyyar.

Taron gwamnonin Najeriya
Gwamnonin Najeriya yayin wani taro a Abuja. Hoto: Abdul No Shaking
Source: Twitter

Sai dai hakan zai kasance gagarumin kalubale, domin dole ne ta karbe mulki daga hannun gwamna mai ci, Charles Soludo na jam’iyyar APGA kafin cika burinta.

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: Gwamnatin Jihar Anambra ta ayyana ranar hutu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wannan rahoton, Legit Hausa ta lissafa adadin jihohin da ke karkashin ikon jam’iyyun APC da PDP kafin zaben gwamnan Anambra.

Jihohin da APC ke mulki a Najeriya

  1. Jihar Akwa Ibom – Gwamna Umo Eno
  2. Jihar Bayelsa – Gwamna Douye Diri
  3. Jihar Benue – Gwamna Hyacinth Alia
  4. Jihar Borno – Gwamna Babagana Zulum
  5. Jihar Cross River – Gwamna Bassey Otu
  6. Jihar Delta – Gwamna Sheriff Oborevwori
  7. Jihar Ebonyi – Gwamna Francis Nwifuru
  8. Jihar Edo – Gwamna Monday Okpebholo
  9. Jihar Ekiti – Gwamna Biodun Oyebanji
  10. Jihar Enugu – Gwamna Peter Mbah
  11. Jihar Gombe – Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya
  12. Jihar Imo – Gwamna Hope Uzodinma
  13. Jihar Jigawa – Gwamna Umar Namadi
  14. Jihar Kaduna – Gwamna Uba Sani
  15. Jihar Katsina – Gwamna Dikko Umaru Radda
  16. Jihar Kebbi – Gwamna Nasir Idris
  17. Jihar Kogi – Gwamna Ahmed Usman Ododo
  18. Jihar Kwara – Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq
  19. Jihar Lagos – Gwamna Babajide Sanwo-Olu
  20. Jihar Nasarawa – Gwamna Abdullahi Sule
  21. Jihar Neja – Gwamna Mohammad Umar Bago
  22. Jihar Ogun – Gwamna Dapo Abiodun
  23. Jihar Ondo – Gwamna Lucky Aiyedatiwa
  24. Jihar Sokoto – Gwamna Ahmad Aliyu
  25. Jihar Yobe – Gwamna Mai Mala Buni

Kara karanta wannan

Anambra 2025: Dalilai 4 da za su sanya dan takarar APGA ya lashe zaben gwamna

Jihohin da PDP ke mulki a Najeriya

  1. Jihar Adamawa – Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri
  2. Jihar Bauchi – Gwamna Bala Muhammed
  3. Jihar Osun – Gwamna Ademola Adeleke
  4. Jihar Oyo – Gwamna Seyi Makinde
  5. Jihar Filato – Gwamna Caleb Mutfwang
  6. Jihar Rivers – Gwamna Siminalayi Fubara
  7. Jihar Taraba – Gwamna Agbu Kefas
  8. Jihar Zamfara – Gwamna Dauda Lawal

Atiku ya bukaci a yi adalci a Anambra

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga ‘yan jihar Anambra da su fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri’a a zaben gwamnan jihar.

Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a X, inda ya bayyana zaben a matsayin babban dama ga jama’ar Anambra domin kawo karshen mulkin da ba su so.

Atiku Abubakar, Sule Lamido
Sule Lamido na gaisawa da Atiku Abubakar. Hoto: Paul O. Ibe
Source: Facebook

Ya kuma bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ƙarƙashin jagorancin Farfesa Joash Amupitan da ta tabbatar da gudanar da sahihin zabe mai tsafta.

Atiku ya ce wannan lokaci ne da al’ummar Anambra za su tashi tsaye wajen tallafa wa dan takarar jam’iyyar ADC, Nwosu Chima John.

Kara karanta wannan

Trump na neman kawo hari Najeriya, an jibge jami'an tsaro 60000 domin zaben Anambra

'Yan takarar zaben gwamna a Anambra

A wani labarin, Legit Hausa ta hada rahoto na musamman kan 'yan takarar da za su buga da gwamna Charles Soludo na jihar Anambra.

Bincike ya gano cewa sama da 'yan takara 15 ne za su fafata a zaben da za a yi a ranar Asabar, 8 ga Oktoba, 2025.

'Dan takarar ADC, Nwosu Chima John da na jam'iyyar APC, Nicholas Ukachukwu na cikin wadanda za su fafata a zaben.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng