Rubutu a Facebook Ya Jefa 'Yan Kwankwasiyya 2 a Gagarumar Matsala a Kano

Rubutu a Facebook Ya Jefa 'Yan Kwankwasiyya 2 a Gagarumar Matsala a Kano

  • Yan sandan Kano sun kama mutum biyu mabiya Kwankwasiyya bisa taba kimar shugaban karamar hukumar Tofa, Yakubu Ibrahim Addis
  • Wadanda yan sandan suka kama sun yi wani rubutu a shafin sada zumunta na Facebook, ana zargin sun soki ciyman kan aikin titin Lambu
  • Hon. Yakubu ya bayyana cewa wannan ne karo na biyu da matasan suka taba shi, kuma ya kai korafi ne domin su kawo hujja a kan zargin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - An shiga fargaba a karamar hukumar Tofa ta Jihar Kano bayan kama wasu ‘yan jam’iyyar NNPP saboda rubutun da suka wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

'Wane hali muke ciki,' Tsohon hadiminsa ya nemi Tinubu ya yi bayani kan barazanar Trump

'Yan sanda sun kama mutanen biyu bisa sukar da suka yi da zargin shugaban karamar hukumar Tofa, Hon. akubu Ibrahim Addis, da kin kammala aikin gyaran hanya.

Hon. Ibrahim Yakubu Addis.
Hoton shugaban karamar hukumar Tofa, Hon. Yakubu Ibrahim Addis a ofishinsa Hoto: Yakubu Ibrahim Addis
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mutanen biyu da aka kama sun haɗa da Murtala Garba Doka da Shamsu Safiyanu Lambu, wanda aka fi sani da Shamzeet Lambu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa an kama su ne a ranar Litinin bisa umarnin shugaban karamar hukumar, Hon. Ibrahim Yakubu.

Dalilan kama yan Kwankwasiyya 2 a Kano

An ce kama su ya samo asali ne daga wani rubutu da Shamzeet Lambu ya wallafa a Facebook, inda ya zargi ciyaman da gaza kammala aikin gina titin Lambu–Banki–Yarimawa–Jakata.

Lambu ya yi ikirarin cewa gwamnatin jihar Kano ta fitar da kimanin Naira miliyan 240 domin gina wannan titi amma ciyaman din ya gaza yin aikin.

A cikin rubutun, Lambu ya ce: “Allah ya isa kudinmu Naira Miliyan 240, Allah Ya saka mana."

Wane halin matasan ke ciki a Kano?

Majiyoyi sun ce da farko an tsare matasan a ofishin ‘yan sanda na karamar hukumar Tofa, kafin daga bisani a maida su hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta Kano da ke Bompai domin bincike.

Kara karanta wannan

Zargin Triumph: Kungiyoyin addinin musulunci a Kano sun maka Gwamna Abba a gaban kotu

Da yake tabbatar da lamarin, Comrade Nazifi Ado Lambu, shugaban matasa a yankin, ya ce kama mutanen biyu ta jawo damuwa da ce-ce-ku-ce a tsakanin mazauna yankin, cewar rahoton Daily Post.

“Eh, an kama su saboda rubutun da suka yi a Facebook kan aikin hanya. An fara tsare su a ofishin ‘yan sanda na Tofa kafin a kai su Bompai," in ji shi.

Ciyaman na da hannu a kama matasan?

Da aka tuntube shi, shugaban karamar hukumar Tofa, Hon Yakubu Addis, ya tabbatar da cewa shi ne ya kai korafi har aka kama su, domin a binciki gaskiyar zargin.

Ya ce:

“Mun nemi su kawo hujja kan abin da suka rubuta, amma babu. Ina da iyali da mutane da ke kallona, wasu sun gaskata abin da suka fada.
"Sun taba yin haka a baya na yi shiru, amma yanzu sun maimaita. Aikin titin da gwamnati ta bayar bai kai Naira miliyan 100 ba, amma sun je suna yaɗa cewa ya haura. Mun nemi su kawo shaida.”
Hon. Yakubu Ibrahim Addis.
Hoton shugaban karamar hukumar Tofa, Hon. Yakubu Ibrahim Addis Hoto:Yakubu Ibrahim Addis
Source: Facebook

An fitar da N4.9bn domin ayyuka a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano ta amince da kashe sama da Naira biliyan 4.9 don gudanar da manyan ayyuka da nufin farfado da harkar ilimi a fadin jihar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi wa shugabannin al'umma 2 yankar rago a jihar Katsina

Gwamnatin ta ce wadannan ayyuka za su taimaka wajen inganta makarantu, karfafa matakin koyarwa da koyo, da kuma bai wa yara da matasa damar samun ilimi.

Daga cikin abubuwan da aka amince da su akwai gyaran Makarantar Gwamnati ta Fasaha da ke Ungogo da biyan bashin masu samar da abinci a makarantun kwana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262