Musulmi, Zohra Mamdani Ya Lashe Zaben Amurka duk da Barazanar Trump
- Zohran Mamdani ya doke Andrew Cuomo a zaben magajin garin New York, ya zama Musulmi na farko da ya samu matsayin
- Yayin da ya ke yakin neman zabe, ya yi alkawarin kula da yara kyauta, bada tallafin sufuri da kuma rage nauyin kudin haya
- Mamdani ya ce nasarar da ya yi ta kara tabbatar da cewa dimokuraɗiyya mallakin jama’a ce ba ta manyan ’yan siyasa kadai ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
New York – 'Dan takarar jam’iyyar Democrat, Zohran Mamdani ya lashe zaben magajin garin New York bayan doke abokin hamayyarsa, Andrew Cuomo, a zaben da aka fafata sosai.
Nasarar ta sanya Mamdani zama Musulmi na farko da zai shugabanci birnin, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Source: Facebook
Al-Jazeera ta wallafa cewa Mamdani ya samu goyon bayan masu sassaucin ra’ayi saboda manufofinsa na kula da yara kyauta, bada tallafin sufuri da kuma daina ƙara kudin gidajen haya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkawarin Mamdani ga mutanen New York
A jawabinsa bayan sanar da sakamakon, Mamdani ya bayyana cewa birnin zai zama “fitila a wannan lokacin na duhun siyasa.”
Baya ga haka, ya yi jawabi yana mai cewa zai kare kowane ɗan New York ba tare da nuna bambanci ba.
Ya ce:
“Ko kai ɗan gudun hijira ne, ko ɗaya daga cikin mata bakaken fata da Donald Trump ya kora daga aiki, ko uwa da ke jiran farashin kayan abinci ya ragu, gwagwarmayarka tamu ce.
"Za mu ba Yahudawa hakkinsu, kuma sama da Musulmi miliyan 1 da suke garin za su ji cewa garin nasu ne.”
Zohran Mamdani ya ƙara da cewa zai yi kokarin inganta aiki a kowace rana domin birnin ya fi yadda yake a jiya.
‘Dimokuraɗiyya taku ce,’ inji Zohra Mamdani
A yayin da yake jawabin godiya, Mamdani ya yaba wa magoya bayansa saboda nuna cewa yana yiwuwa a sauya jagoranci a siyasa.

Source: Facebook
Ya bayyana lashe zaben a matsayin nasarar masu aikin tuki daga Senegal, ma'aikatan lafiya daga Ungazbekistan, da masu dafa abinci daga Trinidad da aka saba mantawa da su.
Ya ce:
“Wannan birni naku ne, kuma wannan dimokuraɗiyya taku ce.”
Ya yi fatan alheri ga abokin hamayyarsa Andrew Cuomo, yana mai cewa:
“Amma bari wannan daren ya zama karon ƙarshe da na ambaci sunansa, domin mu buɗe sabon shafi na siyasa.”
Barazanar Trump a New York kafin zabe
A daidai lokacin da zaben ke tafe, shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazana ga jama’ar New York cewa su hana Mamdani nasara ko kuma su fuskanci hukunci.
The Guardian ta rahoto Trump ya ce:
“Idan ɗan takara Zohran Mamdani ya ci zaben, ba zan ba da kuɗi ga birnin ba, sai mafi ƙarancin da doka ta wajabta. Ba na son bayar da kuɗi masu yawa bayan mummunan sakamako.”
Iran ta kafawa Trump sharadin sulhu
A wani rahoton, kun ji cewa Iran ta yi magana kan zaman fahimtar juna da ta ce Amurka na so su yi kwanan nan.
Ayatolla Ali Khamenei ne ya yi maganar yayin ganawa da wasu dalibai a Tehran domin tuna tarihin kasar.
Khamenei ya ce daga cikin abubuwan da za su saka Iran daina zaman doya da manja da Amurka akwai yanke alaka da Isra'ila.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


