Babbar Kotu Ta Yi Hukunci, Alkalai Sun Fara Cin Karo da Juna kan Taron PDP na Kasa
- Babbar kotun jihar Oyo ta yanke hukuncin da ya ci karo da na kotun tarayya mai zama a Abuja game da babban taron PDP na kasa
- Hakan na zuwa ne bayan rikicin cikin gida ya kara dabaibaye babbar jam'iyyar adawa ta kasa, wanda ya kai ga darewarta gida biyu
- PDP ta shirya gudanar da babban taron kasa wanda za a zabi sababbin shugabannnin jam'iyya a watan Nuwamba, 2025 a Ibadan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ibadan, jihar Oyo - Kwanaki kadan bayan babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta dakatar da babban taron PDP na kasa, jam'iyyar ta samu wani umarni da ya saba wa hukuncin.
Babbar kotun jihar Oyo ta sahalewa jam'iyyar PDP ta kasa ta gudanar da babban taron kamar yadda ta tsara a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta tattaro cewa kotun ta yanke wannan hukunci ne a jiya Litinin, 3 ga watan Nuwamba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta yarda jam'iyyar PDP ta shirya taro
Kotun ta umarci shugaban PDP na kasa, Umar Damagum da sauran masu ruwa da tsaki su ci gaba da shirye-shiryen gudanar da taron yadda suka tsara.
Mai shari’a A.L. Akintola na babbar kotun Oyo, wanda yake jagorantar zaman kotun, ne ya bayar da wannan umarni a ranar Litinin.
Alkalin ya yanke wannan hukunci ne bayan ya saurari bukatar gaggawa da wani jigon PDP, Folahan Malomo Adelabi ya shigar a gaban kotun.
A karar, an bayyana PDP, Umar Damagum, gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) matsayin wadanda ake kara.
Bukatun da aka nema a kotun Oyo
Adelabi, ya roki kotu ta ba da umarnin wucin gadi da zai hana wadanda ake kara yin wani abu da zai iya rushewa, jinkirta ko dakatar da Babban Taron PDP da aka shirya yi a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025.
Adelabi ya kuma nemi kotun ta tilasta wa PDP, Damagum, da Gwamna Fintiri su bi kuma su mutunta ka’idojin da jadawalin ayyukan jam’iyyar da aka tsara domin gudanar da babban taron.

Source: Facebook
PDP: Hukuncin da kotun ta yanke
Alkalin ya amince da bukatar mai kara, inda ya umarci PDP da Damagum su ci gaba da shirye-shiryan taron kamar yadda suka tsara kafin yanke hukuncin karshe, in ji Tribune Nigeria.
Wannan hukunci na kotun ya biyo bayan takaddamar cikin gida da ta dabaibaye jam’iyyar PDP kan ko za ta ci gaba da taron ko kuma a dakatar da shi.
Da wannan sabon hukunci, watakila PDP za ta iya ci gaba da shirye-shiryenta na gudanar da babban taron zaben shugabanni na kasa a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
'Yan PDP sun yi zanga-zanga a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa rikicin shugabanci tsakanin tsagin Ministan Abuja, Nyesom Wike da bangaren Umar Damagum ya kara tsananta a PDP.
Wasu mambobin PDP sun yi zanga-zanga a babbar sakatariyar jam'iyyar PDP ta kasa da ke Wadata Plaza a Abuja ranar Litinin, 3 ga watan Nuwamba, 2025.
Masu zanga-zangar sun zargi Damagum da rashin gaskiya da karkatar da harkokin jam’iyya, suna masu rantsuwa cewa za su kwace ikon sakatariyar PDP.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


