Rikicin PDP Ya Dauki Sabon Salo, an Dakatar da Manyan Shugabannin Jam'iyyar

Rikicin PDP Ya Dauki Sabon Salo, an Dakatar da Manyan Shugabannin Jam'iyyar

  • ​Jam'iyyar ta dauki matakin ladabtarwa kan wasu masu rike da manyan mukamai a cikinta kan wasu zarge-zarge
  • PDP ta dakatar da sakatarenta na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, tare da wasu manyan jami'ai guda uku
  • Jam'iyyar ta bada umarnin ne bayan rikicin cikin gidan da ya dade yana addabarta ya ki ci ya ki cinyewa wanda hakan ke barazana da babban taronta na kasa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Rikicin da ke girgiza jam’iyyar adawa ta PDP ya dauki sabon salo bayan da aka dakatar da wasu manyan shugabanni.

Daga cikin mutanen da aka dakatar akwai sakataren PDP na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, tare da wasu jami’an jam’iyyar da ake cewa magoya bayan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ne.

PDP ta dakatar da wasu jami'anta
Shugaban PDP tare da wasu manyan jami'an jam'iyyar Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Hon. Debo Ologunagba, ne ya sanar da dakatarwar a shafin jam'iyyar na X.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: PDP ta dare gida 2, an dakatar da shugaban jam'iyya na kasa da kan shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP ta dakatar da sakatarenta na kasa

Dakatarwar na zuwa ne bayan wani dogon taro da kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) ya gudanar a hedkwatar jam’iyyar a ranar Asabar, 1 ga watan Nuwamban 2025.

Debo Ologunagba ya bayyana cewa wadanda abin ya shafa sun hada da, sakataren jam'iyya na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, sakataren tsare-tsare na kasa, Umar Bature.

Sauran sun hada da lauyan jam'iyya na kasa Kamaldeen Ajibade da mataimakin lauyan jam'iyya na kasa, Okechukwu Osuoha.

Meyasa PDP ta dakatar da shugabannin?

Ologunagba ya ce an dakatar da su ne saboda wasu manyan laifuffuka da suka sabawa kundin tsarin mulkin PDP.

“An dakatar da Sanata Samuel Anyanwu, Umar Bature, Kamaldeen Ajibade (SAN), da Okechukwu Osuoha na tsawon wata guda, tare da tura su gaban kwamitin ladabtarwa na kasa don bincike."
"A wannan lokacin, ba za su ci gaba da aiki a matsayin jami’an jam’iyyar ba.”

- Debo Ologunagba

Wata majiya ta tabbatar da cewa wadanda aka dakatar sun daina halartar tarurrukan jam’iyya tun wani lokaci da ya gabata.

Kara karanta wannan

Kotu ta jikawa PDP aiki, ta dakatar da babban taron jam'iyyar na kasa

PDP ta dakatar da Sanata Anyanwu
Sanata Samuel Anyanwu da PDP ta dakatar Hoto: Hon. Sen Samuel Anyanwu
Source: Facebook

Ana takaddama kan babban taron PDP

Hakan na zuwa ne kasa da kwanaki guda bayan babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umurci jam’iyyar da ta dakatar da gudanar da babban taronta da aka shirya a Ibadan, jihar Oyo, a ranakun 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba, 2025.

Sai dai, jam'iyyar PDP ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin kotun, amma hakan ba zai hana ta ci gaba da shirye-shirye don gudanar da taron ba.

'Yan majalisa 5 sun fice daga PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta samu koma bayan wasu mambobinta a majalisar wakilai sun sanar da ficewarsu daga cikinta.

'Yan majalisar wakilan guda biyar wadanda suka fito daga jihar Enugu sun koma jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Tsofaffin mambobin na PDP sun bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da suka addabi jam'iyyar, sun taka muhimmiyar rawa wajen yanke shawarar ficewa daga cikinta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng