Kotu Ta Jikawa PDP Aiki, Ta Dakatar da Babban Taron Jam'iyyar na Kasa

Kotu Ta Jikawa PDP Aiki, Ta Dakatar da Babban Taron Jam'iyyar na Kasa

  • PDP ta gamu da cikas a shirinta na gudanar babban taro, wanda za a zabi shugabannin jam'iyyar na kasa a watan Nuwamba, 2025
  • Babbar Kotun Tarayya ta umarci PDP ta dakatar da taron wanda ta tsara gudanarwa a Ibadan, babban birnin jihar Oyo
  • Wasu manyan jiga-jigan PDP da ake zargin suna goyon bayan Ministan Harkokin Abuja ne suka shigar da kara kan taron a gaban kotu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke zama Abuja ta dakatar da jam’iyyar PDP daga gudanar da babban taronta na kasa, wanda ta shirya yi a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Bakary: Za a gurfanar da dan adawar Kamaru da ya buga takara da Paul Biya

Mai shari’a James Omotosho ne ya bayar da wannan umarni ranar Juma'a, yayin da yake yanke hukunci kan wata kara da aka shigar gabansa.

Shugaban PDP na kasa, Umar Damagum.
Hoton shugaban PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum a hedkwatar jam'iyyar da ke Abuja Hoto: @officialPDPNigeria
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa masu shigar da karar su nemi sanin ko jam’iyyar PDP na da hurumin ci gaba da shirinta na gudanar da babban taron da aka tsara a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jiga-jigan da suka maka PDP a kotu

Wadanda suka shigar da karar sun hada da shugaban PDP na Imo, Austine Nwachukwu, takwaransa na Abia, Amah Abraham Nnanna da sakataren jam’iyyar na Kudu maso Kudu, Turnah George.

Sun bayyana Hukumar Zabe (INEC), jam’iyyar PDP, sakataren jam’iyya na kasa, Samuel Anyanwu, sakataren tsare-tsare Umar Bature, Kwamitin Gudanarwa (NWC) da Kwamitin Zartaswa na Kasa (NEC) a matsayin wadanda ake kara.

Masu karar, wadanda ake kyautata zaton magoya bayan Ministan Harkokin Abuja Nyesom Wike ne, sun nemi kotu ta dakatar da taron gaba daya.

An zargi PDP da karya dokar kasa

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya fara daukar matakin shari'a, ya kai PDP kotu kan hana shi neman takara

Sun yi zargin cewa jam’iyyar PDP ta karya kundin tsarin mulkinta, Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, da kuma Dokar Zabe, wajen shirya babban taron.

Lauyan masu kara ya shaida wa kotu cewa “ba a gudanar da zaben shugabanni a jihohi 14 ba,” don haka babu dalilin shirya babban taro na kasa.

Tutar jam'iyyar PDP.
Hoton magoya bayan PDP su na daga tuta a daya daga cikin tarukan jam'iyyar Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Sai dai PDP ta dage cewa lamarin na cikin gida ne kuma bai kamata kotu ta tsoma baki ba, tana zargin masu karar da yunƙurin kawo cikas ga tsarin sauya shugabanci cikin lumana.

Da yake yanke hukunci yau Juma'a, 31 ga watan Oktoba, 2025, Mai shari'a James Omotosho ya umarci PDP ta dakatar da shirin gudanar da babban taron, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Wike ya caccaki gwamnonin PDP

A wani labarin, kun ji cewa Nyesom Wike ya zargi gwamnonin PDP da wasa da makomar jam’iyyar, yana mai cewa irin yadda suke tafiyar da jam’iyyar, zai kai ta ga rugujewa.

Mimistan Abujan ya bayyana cewa bai yi mamaki ba ko kadan kan yadda ake yawan ficewa daga jam'iyyar domin masu jagorantar PDP sun sauka daga akidar da aka kafa ta.

Kara karanta wannan

Shugabancin PDP: Turaki ya cike fam, ya bar Sule Lamido da barazanar zuwa kotu

Wike ya yi nuni da cewa dukkan hasashen da ya yi kan abubuwan da za su faru da jam'iyyar, sai da suka auku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262