Babbar Magana: Kotu Ta Kwace Kujerar Dan Majalisar Tarayya daga Jihar Zamfara

Babbar Magana: Kotu Ta Kwace Kujerar Dan Majalisar Tarayya daga Jihar Zamfara

  • Kotu ta yanke hukuncin karbe kujerar dan Majalisar Gummi da Bukkuyum daga jihar Zamfara, Hon. Abubakar Gummi saboda ya koma APC
  • Mai Shari'a Obiora Egwuatu ya ce abin da dan Majalisar ya yi na ficewa daga jam'iyyar da ya ci zabe ya saba wa dokar Najeriya
  • Ya gargadi 'yan siyasa da cewa bai kamata su dauki sauya sheka a matsayin al'ada ba domin amana mutane suka dora masu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsige Dan Majalisar Wakilan Tarayya, Hon. Abubakar Gummi daga kujerarsa saboda sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Kara karanta wannan

Jiga jigai da 'yan Kwankwasiyya sama da 600 sun watsar da jar hula, sun koma APC a Kano

Hon. Abubakar, mai wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum daga Zamfara, ya rasa kujerarsa ne bayan da mai shari’a Obiora Egwuatu ya yanke hukunci a karar da aka shigar gabansa.

Hon. Abubakar Gummi.
Hoton dan Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Gummi Hoto: Abdulrahman Musa
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa alkalin ya yanke hukuncin cewa cewa sauya shekar da dan Majalisar ya yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC ya sabawa kundin tsarin mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta sauke dan Majalisar Wakilai

A cikin hukuncin da aka yanke ranar Alhamis, mai shari’a Egwuatu ya umurci Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, da kada ya ci gaba da karɓar Abubakar a matsayin mamba mai wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum.

Haka kuma kotun ta umurci Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC) da ta shirya sabon zabe domin cike gurbin da Abubakar Gummi ya bari cikin kwanaki 30 daga ranar yanke hukuncin.

Abin da ya faru a zaman shari'ar

Tun farko, PDP da shugabanta na jihar Zamfara, Jamilu Jibo Magayaki, ne suka shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1803/2024 domin kalubalantar sauya shekar dan Majalisar.

Masu shigar da kara, ta hannun lauyansu Ibrahim Bawa (SAN), sun yi zargin cewa Abubakar ya bar PDP ba tare da wani rabuwar kai ba, sabanin abin da Sashe na 68(1)(g) na kundin tsarin mulki ya tanada.

Kara karanta wannan

Kotu ta jikawa PDP aiki, ta dakatar da babban taron jam'iyyar na kasa

A nasa bangaren, Hon. Abubakar Gummi ya kare kansa ta hannun lauyansa, inda ya ce ya koma APC ne sakamakon rikicin cikin gida da PDP ke fama da shi a matakin kasa da na mazabarsa.

Kotu ta yi gargadi kan sauya sheka

Sai dai kotun ta yi watsi da wannan hujja, inda mai shari’a Egwuatu ya yanke hukunci cewa babu wani dalilin doka da ya halatta masa sauya sheka, don haka ya amince da bukatun masu shigar da kara.

A rahoton Vanguard, alkalin ya ce:

“’Yan siyasa su daina ganin sauya sheka a matsayin al’ada. Idan mutum yana son barin jam’iyya, kar ya tafi da amanar da mutane suka ba shi. Ba shi da ikon canja kuri’un da aka ba shi a jam’iyya guda zuwa wata jam’iyya.”
Hon. Abubakar Gummi.
Hoton tutar PDP da na dan Majalisar Gummi da Bukkuyum, Hon. Abubakar Gummi Hoto: Zaharadden Salisu
Source: Facebook

Yan Majalisa 6 daga Enugu sun koma APC

A wani labarin, kun ji cewa yan majalisar wakilai guda biyar daga jihar Enugu sun sanar da ficewarsu daga jam'iyyar PDP zuwa APC a hukumance.

Kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya karanta wasikun sauya shekar abokan aikinsa a zaman majalisar na ranar Alhamis, 30 ga watan Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan

APC ta samu rinjaye, ta kulle damar tsige Shugaban ƙasa a majalisa

Wadanda suka sauya shekarsun haɗa da, Martins Oke, Anayo Onwuegbu, Nnamdi Agbo, Nnolim Nnaji da Mark Obetta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262