Kurunkus: Gwamnan Taraba Ya Kawo Karshen Jita Jita kan Komawa Jam'iyyar APC
- Magana na ta nisa kan shirin gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, na sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC
- Gwamna Kefas ya bayyana cewa ya sanar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu aniyarsa ta komawa jam'iyyar APC mai mulki
- Matasan APC a jihar Taraba sun bayyana cewa a shirya suke su karbi Gwamna Kefas zuwa jam'iyyar APC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Taraba - Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya yi magana kan sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Gwamna Kefas ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika shi hannun shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, domin a kaddamar da shi yadda ya kamata a matsayin sabon ɗan jam’iyyar.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce Gwamna Kefas ne ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin wata ganawa da matasa da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC a T.Y. Danjuma House, Abuja.

Kara karanta wannan
APC ta jero sunayen gwamnan Filato da gwamnoni 3 da za su sauya sheka kafin karshen 2025
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Gwamna Kefas ya ce kan komawa APC?
Kefas ya ce shugaban kasa ya riga ya karɓi aniyarsa ta sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, tare da bayar da wasikar amincewa da hakan.
Gwamnan ya bayyana cewa Tinubu ya riga ya mika shi ga shugaban jam’iyyar na kasa, Yilwatda, kuma shirye-shiryen kaddamar da shi a hukumance a Taraba sun yi nisa.
Kwamared Abubakar Gembo, wanda ya yi jawabi bayan taron, ya ce matasan APC sun nuna shirinsu na tarbar gwamnan cikin farin ciki, yana mai bayyana sauya shekarsa a matsayin babban karfafa gwiwa ga jam’iyyar a jihar.
“Gwamna Kefas ya kira mu domin sanar da mu shirinsa na shiga jam’iyyar mu mai girma, APC. Ya shaida mana cewa ya gana da Shugaba Tinubu, wanda ya karɓe shi tare da mika shi hannun shugaban jam’iyyar na ƙasa."
- Kwamared Abubakar Gembo
Ya kara da cewa, gwamnan ya tabbatar wa matasan cewa za su ci gaba da taka muhimmiyar rawa a gwamnatinsa.
Ana shirin tarbar Kefas zuwa APC
Shugaban APC Youth Vanguard na Taraba, Idris Ayuba, ya tabbatar da cewa an kammala batun sauya shekar gwamnan a matakin kasa, kuma abin da ake jira kawai shi ne karɓarsa a hukumance a matakin mazaba, karamar hukuma, da jiha.
Idris Ayuba ya yi kira ga mambobin APC da matasa su goyi bayan gwamnan, yana mai bayyana shi a matsayin jigo mai kishin matasa, wanda manufofinsa suka ta’allaka kan ci gaban su da haɗin kai.

Source: Twitter
Gwamna Kefas ya gana da jiga-jigan APC
Mai magana da yawun APC Youth Vanguard na Taraba, Rikwense Muri, ya tabbatar da cewa gwamnan ya gana da manyan shugabannin matasa da masu tasiri a jam’iyyar domin samar da haɗin kai, za a iya samun labarin a rahoton Premium Times.
“Gwamna Kefas ya bayyana cewa Taraba ba za ta iya ci gaba da zama a saniyar ware daga tsarin siyasar kasa ba.”
- Rikwense Muri
Ya bayyana cewa shawarar da gwamnan ya yanke ta sauya sheka ta samo asali ne daga burinsa na ganin Taraba ta samu ci gaba, tsaro, da karin tasiri a gwamnatin tarayya.
'Yan majalisun PDP sun koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta samu nakasu a majalisar wakilai bayan wasu mambobinta sun sauya sheka zuwa APC.
'Yan majalisar wakilai guda biyar na jam'iyyar PDP a jihar Enugu sun sanar da sauya shekar su zuwa APC mai mulki.
Sun bayyana cewa sun yanke shawarar komawa APC ne saboda gamsuwa da kamun ludayin mulkin Gwamna Peter Mbah.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

