Jerin Sanatoci 11 da Za Su Iya Neman Takarar Gwamna a Zaben 2027

Jerin Sanatoci 11 da Za Su Iya Neman Takarar Gwamna a Zaben 2027

FCT, Abuja - Yayin da zaɓen 2027 ke kara matsowa, ana ganin cewa karin sanatoci za su bayyana sha’awar takarar gwamna.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Ana ganin lamarin da zai haifar da gagarumar fafatawa tsakanin gwamnonin jihohi da ‘yan majalisar da ke harin kujerunsu.

Sanatocin da za su iya neman kujerar gwamna a 2027
Sanata Saliu Mustapha, Sanata Shehu Buba Umar da Sanata Barau Jibrin Hoto: Barau I Jibrin, Musa Badamasi, Mustapha Mallick
Source: Facebook

Sanatocin da za su iya takarar gwamna

Jaridar TheCable ta tsakuro wasu sanatoci da ake hasashen suna da burin yin takarar gwamna a jihohinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin sanatocin da sun nuna alamun neman tsayawa takarar gwamna a jihohin da suka fito.

Ga jerinsu a nan kasa:

1. Umar Shehu Buba

Sanata Umar Shehu Buba da ke wakiltar Bauchi ta Kudu bai taɓa ɓoye burinsa na zama magajin Gwamna Bala Mohammed ba.

Umar Shehu Buba, wanda shi ne shugaban kwamitin tsaro da leken asiri na majalisar dattawa, na daga cikin manyan masu mukamin siyasa na jam’iyyar APC a jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya fara daukar matakin shari'a, ya kai PDP kotu kan hana shi neman takara

Masana harkokin siyasa na ganin hakan ya sanya shi cikin manyan masu iya samun tikitin jam’iyyarsa.

Jaridar The Guardian ta ce wasu magoya bayansa sun taba zuwa hedkwatar APC ta Bauchi domin neman masu ruwa da tsaki, su ba shi tikitin takarar gwamna a 2027.

2. Abdul Ningi

Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya na daga cikin masu sha’awar tsayawa takarar gwamna.

Akwai yiwuwar Sanata Abdul Ningi ya yi takarar gwamnan Bauchi a 2027
Sanata Abdul Ningi a zauren majalisar dattawa Hoto: Abdul Ningi
Source: Twitter

Ningi na da ƙwarewa, karfin siyasa da dukiya, amma har yanzu ba a tabbatar ko Gwamna Bala Mohammed zai mara masa baya ba.

Ana ganin kusancinsa da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar zai taimaka masa sosai.

3. Mohammed Tahir Monguno

Sanata Mohammed Tahir Monguno da ke wakiltar Borno Arewa, lauya ne kuma gogaggen ɗan siyasa.

Shi ne babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa ta 10 kuma tsohon babban lauyan gwamnati na jihar Borno.

Yana da goyon bayan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, kuma ya fito daga kabilar Kanuri, wadda ta fi rinjaye a jihar.

Masu lura da siyasa na ganin yana da cikakkiyar dama ta zama magajin Gwamna Babagana Zulum.

Kara karanta wannan

2027: Gwamnonin Arewa 3 na tsaka mai wuya game da barin PDP zuwa APC

4. Kaka Shehu Lawan

Sanata Kaka Shehu Lawan mai wakiltar Borno ta Tsakiya yana da karfi a siyasar Borno.

Ana ganin kusancinsa da Kashim Shettima na daga cikin manyan abubuwan da za su taimaka masa wajen zama magajin Gwamna Zulum.

A baya an samu Ali Modu Shariff wanda ya yi gwamna bayan ya taba zama sanata.

5. Barau Jibrin

Ana ganin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, shi ne ɗan APC mafi ƙarfi da zai iya kalubalantar Kwankwasiyya.

Tun bayan zama mataimakin shugaban majalisar, Barau ya ja wasu 'yan siyasa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, domin karfafa shirin kalubalantar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ana ganin idan Barau wanda ya fito daga Arewacin Kano ya samu goyon bayan Shugaba Bola Tinubu, yana da babbar damar samun nasara a 2027.

6. Saliu Mustapha

Sanatan Saliu Mustapha mai wakiltar Kwara ta Tsakiya, shi ne shugaban kwamitin noma na majalisar dattawa.

A matsayinsa na Turakin Ilorin, ya samu sabani da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, inda aka cire allunan kamfen dinsa daga wurare da dama.

Kara karanta wannan

Shugabancin PDP: Turaki ya cike fam, ya bar Sule Lamido da barazanar zuwa kotu

Tawagar matasa da masu kananan sana’o’in na ba shi goyon baya sosai.

7. Suleiman Sadiq Umar

Sanata Suleiman Sadiq Umar wanda ake yi wa lakabi da 3SU, mai wakiltar Kwara ta Arewa na daga cikin mutanen da ake hasashen za su nemi takarar gwamna.

Ana ganin zai iya yin katabus saboda kyakkyawar dangantakarsa da gwamna AbdulRazaq, da kuma rashin samun gwamna daga yankin Kwara ta Arewa tun 1999.

8. Tokunbo Abiru

Ana ganin Sanata Tokunbo Abiru mai wakiltar Legas ta Arewa, yana daga cikin sababbin sanatoci masu aiki sosai.

Ya dauki nauyin kudirori masu muhimmanci a fannin kudi, ciki har da sabuwar dokar Inshora.

Ana tunanin yana iya zama magajin Gwamna Babajide Sanwo-Olu saboda kwarewar da yake da ita.

9. Aliyu Wadada

Ana hasashen Sanata Aliyu Wadada, mai wakiltar Nasarawa ta Yamma zai tsaya takarar gwamna a Nasarawa.

Sanatan mai rike da sarautar Magajin Dangin Lafia, yana da goyon bayan jama'a da kuma kusanci da fadar shugaban kasa.

Masu lura da siyasa na cewa dawowarsa cikin APC alama ce ta niyyarsa ta hawa karagar gwamna a 2027.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kebbi ya yi garambawul, ya sauyawa wasu kwamishinoni ma'aikatu

10. Solomon Adeola

Sanata Solomon Adeola, wanda ake kira “gwamna mai jiran gado”, shi ne shugaban kwamitin kasafin kuɗi kuma amini ne na Shugaba Tinubu.

Sanata Solomo Adeola na shirin yin takarar gwamna a 2027
Sanata Solomon Adeola mai wakiltar Ogun ta Yamma Hoto: Senator Solomon Olamilekan Adeola
Source: Facebook

Ana ganin yana da gagarumar dama saboda matsin lambar jama’ar Ogun ta Yamma na a kai kujerar gwamna yankinsu.

11. Buhari Abdulfatai

Sanata Buhari Abdulfatai mai wakiltar Oyo ta Arewa ya bayyana aniyarsa ta zama magajin Gwamna Seyi Makinde, rahoton shafin Oyoaffairs ya tabbatar da hakan.

Shugaban kwamitin sufurin jiragen sama yana wa’adinsa na uku a majalisar dattawa kuma yana daga cikin manyan ‘yan APC daga Ogbomosho tun bayan rasuwar tsohon gwamna Adebayo Alao-Akala.

Ana cewa yana da goyon bayan mutane masu tasiri a fadar Aso Rock. Babu mamaki ya nemi ganin bayan mulkin PDP a jihar Oyo a 2027.

Sanatan PDP ya koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Bayelsa ta Gabas, Benson Adagada, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

An gano daloli, motoci da alfarma da Tinubu ya ware wa korarrun hafsoshin tsaro

Sanata Benson Adagada ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, bayan ya fice daga PDP.

Ya bayyana cewa ya raba gari da jam'iyyar PDP ne saboda rikice-rikicen cikin gida da suka addabe ta wadanda suka rage mata farin jini a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng