APC Ta Jero Sunayen Gwamnan Filato da Gwamnoni 3 da Za Su Sauya Sheka kafin karshen 2025

APC Ta Jero Sunayen Gwamnan Filato da Gwamnoni 3 da Za Su Sauya Sheka kafin karshen 2025

  • Akwai yiwuwar wasu gwamnonin jihohi hudu a Arewa da Kudancin Najeriya za su bar jam'iyyun adawa zuwa APC kafin karshen 2025
  • Mataimakin shugaban APC na kasa (Kudu maso Gabas), Dr. Ijeoma Arodiogbu ya ce tattaunawa da gwamnonin ta kai matakin karshe
  • Daga cikin gwamnonin da ya ambaci sunayensu akwai Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato da Gwamna Simi Fubara na Ribas

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - APC ta bayyana cewa akalla gwamnoni hudu daga jam’iyyun adawa na tattaunawa ta karshe domin shiga jam’iyya mai mulki kafin ƙarshen shekarar 2025.

Kara karanta wannan

Magana ta fara Tabbata, Gwamna Agbu Kefas zai sauya sheka zuwa APC mai mulki

Wannan lamari a cewar jam’iyyar APC, zai kara ƙarfafa matsayinta a fagen siyasar ƙasar nan gabanin babban zaben 2027 mai zuwa.

Jam'iyyar APC.
Hoton tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: @officialAPCNig
Source: Getty Images

Tribune Nigeria ta tattaro cewa mataimakin shugaban APC na Kasa (Kudu maso Gabas), Dr. Ijeoma Arodiogbu, ne ya bayyana hakan a wata hira da menama labarai ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnoni 4 da ka iya komawa APC

Ya ce gwamnonin jihohin Filato, Taraba, da Ribas daga PDP da gwamnan Abia na LP, sun shiga tattaunawa da APC domin cimma matsaya kafin su sauya sheka.

Arodiogbu ya bayyana cewa da yiwuwar wadannan gwamnoni su shigo cikin APC a makonni kadan masu zuwa.

“Da yiwuwar gwamnan Filato, Caleb Mutfwang ya shiga jam’iyyarmu, haka ma na Taraba, Agbu Kefas.
"Muna kuma sa ran karɓar gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara, da gwamnan Abia, Alex Otti, wadanda za su hade da mu a APC,” in ji Arodiogbu.

APC na sa ran karbar gwamnonin a 2025

Arodiogbu ya ƙara da cewa:

Kara karanta wannan

2027: Gwamnonin Arewa 3 na tsaka mai wuya game da barin PDP zuwa APC

“Wannan abu ne da zai yiwu, kuma muna sa ran hakan zai faru kafin mu gudanar da babban taron APC. Ina tsammanin galibin wadannan gwamnoni za su sauya sheka kafin karshen 2025.
"Idan hakan ya tabbata, za mu kara tabbatar da cewa APC ce jam’iyya mafi ƙarfi da tsari a Najeriya.”

Mataimakin shugaban APC ya ce manufofi da shirye-shiryen gyaran tattalin arziki na gwamnatin Bola Tinubu, su ke ƙara jan hankalin shugabanni daga jam’iyyun adawa, cewar rahoton Daily Post.

“Gaskiyar magana ita ce, APC ta zama gida ga dukkan masu kishin ci gaba. Ba kawai muna ƙaruwa da yawan mutane ba ne, muna kuma ƙara samun shugabanni masu inganci," in ji shi.
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe.
Hoton shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe a ofishinsa da ke Abuja Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

A karshe, Dr. Arodiogbu ya ce shigowar wadannan gwamnoni cikin APC za ta ƙara ƙarfafa jam’iyya mai mulki a shirye-shiryenta na tarukan zaben shugabanni a 2025 da kuma zaben 2027.

Sanata daga Bayelsa ya koma APC

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Benson Agadaga, mai wakiltar Bayelsa ta Gabas ya tabbatar da sauya sheka daga PDP zuwa APC a zaman Majalisar Dattawa.

Agadaga ya bayyana cewa ya bar PDP ne saboda rikice-rikicen cikin gida da suka lalata jam’iyyar kuma suka rage mata farin jini a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Borno ta APC ce," Gwamna Zulum ya tuna alherin da Buhari da Tinubu suka kawo a Arewa

Bayan karanta wasikar sanatan a zaman Majalisar Dattawa, ‘yan majalisar APC sun taya shi murna tare da raka shi har kujerarsa a bangaren masu rinjaye.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262