"Laima Ta Yage,' Sanata Agadaga Ya Kara Ruguza PDP, Ya Sauya Sheka zuwa APC

"Laima Ta Yage,' Sanata Agadaga Ya Kara Ruguza PDP, Ya Sauya Sheka zuwa APC

  • Jam'iyyar APC mai mulkin kasar nan ta samu karuwa a Majalisar Dattawa da Sanata Benson Agadaga ya raba gari da PDP
  • Sanata Benson Agadaga, mai wakiltar Bayelsa ta Gabas ya tabbatar da sauya sheka daga PDP zuwa APC a hukumance
  • 'Yan APC a Majalisar Dattawa ciki har da Sanata Godswill Akpabio sun taya Agadaga murna a zaman yau Laraba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Sanata Benson Agadaga mai wakiltar mazabar Bayelsa ta gabas a Majalisar Dattawa ya sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Akpabio ya gano matsalar da ke hana mata lashe zabe a Najeriya

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya karanta wasikar sauya shekar sanatan a ƙarshen zaman yau ranar Laraba.

Sanata Benson Agadaga.
Hoton Sanata Benson Agadaga a ofishinsa na Majalisar Dattawa Hoto: @OfficialDanAtim
Source: Twitter

Me yasa Sanata Agadaga ya bar PDP?

Sanata Agadaga ya bayyana cewa ya bar PDP ne saboda rikice-rikicen cikin gida da suka lalata jam’iyyar kuma suka rage mata farin jini a Najeriya da nahiyar Afirka, in ji rahoton Premium Times.

'Dan Majalisar Dattawan ya soki PDP da cewa alamarta ta laima ta fashe kuma ta tsage, sannan a cewarsa, jam'iyyar ta rasa mutuncin da take da shi a idon jama'a

“Abu ne mai ban mamaki da takaici ganin jam’iyyar da ake taƙama da ita a Afirka ta yi rugu-rugu saboda rikicin cikin gida. Laimar PDP ta karye, sannan a yanzu ba ta iya kare mutane daga zubar ruwa.
"Na fahimci cewa tunani na ci gaba da aiki bisa manufofi masu kyau su ne hanyar da za ta sake gina fata ga ‘yan Najeriya, saboda haka, na yanke shawarar fita daga jam’iyyar PDP,” in ji shi.

Yadda APC ta kama jihar Bayelsa

Kara karanta wannan

PDP ta samu koma baya a Zamfara, dan majalisarta ya sauya sheka zuwa APC

Sauyin shekar Sanata Agadaga na zuwa ne a daidai lokacin da wasu fitattun ‘yan siyasa daga Bayelsa ke barin PDP.

A ‘yan makonnin da suka gabata, Gwamna Douye Diri ya fice daga jam’iyyar PDP, haka kuma Sanata Konbowei Benson mai wakiltar Bayelsa ta Tsakiya ya koma APC.

Da wannan sabon mataki, tsohon gwamnan jihar, Sanata Seriake Dickson mai wakiltar Bayelsa ta Yamma, shi ne kaɗai sanatan PDP da ya rage a Bayelsa.

Jihar Bayelsa dai ta daɗe a matsayin wani ginshiƙin PDP tun bayan komawar ƙasar mulkin dimokuraɗiyya, amma yanzu al'amura sun sauya.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akoabio.
Hoton shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Yan APC sun taya Sanata Agadaga murna

Bayan karanta wasikar sanatan, ‘yan majalisar APC sun taya shi murna tare da kai shi kujerarsa a bangaren masu rinjaye.

Haka zalika shugaban majalisar, Sanata Akpabio, ya taya shi murna tare da maraba da shi cikin jam’iyya mai mulki watau APC, kamar yadda The Cable ta kawo.

Abin da ke jawo sanatoci zuwa APC

A wani labarin, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya ce yan siyasa na tururuwar komawa APC ne saboda kishin kasa da amincewa da jagorancin Tinubu.

Kara karanta wannan

Shugabancin PDP: Turaki ya cike fam, ya bar Sule Lamido da barazanar zuwa kotu

A cewar Akpabio, sauya shekar da ake ganin sanatoci na yi na kara nuna yadda jama'a suka gamsu da tsare-tsaren tattalin arziki na gwamnatin APC.

Ya ce manufofin Shugaba Tinubu na farfado da tattalin arzikin Najeriya sun fara haifar da da mai ido, kuma hakan ke jawo yan siyasa zuwa jam'iyya mai mulki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262