Magana Ta Fara Tabbata, Gwamna Agbu Kefas Zai Sauya Sheka zuwa APC Mai Mulki
- Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas zai fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya domin samar da ci gaba ga al'ummarsa
- Mai ba gwamnan shawara kan harkokin siyasa, Josiah Kente, ya bukaci masu ruwa da tsaki a Taraba su karawa wannan mataki baya
- Ya ce Gwamna Kefas zai koma APC je ba don son rai ko wata riba da zai samu ba, sai don samun ayyuka daga gwamnatin tarayya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jalingo, Jihar Taraba – Alamu sun fara tabbatar da rade-radin da ake yadawa cewa gwamnan Taraba, Agbu Kefas na zai sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Kara karanta wannan
"Borno ta APC ce," Gwamna Zulum ya tuna alherin da Buhari da Tinubu suka kawo a Arewa
Mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin siyasa, Josiah Kente, ya bayyana cewa komawar Gwamna Kefas APC zai kawo gagarumin ci gaba ga jihar Taraba.

Source: Twitter
Mista Kente ya fadi haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 28 ga watan Oktoba, 2025 a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, innji rahoton Punch.
Dalilin Gwamna Kefas na komawa APC
Kente ya ce hadewar Gwamna Kefas da jam’iyyar APC wata dabara ce da za ta kara shigar da Jihar Taraba cikin tsarin ci gaban ƙasa da samun karin dama daga gwamnatin tarayya.
Ya bayyana cewa wannan yunƙuri ba shi da alaka da son kai ko ribar siyasa, illa kawai lalubo hanyar cika bukatun jama’ar Taraba baki ɗaya.
Hadimin gwamnan ya jaddada cewa nasarorin Agbu Kefas a fannin ilimi, lafiya, da gine-gine sun cancanci ƙarin tallafi daga gwamnatin tarayya, kuma hakan za ta samu ne idan ya koma APC.
"Wannan ba abu ne na siyasa kadai ba, shi ne muradin jama’an Taraba don samun ci gaba mai ɗorewa, gyaran muhimman abubuwa, da shiga cikin harkokin ƙasa,” in ji Kente.
Hanyoyin da Taraba za ta amfana
Ya ƙara da cewa idan gwamnan Taraba ya koma jam’iyya mai mulki, hakan zai buɗe sababbin hanyoyin ci gaba, musamman ta fuskar aikin gwamnati na tarayya, tsaro, da tallafin ƙasashen waje.
A ruwayar Daily Post, Josiah Kente ya ce:
“Idan Gwamna Kefas ya koma APC, Taraba za ta samu ƙarin ayyuka kamar hanyoyi, gadoji, asibitoci da wutar lantarki, waɗanda yanzu sun fi mai da hankali a jihohin da ke da kusanci da gwamnatin tarayya."
Ya yi kira ga shugabannin siyasa, kungiyoyin matasa da masu ruwa da tsaki a Taraba da su mara wa Gwamna Kefas baya a shirinsa na komawa APC, wanda ya kira da "daidaituwa da tarayya don samun ci gaba."

Source: Twitter
An zabi Gwamna Agbu Kefas a 2023 a karkashin jam’iyyar PDP, kuma idan ya sauya sheƙa zuwa APC, hakan zai zama babban juyin siyasa a Taraba.
Jihar Taraba ta kasance garkuwa a jam’iyyar PDP tsawon shekaru 26 tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999.
Agbu Kefas ya kashe N5.22bn a tafiye-tafiye
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Taraba ta laryata rahoton da ke cewa Gwamna Agbu Kefas, ya kashe Naira biliyan 5.22 a tafiye-tafiye zuwa kasashen waje.
Tun farko dai an yada jita-jitar cewa gwamnan ya kashe wadannan makudan kudi wajen tafiye-tafiyen da ya yi zuwa kasashen ketare a watanni shida kacal.
Sai dai gwamnatin Taraba ta musamta labarin ta hannun kwamishinar yada labarai, Zainab Jalingo, tana mai cewa rahoton da ake yadawa karya ce da yaudara.
Asali: Legit.ng

