Turaki, Sule Lamido da Wasu Manyan Jiga Jigan Arewa 2 da Ka Iya Neman Shugabancin PDP
Babbar jam'iyyar adawa watau PDP na ci gaba da shirye-shiryen babban taronta na kasa wanda zai gudana a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
A wannna taro ne, masu ruwa da tsakin PDP daga lungu da sako na kasar nan za su hadu su zabi sababbin shugabannin jam'iyyar na kasa.

Source: Twitter
Kamar yadda The Nation ta rahoto, PDP ta shirya gudanar da wannan taro ne a ranakun Asabar, 15 da Lahadi, 16 ga watan Nuwamba, 2025.
PDP ta ba Kudu takarar shugaban kasa
Jam'iyyar PDP ta yanke shawarar mika tikitin takarar shugaban kasa na zaben 2027 ga yankin Kudu, domin tabbatar da daidaito da adalci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon Ministan Yada Labarai, Farfesa Jerry Gana ne ya bayyana haka bayan taron masu ruwa da tsakin PDP da ya gudana a watan Yuli, 2025, in ji rahoton Vanguard.
A cewarsa, sun dauki wannan matakin ne domin warware duk rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar, wanda ya samo asali daga zaben shugaban kasa na 2023.
An ba Arewa kujerar shugaban PDP
Wannan mataki da PDP ta dauka na kai tikitin takara Kudu, ya bai wa Arewa damar fitar da sabon shugaban jam'iyya na kasa.
Sai dai kan jagororin PDP ya fara rabuwa kan wanda za su hadu su marawa baya domin ya zama dan takarar masalaha daga Arewacin Najeriya.
PDP: 'Yan Arewa da ka iya neman takara
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku jiga-jigan PDP daga Arewa da ake ganin sun cancanci karbar ragamar shugabancin jam'iyyar a babban taron da za a yi a jihar Oyo.
1. Kabiru Tanimu Turaki
Tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabiru Tanimu Turaki, shi ne a sahun gaba cikin wadanda za su nemi kujerar sshugaban PDP na kasa.
Shugabannin PDP daga Arewa, ciki har da gwamnoni, sun amince da Turaki, a matsayin dan takararsu na kujerar shugaban jam'iyya.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa wasu jagororin PDP na Arewa sun cimma wannan matsaya ne a wani taro da suka gudanar a Abuja.
Da yake jawabi bayan taron, Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya ce:
“Manufar wannan amincewa ita ce tabbatar da daidaito da hadin kai kafin babban taron. Sauran mukamai kuma za a tattauna su ne a matakin yankuna."

Source: Facebook
Sai dai wannan mataki ya kawo rabuwar kai a tsakanin masu ruwa da tsakin PDP a Arewa, inda shugabannin jam'iyyar na Arewa maso Yamma suka yi fatali da Turaki.
A wani taron menama labarai da suka kira a Abuja, sakataren tsare-tsaren PDP na kasa, Umar Bature ya ce amincewa da Turaki ba shi da tushe kuma ba ya wakiltar matsayar Arewa gaba daya.
2. Sule Lamido
Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, na ɗaya daga cikin wadanda suka kafa PDP tun 1998, yana da dogon tarihi a cikin jam’iyyar.
Sule Lamido ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar kujerar shugaban PDP na kasa a babban taron zaben shugabanni da za a gudanar a Ibadan, Jihar Oyo.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, Lamido ya tabbatar da cewa zai sayi fom ɗin takara daga hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza, Abuja.

Source: Twitter
Lamido ya bayyana cewa burinsa shi ne mayar da jam’iyyar PDP zuwa martabarta da aka sani tun usuli watau abar koyi a tsarin dimokuraɗiyya.
“Kudurin da nake da shi na kare dimokuraɗiyya da dawo da jam’iyyarmu zuwa darajarta ta baya ba zai taɓa yankewa ba,” in ji shi.
Sai dai lokacin da Sule Lamido ya je hedkwatar PDP domin sayen fam, rahotanni sun nuna cewa shugahannin jamiyyar sun hana shi.
Hakan ya sa ya sha alwashin shigar da kara kotu domin neman hakkinsa da ya ce PDP na neman tauye masa.
3. Malam Ibrahim Shekarau
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau na daya daga cikin wadanda ake hasashen za su nemi shugabancin PDP bayan kawo kujerar Arewa.
Duk da Shekarau bai fito ya bayyana cewa zai nemi mukamin ba, amma a wata hira da ya yi da BBC Hausa, tsohon gwamnan ya ce bai kamata PDP ta hana wasu yayanta takara ba.
Ya ce ya kamata shugabanin PDP su bar ƙofarsu a buɗe ga dukkan wani ɗan jam'iyyar da ya nuna sha'awar tsayawa takarar kowanne muƙami don tabbatar da dimokaraɗiyya a cikin gida.

Source: Facebook
4. Sanata Ahmed Makarfi
Tsohon gwamnan Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi na cikin wadanda ake ganin za su nemi zama shugaban PDP a babban taron jam'iyyar mai zuwa.
Hakan ya biyo bayan matsayar da jagororin jam'iyyar a Arewa suka dauka na zabo wanda zai shugabanci PDP daga Arewa maso Yamma.
Wasu majiyoyi sun shaida wa Punch cewa Sanata Makarfi na cikin wadanda ake ganin za su iya kawo sauyi a PDP idan har ya zama shugaban jam'iyyar na kasa.
A cewar wata majiya, Saminu Turaki da Ahmed Makarfi, su ne a sahun gaba a cikin wadanda shugabannin PDP na Arewa ke tunanin tsaidawa takara kafin taron watan Nuwamba, 2025.

Source: Facebook
Kotu ta dakatar da taron PDP
A wani labarin, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke zama Abuja ta dakatar da jam’iyyar PDP daga gudanar da babban taronta na kasa.
Wasu manyan jiga-jigan PDP da ake zargin suna goyon bayan Ministan Harkokin Abuja ne suka shigar da kara kan taron a gaban kotu.
Da yake yanke hukunci ranar Juma'a, 31 ga watan Oktoba, 2025, Mai shari'a James Omotosho ya umarci PDP ta dakatar da shirin gudanar da babban taron har sai ta cika ka'idoji.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



