ADC Ta Raba Gardama kan Rikicin Shugabancin Jam'iyyar a Adamawa

ADC Ta Raba Gardama kan Rikicin Shugabancin Jam'iyyar a Adamawa

  • Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta tsinci kanta cikin rikicin shugabanci a jihar Adamawa w​anda hakan ya sa aka samu bangarori
  • Sai dai, shugabancin jam'iyyar na kasa ya shiga cikin lamarin inda ya bayyana shugaban da ya amince da shi na reshen jihar
  • Mai magana da yawun jam'iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa an amince da shugabancin ne domin tabbatar da gaskiya da adalci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Adamawa - Jam’iyyar ADC ta tsoma baki cikin rikicin shugabanci da ke addabar reshenta na Jihar Adamawa.

Jam'iyyar ADC mai hamayya ta amince da Sadiq Dasin a matsayin shugaban rikon kwarya na jihar Adamawa.

ADC ta fadi shugabanta a jihar Adamawa
Sakataren yada labaran ADC, Mallam Bolaji Abdullahi da tambarin jam'iyyar Hoto: @BolajiADC
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakinta na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

ADC ta rabu gida 3 kowanne bangare ya ja daga a Adamawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar ADC ta rabu a jihar Adamawa

Legit Hausa ta rahoto cewa jam’iyyar ta rabu gida biyu saboda takaddama kan shugabancin a jihar.

Wangare yana karkashin jagorancin Sadiq Dasin, yayin da ɗaya bangaren ke karkashin Saidu Komsiri.

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya bayyana cewa bangaren da Dasin ke jagoranta shi ne sahihin shugabancin jam’iyyar.

Haka kuma, manyan ’yan siyasa kamar tsohon Gwamna Jibrilla Bindow, Sanata Abdul-Aziz Nyako, da Sanata Elisha Abbo, sun nuna goyon bayansu ga bangaren Dasin.

Hatta tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana goyon bayansa ga jagorancin Dasin.

Sai dai bangaren Komsiri, wanda ake cewa tsohuwar Sanata kuma ‘yar takarar gwamna, Aisha Binani ke mara wa baya, ya ki amincewa, yana mai cewa su ne sahihin shugabannin jam’iyyar a jihar.

Wane bangare ADC ta amince da shi?

A cikin sanarwar da Mallam Bolaji Abdullahi ya fitar, ADC ta tabbatar da Sadiq Dasin a matsayin shugaban rikon kwarya na jam’iyyar a Adamawa.

Kara karanta wannan

Shugabar LP ta kasa ta samu mukami a jam'iyyar hadaka, ADC ta yi nade made 2 a Kaduna

“Hankalin hedkwatar jam'iyyar ADC ta kasa ya kai ga cewa akwai rabuwar kai a cikin shugabancin jam’iyyar a jihar Adamawa."
“Idan za a tuna cewa a taron da aka gudanar ranar 8 ga Oktoba, 2025, kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) ya amince da kafa kwamitocin rikon kwarya a jihohi don gudanar da harkokin jam’iyya na ɗan lokaci.”
“Bayan bincike, jam’iyyar ta tabbatar da cewa zaben da aka gudanar ranar Asabar, 25 ga Oktoba, karkashin jagorancin mataimakin shugaban jam’iyya na Arewa maso Gabas, wanda ya haifar da Sadiq Dasin a matsayin shugaban rikon kwarya, ya yi daidai da amincewar NWC da ka’idojin jam’iyya.”

- Mallam Bolaji Abdullahi

ADC ta yi gargadi kan mambobinta a Adamawa
Mai magana da yawun ADC na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi Hoto: @BolajiADC
Source: Facebook

Jam’iyyar ta bukaci dukkan ’ya’yanta da suka shiga wani tsari daban su nemi sulhu kuma su koma tafarkin haɗin kai.

Haka kuma, ta shawarci sabon shugaban rikon kwarya da ya yi kokarin haɗa kan dukkan ’ya’yan jam’iyyar tare da sauraron korafe-korafensu.

“Jam’iyyar na nan daram wajen tabbatar da gaskiya da adalci ga kowa, amma ba za ta lamunci rashin ladabi ko ayyukan da za su lalata kokarin gina jam’iyya mai karfi da ingantacciyar dimokuradiyya ba."

Kara karanta wannan

Turaki ya kara fuskantar matsala a shirin zama shugaban PDP na kasa

- Bolaji Abdullahi

​ADC ta gargadi Atiku Abubakar

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC reshen jihar Adamawa ta aika da sakon gargadi ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Jam'iyyar ta bukaci Atiku Abubakar da ya je mazabarsa domin yankan katin zama cikakken mamba a cikinta.

Shugaban jam'iyyar na jihar Adamawa, Shehu Yohana, ya ce babu wanda zai ci gaba da yanke shawara a madadin jam’iyya alhali ba shi da rijista.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng