ADC Ta Rabu Gida 3, Kowanne Bangare Ya Ja Daga a Adamawa
- 'Yan hamayyar ADC reshen Adamawa sun rabu gida uku, kowanne bangare yana ikirarin shi ne sahihin shugaban jam’iyyar a jihar
- Rikicin ya haɗa magoya bayan tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, da na Sanata Aishatu Dahiru Binani
- Sai kuma a gefe guda, shugaban jam’iyyar na yanzu, Shehu Yohanna, inda dukkaninsu ke adawar shugabancin daya bangaren
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Adamawa – Rikici ya kunno kai cikin jam’iyyar ADC a jihar Adamawa, inda aka samu sabani tsakanin bangarorin uku masu ikirarin shugabanci.
Bangaren tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya amince da Sadiq Dasin a matsayin shugaban jam’iyyar.

Source: Facebook
Dailyt Trust ta wallafa cewa Sanata Aishatu Dahiru Binani suka goyi bayan Saidu Komsiri. Sai kuma shugaba na yanzu, Shehu Yohanna, wanda ya dage cewa shi ne halastaccen shugaba.

Kara karanta wannan
Shugabar LP ta kasa ta samu mukami a jam'iyyar hadaka, ADC ta yi nade made 2 a Kaduna
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An samu sabanin shugabanci a ADC
Trust radio ta wallafa cewa Saidu Komsiri ya musanta cewa jam’iyyar ta rabu gida uku, yana mai cewa kafafen yada labarai ne suka kara wa lamari armashi.
Ya ce:
“Abin da muke da shi ba bangaranci bane, abin da ke akwai shi ne tsofaffin tsarin shugabanci biyu — na Shehu Yohanna da na Mustapha Arabi — wadanda kwamitin kasa na ADC ya riga ya shiga tsakani.”
Saidu Komsiri ya bayyana cewa shugabannin ADC na kasa sun kafa kwamitocin wucin gadi a duk jihohi domin tabbatar da daidaito.
Ya kara da cewa daga ciki har da kwamitin rikon kwarya da ke kula da harkokin yau da kullum da shirya zaben jam’iyya kafin 2026.
Yohanna na takaddama kan shugabancin ADC
Shehu Yohanna, wanda ke jagorantar jam’iyyar a yanzu, ya ce labarin bangaranci karya ne, saboda har yanzu shi ne shugaban jam'iyya.

Source: Twitter
A kalamansa:
“Abin da ke faruwa tsakanin masu karfi da talakawan jam’iyya ne. Wasu manyan mutane na kokarin karbe ikon jam’iyya ta hanyar kafa kwamitoci na bogi.”
Yohanna ya kuma jaddada cewa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, bai taba shiga ADC ba, duk da jita-jitar da ke yawo.
Ya ce:
“Atiku ba ya da katin zama 'dan ADC, don haka ba zai iya jagorantar abin da ke faruwa cikin jam’iyyar da bai shiga ba."
Sai dai Umar Bello Jada, Sakataren kula da shirye-shirye a yankin Arewa maso Gabas na ADC, yana goyon bayan Atiku ga Sadiq Dasin ba ya soke halascin Saidu Komsiri.
ADC: Ana yi mana makarkashiya
A baya, mun wallafa cewa shugaban riƙo na ADC, David Mark, ya bayyana cewa jam’iyyar APC na shirin yin amfani da karfin gwamnati da tsarin shari’a domin dakile cigaban jam'iyyar.
Ya bayyana cewa jam'iyyar ADC ta zama barazana ga masu mulki a yanzu, wanda ya sa ake shirin dakile hasken tauraruwarta ta hanyar kotu da sauran dabarun amfani da hukumomi.
Sai dai tawagar lauyoyin ADC na kasa ta bayyana cewa ta akwai lauyoyi 310 da suka sa hannu domin kare jam’iyyar a duk wata shari’a da za ta shafe ta a fadin Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

