Sule Lamido Ya Fara Daukar Matakin Shari'a, Ya Kai PDP Kotu kan Hana Shi Neman Takara

Sule Lamido Ya Fara Daukar Matakin Shari'a, Ya Kai PDP Kotu kan Hana Shi Neman Takara

  • Tsohon gwamna, Sule Lamido ya fara daukar matakin shari’a don kalubalantar hana shi damar samun fam din takara a PDP
  • Rahotanni sun ce Sule Lamido ya hadu da lauyoyinsa a ranar Talata inda aka fara hada takardun da za a shigar da kara a gaban kotu
  • Hukumar shirya taron jam’iyyar ta dage aikin tantance ‘yan takara, yayin da rikicin ke ci gaba da yamutsa jam'iyyar gabanin taron

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Jigawa – Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya fara shigar da kara don kalubalantar yadda aka hana shi shiga cikin jerin wadanda za su nemi mukamin shugaban PDP.

Rahotanni sun bayyana cewa Sule Lamido ya hadu da lauyoyinsa a ranar Talata inda ya rattaba hannu a kan takardar da ake sa ran za a mika a gaban babbar kotun tarayya a a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

'Abin da zai faru da Sule Lamido idan ya shiga shari'a da jam'iyyar PDP'

Sule Lamido ya tafi kotu
Sule Lamido Ya Fara Daukar Matakin Shari'a, Ya Kai PDP Kotu kan Hana Shi Neman Takara
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa hakan na zuwa ne yayin da Lamido ya zargi jam’iyyarsa da tauye masa hakki na neman fam din takara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP ta yi martani ga Sule Lamido

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ba za ta ar wasu fusattu su hana a gudanar da taronta na kasa ba, duk da barazanar shari’ar da Lamido ya dauka.

Kwamitin shirya taron NCOC ya sanar da dakatar da aikin tantance ‘yan takara da aka shirya a ranar 28 ga Oktoba ba tare da sanya sabon lokaci ba.

Sule Lamido ya fusata
Hoton Sule Lamido, daya daga cikin wadanda suka kafa PDP Hoto: Sule Lamido
Source: Facebook

A gefe guda kuma, kotu za ta fara sauraron karar da wasu shugabannin jihohi suka shigar don dakatar da taron jam’iyyar a ranar 30 ga Oktoba.

Rikicin PDP na shirin jawo mata matsala

A lokaci guda, an samu sabon rikici dake kokarin ballewa, inda Samuel Anyanwu ke zargin cewa an yi satar sa hannunsa a wasu takardun da aka kai ga INEC.

Kara karanta wannan

PDP ta yi wa Sule Lamido martani mai zafi kan barazanar kai ta kara kotu

Amma kwamitin kwamitin amintattu na jam'iyyar ya musanta wannan ikirari, inda suka bayyana cewa ya sa hannunsa da kansa.

Wannan rikici na cikin gida na PDP na iya jefa taron na Nuwamba 15-16 a Ibadan, jihar Oyo State cikin hadari idan ba a dauki mataki da wuri ba.

Wadannan rikice-rikice na zuwa ne a lokacin da karfin jam'iyyar ke sake raguwa, inda manyan cikinta ke sauya sheka zuwa wasu jam'iyyun, musamman APC mai mulki.

Turaki ya kai fam na takarar PDP

A baya, mun wallafa cewa Kabiru Tanimu Turaki, ya mika fam ɗinsa na tsayawa takarar shugabancin PDP a ranar Litinin a ofishin kwamitin shirya babban taron jam’iyyar da ke Abuja.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Turaki ya kai takardunsa tare da magoya-bayansa kuma ya samu goyon bayan wasu manyan shugabannin jam’iyyar musamman daga Arewa.

Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana takaici bayan ya je ofishin jam’iyyar zuwa sayen fam ɗin takara sai ya tarar babu wanda ke sauraron masu neman fam ko ofishin a rufe.

Kara karanta wannan

Shugabancin PDP: Turaki ya cike fam, ya bar Sule Lamido da barazanar zuwa kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng