"Borno Ta APC ce," Gwamna Zulum Ya Tuna Alherin da Buhari da Tinubu Suka Kawo a Arewa

"Borno Ta APC ce," Gwamna Zulum Ya Tuna Alherin da Buhari da Tinubu Suka Kawo a Arewa

  • Gwamna Babagana Umaru Zulum ya tabbatar da cewa jihar Borno na tare da APC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027
  • Mai girma gwamnan ya ce Borno da Arewa maso Gabas gaba daya ba za su manta da marigayi Muhammadu Buhari da Tinubu ba
  • Ya ce kowa ya san Borno ta APC ce tun asali kuma babu abin da zai sauya hakan, yana mai tuna halin da jihar ta shiga a baya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Maiduguri, Jihar Borno – Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jaddada cikakken goyon bayan jiharsa ga APC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya fadi dalilin da zai saka Arewa ta zubawa Tinubu kuri'a a 2027

Gwamna Babagana Zulum ya bayyana cewa Borno ta kasance gidan jam'iyyar APC kuma za ta ci gaba da zama a haka ba tare da hamayya ba.

Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum.
Hoton Gwamna Babagana Umaru Zulum a wurin taro Hoto: @ProfZulum
Source: Twitter

Zulum ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin ƙaddamar da aikin sabunta rijistar yan APC na yankin Arewa maso Gabas wanda aka yi a Maiduguri, kamar yadda Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zulum ya kaddamar da rijistar 'yan APC

Taron ya tattaro manyan jiga-jigan jam’iyyar APC daga matakai daban-daban, ciki har da shugabannin APC na ƙasa da jihohi, ‘yan majalisun dokoki, da shugabannin ƙananan hukumomi.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta ba da gudummuwar da ake bukata don tabbatar da nasarar shirin sabunta rajistar mambobin APC ta intanet a yankin Arewa maso Gabas.

“Ina tabbatar muku cewa Gwamnatin Jihar Borno ƙarƙashin jagorancina za ta bayar da cikakken goyon baya domin nasarar shirin rajistar mambobin APC ta yanar gizo a Arewa maso Gabas.
“Za mu kuma tallafa wa mambobin jam’iyyar APC a jihohin da wasu jam’iyyun ke mulki domin su ma su samu damar yin rajista.”

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya koka kan sabon salon ta'addancin 'yan Boko Haram a Borno

- Gwamna Babagana Zulum.

Me gwamnatin APC ta yi a Borno?

Zulum ya bayyana cewa mutanen Borno na da dalilai masu ƙarfi na kasancewa tare da APC, duba da irin rawar da jam’iyyar ta taka wajen dawo da zaman lafiya da farfaɗo da jihar daga barnar ta’addanci.

Gwamnan ya kara da cewa:

“Babu wani shakku ko tantama, gaba daya jihar Borno ta APC ce, biyayyarmu ga jam’iyya da shugabancinta cikakke ne babu surki.
“Kafin zuwan APC mulki, Borno ta durƙushe; ƙananan hukumomi sun koma hannun ‘yan ta’adda, tattalin arzikinmu ya rushe, jama’a kuma suna rayuwa cikin tsoro.
"Amma yau ga shi mun samu canji kuma wannan canji ya samu ne sakamakon ƙoƙari da goyon bayan gwamnati mai mulki ta APC.”
Shugaba Tinubu da Zulum.
Hoton Shugaba Bola Tinubu yana sa hannu a filin Eagle Square da na Gwamna Babagana Zulum Hoto: OfficialABAT, @profzulum
Source: Twitter

Gwamna Zulum ya yabi Buhari da Tinubu

Zulum ya jinjinawa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da kuma Shugaba Bola Tinubu bisa goyon bayan da su ka baiwa yankin Arewa maso Gabas wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba.

Kara karanta wannan

Injiniyoyi sun ga kokarin Gwamna Abba, sun ba shi lambar girmamawa

A ƙarshe, Zulum ya yi kira ga jama’an jihar Borno da su fara shiri domin sake zaɓen Shugaba Tinubu a zaben 2027, kamar yadda Punch ta rahoto.

Zulum ya koka kan salon Boko Haram

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Babagana Zulum ya koka kan yadda yan Boko Haram suka fara amfani da jirage marasa matuka wajen kai hare-hare.

Zulum ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gudanar da binciken gaggawa da sake duba tsarin tsaron sama da na kasa.

Gwamna Zulum ya nuna matukar damuwarsa kan sabon salo da ’yan ta’addan suka fara amfani da shi, yana mai cewa barazana ce babba ga taaron kasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262