'Dan Majalisa Ya Fadi Dalilin da zai Saka Arewa Ta Zubawa Tinubu Kuri'a a 2027

'Dan Majalisa Ya Fadi Dalilin da zai Saka Arewa Ta Zubawa Tinubu Kuri'a a 2027

  • 'Dan majalisar tarayya Aminu Sani Jaji ya ce Bola Tinubu zai samu nasarar ban-mamaki a yankin Arewa maso Yamma
  • Ya yaba da irin ayyukan da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa a yankin, wanda a ganinsa ya karawa shugaban kwarjini
  • Hon. Jaji ya bukaci shugabannin APC a Zamfara su haɗa kai don kauce wa rarrabuwar kawuna kafin babban zaben 2027

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara – majalisar wakilai mai wakiltar Kaura-Namoda/Birnin Magaji a jihar Zamfara, Honarabul Aminu Sani Jaji ya ce zai a sha mamaki a zaben 2027.

Ya bayyana tabbacin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai lashe zaben shugaban ƙasa na 2027 da babban rinjaye a jihohin Arewa maso Yamma.

Dan majalisar tarayya ya ce Tinubu zai yi nasara a 2027
Hoton Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Hon. Jaji ya faɗi haka ne ranar Lahadi a Gusau yayin da yake ganawa da manema labarai tare da bayyana ayyukan Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kogi ya yabi hangen nesan Tinubu da ya nada 'dan jiharsa hafsan sojan kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan Majalisa ya yabi gwamnatin Tinubu

Hon. Aminu Sani Jaji ya jaddada cewa nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu a yankin sun sa jama’a na ƙara amincewa da ita.

Ya ce:

“Babu wani shakka cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai sake lashe zabe a 2027 karkashin jam’iyyar APC."

Dan majalisar ya kara da cewa a jihar Zamfara babu dalilin da zai sa jama’a su goyi bayan wani ɗan takara daga wata jam’iyya daban.

A Kalamansa:

“A nan Zamfara, babu dalilin tallafa wa wani ɗan takara ban da Shugaba Tinubu,” Jaji ya nanata.

'Dan Majalisar ya nemi hadin kan APC

Jaji ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba mai hangen nesa da akida mai kyau, wanda ke aiwatar da alkawuran da ya ɗauka ga ‘yan Najeriya.

Dangane da siyasar Zamfara, Jaji ya ce jam’iyyar APC na ƙoƙarin farfaɗowa daga rikicin cikin gida da ya sa ta fadi a zaben 2019 da na 2023.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An kama dalibin jami'ar IBB kan saboda gwamna a Facebook

Hon. Jaji ya nemi hadin kan APC a Zamfara kafin 2027
Hoton Shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya ce:

“Rashin haɗin kai tsakanin shugabannin jam’iyyar ne ya janyo mummunar rashin nasara. Ya kamata mu fahimci juna, mu tafi a layi guda."

Ya bayyana Zamfara a matsayin ginshiƙin APC a Arewa maso Yamma, yana mai cewa jihar ta taka rawar gani wajen ganin Tinubu ya yi nasara a zaben 2023.

Hon. Jaji ya roƙi shugabannin jam’iyyar su manta da son rai da ƙiyayya, su haɗa kai don gina jam’iyyar a shirye-shiryen zaben 2027.

A Kalamansa:

“Dole ne mu yi aiki da murya ɗaya don ƙarfafa jam’iyyar APC kafin babban zabe."

Tinubu ya naɗa sabon Minista

A baya, kun ji cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta sanar da nadin Dr. Bernard Doro daga jihar Filato a matsayin sabon minista na tarayya tare da aika sunansa ga majalisa.

Sanarwar da Bayo Onanuga ya fitar ta ce wannan nadin na Doro ya zo ne bayan sauyi da aka yi a shugabancin jam’iyyar APC a watan Yuli karkashin jagorancin Tinubu.

Kara karanta wannan

Jagororin PDP sun rabu a kan bai wa turaki shugabancin jam'iyya

Majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun ce Tinubu ya tattauna da manyan jam’iyyarsa daren Litinin kafin yanke shawarar nadin Dr. Doro a majalisar tarayya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng