Sabon Tarihi: Dan Majalisar Tarayya Ya Janye Takara a 2027, Ya ba Matasa Dama

Sabon Tarihi: Dan Majalisar Tarayya Ya Janye Takara a 2027, Ya ba Matasa Dama

  • Dan majalisar tarayya a Najeriya ya kafa tarihi bayan ya sanar da cewa ba zai sake tsayawa takarar Majalisar Wakilai a 2027 ba
  • Dan majalisar daga jihar Sokoto ya ce ya yi hakan ne domin bai wa matasa dama inda ya ce Najeriya na bukatar sababbin jini
  • Hon. Abdussamad Dasuki ya ce wannan mataki sadaukarwa ce don ganin an samu sauyi a siyasar Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - A wani mataki da mutane da dama suka bayyana a matsayin abin koyi a siyasar Najeriya, dan majalisar wakilai ya sanar da cewa ba zai sake neman tazarce a 2027 ba.

Hon. Abdussamad Dasuki da ke waliltar mazabar Kebbe/Tambuwal a jihar Sokoto ya ce ya yi hakan ne saboda matasa.

Dan majalisa daga Sokoto ya sadaukar da takararsaga matasa
Hon. Abdussamad Dasuki daga jihar Sokoto a majalisa. Hoto: Abdussamad Dasuki.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da dan majalisar ya fitar a shafin Facebook a yau Lahadi 26 ga watan Oktobar 2025.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Majalisa ta amince da kirkirar karin jiha 1 a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin Hon. Dasuki na janye takara

Dasuki ya bayyana cewa wannan shawara tasa “sadaukarwa ce ta kashin kai” domin bai wa sababbin jini damar shiga majalisa.

Ya ce hakan zai ba su dama su kawo sababbin ra’ayoyi da samar da masu kuzari ga tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.

“Najeriya tana bukatar hadin kai da sadaukarwa, Bayan shawara da iyalina, shugabanni da abokai, na yanke shawarar ba zan tsaya takara ba a 2027. Wannan ba don gajiya ba ne, amma don gina makoma mafi inganci.
“Ni ma har yanzu matashi ne, amma na zarce shekaru 40 da muka sanya a matsayin iyaka. Idan muna son gaskata maganganunmu, sai mu nuna hakan da aiki. Wannan ne sadaukarwa ta.”

- Abdussamad Dasuki

Dan majalisar tarayya ya janye takara a 2027
Dan majalisar tarayya daga Sokoto, Hon. Abdussamad Dasuki. Hoto: Abdussamad Dasuki.
Source: UGC

Hon. ya sha ruwan yabo kan matakinsa

Matakin Dasuki ya jawo yabo daga bangarori daban-daban, inda mutane suka bayyana shi a matsayin sabon salo a siyasar kasar, kuma dan siyasa da ya san lokacin da ya dace ya ja gefe.

Kara karanta wannan

"Ba zan boye komai ba," Wike ya fadi abin da zai fadawa Jonathan kan batun takara a 2027

Dasuki ya fara siyasarsa tun shekaru 14 da suka wuce wanda ya fara da majalisar jiha, majalisar tarayya da majalisar zartarwa ta jiha.

Dan siyasar ya gode wa al’ummarsa, abokan aikinsa da kuma jagoransa, tsohon gwamnan Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, saboda irin goyon bayan da suka ba shi.

Ya kara da cewa:

“Ga al’ummata, na dauki amanarku da girma. Ga matasa kuma, lokaci ya yi da za ku dauki matsayin ku, ku tsaya da karfin hali, gaskiya da hangen nesa.
“A yayin da nake matsawa gefe, ina son in bar tarihi mai kyau a siyasar Najeriya, tarihi na shugabanni masu sanin lokacin da ya kamata su ba sababbi dama.”

Sokoto: Hon. Dasuki ya tallafa a Ramadan

A baya, kun ji cewa dan majalisar wakilai Abdussamad Dasuki ya bada tallafin Naira miliyan 100 domin azumin Ramadan ga mutanen mazabarsa a jihar Sokoto.

An kafa kwamitin mutum 35 da ke dauke da limamai da shugabanni domin rarraba kayan agaji ga al’ummar mazabar kafin Ramadan ya karaso.

Dasuki ya bukaci jama’a su ci gaba da kyautatawa, yana mai cewa Ramadan wata dama ce ta sada zumunta da taimakon mabukata a cikin al’umma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.