Kusa a APC Ya Fadi Yadda Gwamna Ya Gurgunta ’Yan Adawa da Ayyukan Alheri

Kusa a APC Ya Fadi Yadda Gwamna Ya Gurgunta ’Yan Adawa da Ayyukan Alheri

  • Jigon APC daga Jigawa ya ce Gwamna Umar Namadi ya gurgunta jam’iyyun adawa a kananan hukumomi 27 da ke jihar
  • Dan APC ya bayyana cewa shirin “Greater Jigawa Agenda” na Namadi ya jawo goyon baya da sauyin jam’iyya sama da mutane 66,000
  • Ya ce gwamnatin Namadi ta yi fice a fannoni da dama, ciki har da ilimi, kiwon lafiya, noma da karfafa tattalin arzikin talakawa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dutse, Jigawa - Jigon jam’iyyar APC daga jihar Jigawa, Abdullahi Mahmood Garun Gabas, ya yi magana kan tasirin ayyukan Gwamna Umar Namadi a jihar.

Abdullahi Mahmood ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Umar Namadi ta murkushe jam’iyyun adawa a fadin jihar saboda irin ayyukan alheri da take yi.

Jigon APC ya kwarara yabo ga Gwamna Namadi
Gwamna Umar Namadi da kusa a APC. Hoto: Garba Muhammad/Abdullahi Mahmood.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata hira da wakilin Legit Hausa ya samu inda dan siyasar ya fadi irin tasirin ayyukan alheri na Gwamna Namadi.

Kara karanta wannan

Bayan murabus daga PDP, ministan Buhari na kokarin 'hana' gwamna shiga APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kusa a APC ya yabawa nasarorin Gwamna Namadi

Abdullahi ya ce Gwamna Namadi ya samu cikakken goyon baya daga kowane yanki na Jigawa saboda manyan nasarorin da ya samu daga shirye-shiryensa 12.

A cewarsa, sauyin jam’iyya da mutane sama da 66,000 suka yi daga adawa zuwa APC ya tabbatar da karfin Gwamna Namadi a siyasa da shugabanci.

Ya ce yanzu jam’iyyun adawa a Jigawa sun rikice, kuma suna cikin rudani saboda rashin abin da za su soki gwamnatin da ta cika alkawura.

Jigawa: Ayyukan Namadi a kasa da shekaru 3

Abdullahi ya bayyana cewa cikin kasa da shekaru uku, Gwamna Namadi ya sauya tsarin mulki da siyasa ta hanyar tabbatar da ci gaba da hadin kai.

Ya ce:

“Nasarorin Gwamna Namadi sun shafi fannoni da dama, kamar ilimi, lafiya, gine-gine, noma da karfafa tattalin arzikin talakawa.”
Kusa a APC ya fadi yadda Gwamna Namadi ya rikita yan adawa
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa. Hoto: Garba Mohammed.
Source: Facebook

'Dalilin samun goyo baya da Namadi ke yi'

Abdullahi ya kara da cewa gwamnatin Namadi tana samun yabo daga cikin gida da waje saboda tasirin sauyi da ta kawo a Jigawa State.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bi sahun Peter Mbah ya koma jam'iyyar APC mai mulki? Gaskiya ta bayyana

Ya ce wannan ne yasa jama’a masu kishin cigaba suka daina nuna bambancin jam’iyya don goyon bayan nasarar gwamnatin Gwamna Umar Namadi.

Har ila yau, shirin gwamnatin da aka fara a bana ya kara karfafa amincewa tsakanin gwamnati da al’umma a jihar Jigawa.

Ya ce shirin yana tabbatar da gaskiya da bayyananniyar tafiya tsakanin jama’a da gwamnati, tare da gina sabuwar dangantaka mai karfi da fahimta.

Gwamna ya fadi matsayarsa kan tazarcen Tinubu

Kun ji cewa ana ci gaba da bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan tazarcen shugaban kaaa, Bola Ahmed Tinubu, a zaben 2027 duk da bai ce zai yi takara ba.

Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba kan salon mulkin da Shugaba Tinubu yake yi a Najeriya wanda ya kawo ci gaba a bangarori da dama.

Ya nuna cewa za su yi bakin kokari domin ganin cewa shugaban kasan ya sake komawa kan madafun iko a karo na biyu domin ci gaba da ayyukan alheri ga yan kasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.