Wike Ya Ragargaji Gwamnonin PDP, Ya Fadi Illar da Za Su Yi Wa Jam'iyyar

Wike Ya Ragargaji Gwamnonin PDP, Ya Fadi Illar da Za Su Yi Wa Jam'iyyar

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya taso gwamnonin jam'iyyar PDP mao adawa a gaba
  • Wike ya bayyana cewa yadda suke tafiyar da al'amuran babbar jam'iyyar hamayyar, zai iya kai ta ga rugujewa gabadaya
  • Ministan ya nuna cewa tuni dama ya hango rikicin da zai dabaibaye jam'iyyar saboda ba a yi abubuwan da suka dace ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki gwamnonin jam’iyyar PDP.

Wike ya bayyana cewa irin yadda suke tafiyar da rikicin cikin gida na jam’iyyar zai kai ta ga rugujewa.

Wike ya soki gwamnonin PDP
Gwamnonin PDP da Nyesom Wike Hoto: @seyimakinde, @GovWike
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Wike wanda sau biyu ya kasance gwamnan jihar Rivers a karkashin jam’iyyar PDP, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai a Abuja, ranar Jumma’a.

Kara karanta wannan

Jagororin PDP sun rabu a kan bai wa turaki shugabancin jam'iyya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar PDP na cikin rikici mai tsanani tsakanin gwamnoninta na yanzu da Wike, yayin da ake shirin gudanar da babban taron jam’iyyar da aka tsara a Ibadan, jihar Oyo, a watan gobe.

Me Wike ya ce kan gwamnonin PDP?

A yayin hirar, Wike ya yi magana kan rikicin da ya addabi jam'iyyar.

“Ban fada muku tun da wuri ba cewa tarkon da kuke kafawa zai kama ku? Ban fada muku ba cewa irin yadda wadannan gwamnoni ke tafiya, su ne za su binne jam’iyyar?
"Kuna nufin saboda ba ni da mukamin gwamna yanzu, sai ku gudanar da taron PDP, ku kira kan ku shugabanni, ku ware ni, kuma kuna tsammanin za ku tsira? Wannan ba zai yiwu ba."

- Nyesom Wike

Wike ya nesanta kansa da batun Turaki

Wike ya kuma nesanta kansa daga jiga-jigan jam’iyyar a Arewa da suka amince da Kabiru Tanimu Turaki a matsayin dan takararsu na kujerar shugaban PDP na kasa.

Kara karanta wannan

Dattawan PDP sun nuna yatsa ga Wike kan rikicin jam'iyyar

“Ban san wani Tanimu Turaki da zai zama shugaban PDP ba. Watakila shugaban wata kungiya ce daban, amma ba PDP da na sani ba."

- Nyesom Wike

Wike ya caccaki gwamnonin jam'iyyar PDP
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Source: Facebook

Wike ya yi hasashen rikicin PDP

Wike ya kara da cewa ya riga ya hango rikici da sauya shekar da ke addabar jam’iyyar tun kafin abubuwan su fara faruwa, za a samu rahoton a jaridar The Punch.

“Tun farko na fada cewa idan abin da ke gudana bai tsaya ba, PDP za ta ci gaba da yin asara. Ba a tafiyar da al’amura daidai, kuma wata rana za mu yi nadama, ga shi yanzu haka abin yake.”
“Abin kunya ne sosai. Daya daga cikin gwamnoni ma shi ne shugaban kwamitin babban taron kasa. Amma duk suna wasa da hankalin jama’a. Na fada tun farko, babu abin da na fada da bai tabbata ba.”

-Nyesom Wike

Dattawan PDP sun ragargaji Wike

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar dattawan PDP a Arewa ta yi kalaman suka kan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Kungiyar ta zargi ministan ta yunkurin ruguza jam'iyyar PDP da sauran jam'iyyun adawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan gwamnoni 2 sun fita, gwamnan PDP ya kawo karshen jita jitar zai koma APC

Sai dai, ta bayyana cewa Wike da 'yan kanzaginsa a PDP ba za su samu nasara kan wannan shirin na su ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng