"Ba Zan Boye Komai ba," Wike Ya Fadi Abin da Zai Fadawa Jonathan kan Batun Takara a 2027
- Ministan Abuja ya ce a shirye yake ya fadawa Goodluck Jonathan ra'ayinsa idan ya nemi shawara kan batun sake neman takara a 2027
- Nyesom Wike dai na daya daga cikin wadanda ba su goyin bayan tsohon shugaban kasar ya sake dawowa ya nemi mulkin Najeriya
- Tsohon gwamnan ya gargadi Jonathan da cewa masu son dawo da shi, su ne dai wadanda suka yaudare shi a lokacin zaben 2015
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Najeriya – Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike, ya ce zai faɗa wa tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan ra’ayinsa kai tsaye idan ya nemi shawararsa kan takara a 2027.
Wike ya bayyana cewa ba zai ji tsoron komai ba, zai fada wa Jonathan duk abin da ke ransa matukar ya tuntube shi game da fitowa takarar shugaban kasa a zabe na gaba.

Source: Twitter
Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya bayyana haka ne a yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja ranar Juma’a, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shin Jonathan ya tuntubi Wike?
Ministan ya karyata jita-jitar da ke cewa Jonathan ya tattauna da shi kan takarar da ake so ya fito don sake neman mulkin Najeriya a 2027.
A cewar Wike:
“Jonathan bai gaya min zai nemi takara ba, bai kira ni ko sau ɗaya ba ya ce ana matsa masa lamba ya tsaya takara. Amma idan ya kira ni ya tambaye ni, zan faɗa masa ra’ayina da abin da nake ji a raina.”
Da yiwuwar Jonathan ya fito takara a 2027
Rahotanni sun nuna cewa ko da yake Jonathan bai bayyana aniyarsa ba, akwai alamar cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP na ƙoƙarin ganin ya dawo takara a 2027.
A watan da ya gabata, tsohon ministan yada labarai, Farfesa Jerry Gana, ya bayyana cewa Jonathan zai tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, in ji rahoton Leadership.
Gargadin da Wike ya yi wa Jonathan
Sai dai Wike, wanda tsohon yaron siyasar Jonathan ne, ya gargade shi da cewa kada ya bari ’yan siyasa su yi amfani da shi kamar yadda aka yi a zaben 2015.
A wani taron manema labarai da ya gabatar a Abuja, Wike ya ce:
“Na san Jonathan sosai, yana da mutunci a idon duniya, kuma ya kamata ya kiyaye hakan. Waɗannan mutanen da ke ƙoƙarin jawo shi su ne waɗanda suka ruɗe shi a 2015.
“Waɗanda ke kira da ya tsaya takara yanzu, su ne waɗanda suka ci amanarsa a baya. Idan har ya bari su sake amfani da shi, to za su jefa jam’iyya cikin rudani.”

Source: Facebook
Tinubu ya hana Wike magana da yawunsa?
A wani rahoton, kun ji cewa Nyesom Wike ya musanta rade-radin da ake yadawa cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya hana shi magana kan gwamnatinsa.
Wike ya ce shi ba mai magana ne da yawun Shugaba Bola Tinubu ba, sai dai yana bayyana ayyukansa a babban birnin Abuja a matsayinsa na minista.
Tsohon gwamnan ya ce aikinsa shi ne sanar da duniya abin da ke faruwa a karkashin gwamnatin Tinubu da kuma irin ci gaban da ake samu a birnin tarayya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


