Akwai Yiwuwar Mata Su Karu a Majalisa, Gwamnoni Sun Goyi bayan Kudiri na Musamman

Akwai Yiwuwar Mata Su Karu a Majalisa, Gwamnoni Sun Goyi bayan Kudiri na Musamman

  • Gwamnonin Najeriya sun bada cikakken goyon baya ga kudirin dokar da ke neman samar da kujeru na musamman ga mata a majalisun dokoki
  • Sun umarci 'ya'yansu da su fara neman kamun kafar ’yan majalisa na tarayya da na jihohi domin tabbatar da amincewa da kudirin a gaggauce
  • Haka kuma, sun yaba da manufofin kudi na gwamnatin tarayya da ke da nufin daidaita tattalin arzikin kasar da karfafa tsaro a fadin Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayyana cikakken goyon bayanta ga kudirin dokar da ke neman samar da kujeru na musamman ga mata a majalisu.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar bayan taron su da aka kammala da safiyar Juma’a, a daidai lokacin da ake kokarin bai wa mata dama a shugabanci.

Kara karanta wannan

An gano daloli, motoci da alfarma da Tinubu ya ware wa korarrun hafsoshin tsaro

Gwamnoni na son a kara yawan mata a majalisun Najeriya
Hoton wasu daga cikin gwamnonin Najeriya a yayin wani taro Hoto: @RealAARahman
Source: Twitter

Channels TV ta wallafa cewa a cewar sanarwar, gwamnonin sun umarci ’ya’yansu da ke majalisun jihohi da su fara kama karfar ‘yan majalisa na kasa don tabbatar da kudirin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnoni na goyon karo mata a majalisu

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa kudirin, wanda na neman a gyara kundin tsarin mulki na 1999 domin samar da guraben na musamman da mata kadai za su tsaya takara a kai.

Ana son samar da wadannan gurabe ne a matakin majalisar tarayya da jihohi 36 da ake da su a Najeriya domin bai wa mata dama a dama da su.

Gwamnoni sun nemi a fara kamun kafa don kara yawan mata a majalisu
Hoton Shugaban Kasa Tinubu a gaban 'yan majalisar tarayyar Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Manufar kudirin ita ce ta kara wa mata damar shiga harkokin mulki, musamman a matakin zartarwa da majalisa, domin rage gibin da ke tsakaninsu da maza.

Baya ga batun kudirin mata, kungiyar ta yaba da manufofin tattalin arziki na gwamnatin tarayya, musamman wadanda Babban Bankin Najeriya (CBN) ke aiwatarwa.

Gwamnoni sun yabi gwamnatin tarayya

Kara karanta wannan

Sauya kundin mulki: Majalisa ta fara bitar bukatun kirkirar jihohi 55 a Najeriya

Gwamnonin Najeriya sun ce manufofin gwamnatin tarayyya na haifar da da mai ido domin daidaita tattalin arzikin kasar.

Sun kuma yi alkawarin ci gaba da bada hadin kai da hukumomin tarayya wajen tabbatar da dorewar ci gaban tattalin arzikin kasa.

A bangaren tsaro, kungiyar gwamnoni ta jaddada kudirinta na karfafa hadin gwiwa da Hukumar Tsaro ta DS* domin tunkarar barazanar 'yan ta'adda da sauran matsalolin tsaro.

Gwamnonin sun bayyana cewa hadin kai da musayar bayanai za su taimaka wajen rage tashe-tashen hankula da inganta tsaron rayuka da dukiyoyin wadanda ake wakilta.

Ana maraba da yunkurin gwamnoni

Barista Halima Abubakar, lauya ce kuma guda cikin cikin yan kungiyar 'Women Support Group ' a Kano, ta shaidawa Legit cewa:

"Mun dade muna so a baiwa mata gurbin shugabanci saboda muna da yawa sosai. Ya kamata a ce akwai mata domin su rika wakiltar yancinmu da ra'ayinmu."

Majalisa ta magantu kan gyara dokar zabe

A baya, mun wallafa cewa shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ana aikin gyaran dokar zabe ta 2022.

Kara karanta wannan

Majalisar dinkin duniya ta ce Najeriya ta zama abin koyi a kula da 'yan gudun hijira

Ya kara da bayar da tabbacin cewa za a kammala gyara dokar kafin karshen watan Disamba na shekarar 2025 domin a samu damar amfani da ita a babban zaben 2027 mai zuwa.

Bamidele ya bayyana hakan ne a zaman majalisar ranar Talata, bayan shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta wasikar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng