Jagororin PDP Sun Rabu a kan Baiwa Turaki Shugabancin Jam'iyya

Jagororin PDP Sun Rabu a kan Baiwa Turaki Shugabancin Jam'iyya

  • Shugabannin jam’iyyar PDP na yankin Arewa maso Yamma sun nesanta kansu daga amincewa da bai wa Tanimu Turaki shugabanci
  • Umar Bature, sakataren shirya harkokin jam’iyyar PDP na kasa, ya bayyana cewa gwamnonin yankin sun yi gaban kansu ne kawai
  • Reshen Yankin Arewa maso Yamma ya ce ba a tuntube shi ba kafin sanar da sunan Turaki, kuma za a fitar da takarda a kan lamarin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugabannin PDP daga yankin Arewa maso Yamma sun nesanta kansu daga amincewar wasu gwamnonin jam'iyya su ka yi da sabon shugaba.

Gwamnonin dai sun amince da a nada tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), a matsayin dan shugabancin jam’iyyar PDP na kasa.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar da El Rufai ya koma ta rikice, an kori shugaban SDP da wasu jiga jigai 2

Jagororin PDP a Arewa maso Yamma sun yi watsi da Tanimu
Kabiru Tanimu Turaki, wanda gwamnonin PDP ke son ya shugabanci jam'iyya Hoto: Kabiru Tanimu Turaki
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja da yammacin Alhamis, wasu 'yan PDP sun yi watsi da batun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP ta dare kan shugabancin jam'iyya

Rahoton ya ce Umar Bature, sakataren shirya harkokin jam’iyyar na kasa, ya bayyana cewa amincewar da aka yi da Turaki bata da tushe kuma bata wakiltar matsayar yankin ba.

A ranar Laraba, gwamnan jihar Adamawa kuma shugaban kwamitin shirya babban taron jam’iyyar, Ahmadu Fintiri, ya sanar da cewa an amince da Turaki ya jagoranci PDP.

Manyan PDP a Arewa maso Yamma za su fitar da dan takararsu
Jigo a PDP daga Arewa maso Yamma, Tanimu Turaki Hoto: Kabiru Tanimu Turaki
Source: Facebook

Amma Umar Bature ya ce:

“Arewa maso Yamma ba ta taba zama tare da yin shawara kan hakan ba, don haka wannan sanarwa bata da inganci.”

A zaman majalisar koli ta jam’iyyar PDP da aka gudanar a ranar 25 ga Agusta a Abuja, jam’iyyar ta amince da cewa zaben shugaban kasa na 2027 zai tafi Kudu.

Sannan kujerar shugaban jam’iyya ta kasa aka kebe wa Arewa. Daga bisani, shugabannin shiyyar suka kebe wannan matsayi ga Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Atiku da wasu manya na fafutukar fito da shi, shugaban IPOB ya rikita lissafin lauyoyi a kotu

An samu baraka a jam'iyyar PDP

Sai dai Bature ya nuna cewa shugabannin yankin ba su yi taro ba kafin a sanar da Turaki a matsayin wanda ake so ya jagoranci PDP ba.

Ya ce:

“Mun ji cewa sun amince da wani suna Turaki, amma mu ba mu halarci wani taro a kan haka ba. Wannan abu ya nuna rashin tuntuba kuma bai dace da tsarin jam’iyya ba.”

Ya kara da cewa:

“Arewa maso Yamma ce aka baiwa wannan dama, amma wasu yankuna ne suka fito da dan takara ba tare da tuntubar mu ba. Wannan abu ba zai yiwu ba.”

Daga cikin wadanda suka halarci taron da Bature ya jagoranta akwai tsohon sakataren jam’iyyar na kasa Ibrahim Tsauri da dan tsohon gwamnan Jigawa, Mustapha Lamido.

Sai kuma dan takarar gwamna na PDP a Kaduna a 2023 Isah Ashiru Kudan, inda su ka tabbatar da cewa za a fitar da dan takarar shugabancin PDP nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Dakarun tsaron Najeriya sun harzuka, sun hallaka jagoran 'yan ta'adda a Filato

Gwamnonin PDP sun fitar da shugaban jam'iyya

A baya, kun ji cewa manyan jam'iyya sun yanke shawarar tsaida Kabiru Tanimu Turaki, a matsayin dan takarar su a mukamin shugaban jam’iyyar na ƙasa a taro mai zuwa.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed; gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal.

Duk da haka, an jaddada cewa ba a rufe ƙofar takara ga wasu da ke da sha'awar kujerar ba, wato duk wanda ya ke da sha’awar wannan mukami zai iya tsayawa takara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng