‘Akwai Aiki a Zaben 2027’: Kwankwaso Ya Fadi Yiwuwar Aiki da Tinubu, Jonathan
- 'Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Mjsa Kwankwaso ya yi magana kan zaben 2027 da ake tunkara a Najeriya
- Kwankwaso ya ce NNPP a shirye take ta yi haɗin gwiwa da jam’iyyun siyasa ko manyan ‘yan takara, ciki har da APC, kafin zaɓen 2027
- Ya bayyana cewa duk wani haɗin kai dole ne ya kasance bisa cin moriyar talakawa da tabbatar da shugabanci nagari
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - 'Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya magantu kan zaben 2027.
Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa jam’iyyarsa ta buɗe ƙofa ga yin haɗin gwiwa da manyan ‘yan siyasa kafin zaɓe mai zuwa.

Source: Twitter
Kwankwaso ya fadi sharadin hadewa da jam'iyyu
Da yake zantawa da BBC Hausa, tsohon gwamnan Kano ya ce jam’iyyarsa tana neman haɗin kai da mutum mai gaskiya da amana, wanda ke son inganta rayuwar talakawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwankwaso, wanda kwanan nan ya cika shekara 69, ya ce NNPP za ta iya haɗuwa da kowace jam’iyya, har da APC, idan hakan zai kawo alheri ga jama’a.
A baya, Rabiu Kwankwaso ya ce shiga APC zai yiwu ne kawai idan jam’iyyarsa za ta amfana da moriyar siyasa mai gamsarwa.
Ya ce:
“Muna jiran kowa daga cikinsu, ko APC, PDP, ADC, Jonathan, ko Peter Obi, muddin muka ga ka dace ba matsala ba ne. Duk wanda ya gaza cika alkawari ga jama’a, ba za mu cigaba da haɗin kai da shi ba.
"Abin da muke so shi ne ko APC ne, mu muna da abin da muke son yi wa Najeriya, idan ana so mu yi sai an zo an dauko abin da suke cikin namu jam'iyyar.
"Mu damuwarmu dai sai talaka ya ji dadi, matasanmu su yi ilimi, matsalar tsaron nan da ake fama da shi ya kawo karshe a yankunanmu."

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya tura sako ga masu barin Kwankwasiyya, ya ce za su gane kurensu a 2027

Source: Facebook
Abin da Kwankwaso ke so daga 'yan siyasa
Kwankwaso ya jaddada cewa abin da suke nema shi ne alheri ga talakawa, tsaro mai inganci, da ilimin matasa, yana mai sukar wasu shugabanni da ke amfani da mulki don ƙara wa kansu dukiya.
Ya yi gargadin cewa zaɓen 2027 zai kasance mafi tsauri a tarihin Najeriya, domin mutane sun waye, sun fahimci ‘yancinsu kuma ba za su sake sayar da ƙuri’unsu ba.
Ya ce:
“A wannan karon, babu wanda zai zo ranar zaɓe ya raba kuɗi don a zabe shi. watakila abin da talakawa za su yi ba a taɓa gani ba a tarihin zaɓen Najeriya.”
Kwankwaso ya kafa tubalin gina Jami'ar Likitanci
Kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi murnar bikin zagayowar ranar haihuwarsa da abubuwan alheri.
Kwankwaso ya kafa tubalin gina jami’ar likitanci a Kwankwaso da ke Madobi, domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Jagoran na Kwankwasiyya ya ce makarantar ta fara aiki 2019, ta yaye dalibai 400, kuma yanzu 400 na ci gaba da karatu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
