Kwankwaso Ya Tabo Batun Rikicin NNPP, Ya Fadi Abin da Ya Haddasa Matsalar
- Madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi tsokaci kan rikicin da ake cewa akwai a cikin jam'iyyar NNPP
- Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana cewa jam'iyyar ba ta rigima da kowa domin hukumar INEC ta san da zamanta
- Ya yi nuni da cewa masu ikirarin suna rigima da su, sun sha kai su kotu da dama amma ko a guda daya ba su taba samun nasara ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Jagoran NNPP na kasa kuma madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan batun rigimar da ake yi a jam'iyyar.
Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa babu wani rikici ko rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar, duk da kokarin wasu da ke neman tayar da hankula a cikinta.

Source: Facebook
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da tashar BBC Hausa kwanan nan.
Me Kwankwaso ya ce kan rikicin NNPP?
Madugun na Kwankwasiyya ya bayyana cewa ko kadan babu wata rigima a jam'iyyar NNPP.
Kwankwaso ya bayyana cewa mutanen da ke kokarin kawo rabuwar kai a jam'iyyar, sun kai su kotuna da dama amma ba su yi nasara ba.
“Babu wata rigima a cikin jam’iyyar NNPP. Ai kotu sun kai mu ta fi 1,000, amma babu ko guda daya inda suka yi nasara. Ba mu da rikici da kowa. Su fa har yanzu mai kayan dadi suke yi."
"Kamar mutumin APC ne ya zo yana rigima shi ACN ya yi, ko yana yin rigima a CPC, to ta ya ya hakan zai kasance."
"Kuna da kungiya eh kuna nan, amma dai ba kazo ka ce kana nan ba, ku bude shafin INEC mana ku gani, duk zabubbukan nan da su wa ake yi? Ai duk abubuwan da ake yi mu ba mu da rigima da su."
- Rabiu Musa Kwankwaso
Ya bayyana cewa wadanda suka kafa jam’iyyar tun farko ba ’yan siyasa ba ne.
“Abin da ba su fahimta ba shi ne, wadanda suka fara rajistar jam’iyyar ba ’yan siyasa ba ne. Ka san idan ka dauko wani abu za ka zubar, sai wani ya ce don Allah sharar nan ina so, sai ka rika tunanin ko akwai wani dan zinare ko wani abu."
"To kamar mu wannan rawar da muka gani, da babu komai a cikinta, amma yanzu mun inganta ta, muna da gwamna, ’yan majalisa, da sanatoci. Kuma suna ganin darajarmu a kasa a NNPP din."
- Rabiu Musa Kwankwaso

Source: Facebook
Abin Kwankwaso ya ce kan hadaka
Kwankwaso ya kara da cewa kofar jam’iyyar NNPP a bude take wajen yin hadakai da shugabanni daga kowace jam’iyya, ko APC, PDP, ko ADC, muddin akwai gaskiya, kwarewa, da kudurin tabbatar da adalci a cikin al’umma.
“Muna a shirye mu hada kai da kowa muddin akwai gaskiya da adalci. Abin da muke so shi ne nagartattun shugabanni da ke son ci gaban kasa, ba siyasa ta son kai ba."

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya tura sako ga masu barin Kwankwasiyya, ya ce za su gane kurensu a 2027
- Rabiu Musa Kwankwaso
Kwankwaso ya gargadi masu barin NNPP
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ja kunnen masu barin jam'iyyar NNPP ko tafiyar Kwankwasiyya.
Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa masu yi wa Kwankwasiyya tawaye za su gane kurensu a zaben shekarar 2027.
Hakazalika, tsohon gwamnan ya jaddada cewa siyasarsa ba za ta samu wani nakasu ba duk da ficewa da wasu ke yi daga tsarin Kwankwasiyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

