‘Cin Amana ne’: Sanatan APC a Katsina Ya Fadi Abin da Ya Kamaci Masu Sauya Sheka
- Sanata Mohammed Muntari Dandutse mai wakiltar Katsina ta Kudu ya ce bai kamata ana sauya sheƙa daga jam’iyya zuwa wata ba
- 'Dan majalisar dattawan ya bayyana hakan da cin amanar dimokuraɗiyya da kuma amincewar jama’a da suka zaɓi shugabanni
- Dandutse ya ce sabuwar dokar zaɓe ta 2025 za ta tabbatar da ingantacciyar dimokuraɗiyya, ta kuma tabbatar da zaɓe mai inganci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Wani sanata a Najeriya ya caccaki masu sauya sheka daga jam'iyyar da aka zabe su zuwa wata bayan lashe zabe.
Sanata Mohammed Muntari Dandutse daga Katsina ta Kudu ya ce sauya sheƙa daga jam’iyya zuwa wata ba tare da hukunci ba na lalata dimokuraɗiyya da amincewar jama’a.

Source: Facebook
TheCable ta ce Dandutse ya bayyana haka ne a majalisar dattawa yayin tattaunawa kan kudirin dokar zabe ta 2025 da za ta maye gurbin wacce aka yi a 2022.
Sauya sheka: Sanata ya fadi shirin majalisa
Sanatan ya ce sabuwar dokar zaɓe za ta taimaka wajen kafa tsarin zabe mai inganci da gaskiya, tare da kare amanar jama’a da ake zaɓe da ita.
Ya yi gargadin cewa dole majalisa ta sanya tanadi mai ƙarfi da zai hana sauya jam’iyya ba tare da hukunci ba domin kare tsarin dimokuraɗiyya.
A cewarsa:
"Ba zai yiwu a zabe ka a wata jam’iyya sannan ka sauya sheƙa ba tare da wani mataki ba, Ana cin amanar amincewar jama'a da zaɓinsu."
Haka kuma, Dandutse ya bukaci a gudanar da dukkan zaɓe a rana ɗaya, na shugaban ƙasa, gwamnoni da ‘yan majalisa, don rage kashe kuɗin gwamnati da tabbatar da gaskiya.

Source: Facebook
Bukatar Sanata Dandutse ga hukumar zabe
Dandutse ya kuma nemi hukumar INEC ta karɓi ikon gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi domin dawo da amincewa a matakin ƙasa.
Sanatan ya kuma ce ya kamata a rage yawan jam’iyyun siyasa zuwa ƙasa da 10, saboda da dama daga cikinsu “a takarda ne kawai” kuma suna kawo rikice-rikice a zabe.

Kara karanta wannan
"Ba zan yi sulhu da yan bindiga ba," Gwamna ya shirya daukar jami'an tsaro 10,000
Daga ƙarshe, ya bukaci ‘yan majalisa su nazarci dokar sassa-sassa domin ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya da dawo da martabar Najeriya a idon duniya, cewar Daily Trust.
Ya kara da cewa:
“A matsayinmu na shugabanni, idan muna son dawo da amincewar ’yan Najeriya da mutuncin dimokuraɗiyyarmu a idon duniya, dole mu duba waɗannan batutuwa sashi bayan sashi.”
Sanata ya magantu kan yiwa Natasha afuwa
A baya, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Kudancin jihar Katsina, Dandutse Mohammed Muntari, ya nuna rashin jin daɗinsa kan shawarar yi wa Natasha Akpoti-Uduaghan afuwa.
An dakatar da Sanata Natasha daga majalisa a baya bisa zargin rashin da’a a zauren majalisa, bayan amincewar sanatoci ta hanyar kada kuri’ar murya.
A wancan lokaci, an bayyana cewa za a iya yi wa Sanatar afuwa ta hanyar rage wa ko janye dakatarwar da aka yi mata matukar ta cika sharuda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
