Kwankwaso Ya Yi Magana a kan Zargin Tafiyar da Gwamnatin Abba a Kano

Kwankwaso Ya Yi Magana a kan Zargin Tafiyar da Gwamnatin Abba a Kano

  • Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce babu wata matsala tsakaninsa da Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Ya bayyana cewa tun kafin zaben 2019 suka yanke shawarar bai wa Abba dama ya jagoranci Kano saboda ganin ya cancanta
  • Kwankwaso ya ce Allah Ya baiwa Abba gwamnan Kano, kuma su suka ba shi dama ya tafi neman kujerar domin yi wa jama'a aiki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano –Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya nanata cewa babu wata matsala ko sabani tsakaninsa da Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ya ce tun kafin shekarar 2019 suka duba suka ga dacewar bai wa Abba dama ya kawo ci gaban jihar Kano.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce tsakaninsa da Abba lafiya lau
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Twitter

A wata hira da Hikima Rediyo, wacce Naseer Babbo ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya bayyana cewa tsakaninsa da gwamnatin Abba, shawara ce kawai idan gwamna ya nema.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya tura sako ga masu barin Kwankwasiyya, ya ce za su gane kurensu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya fadi alakarsa da Abba

Kwankwaso ya ce sun ba wa Gwamna Abba cikakkiyar dama ya gudanar da aikinsa yadda ya ga ya dace, amma wasu ‘yan siyasa ne ke ƙoƙarin haddasa rikici a tsakanin magoya baya.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya soki masu yada karya tsakaninsa da Abba
Hoton tsohon Sanata, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Ya kara da cewa:

“Abin da na sani shi ne, mun duba tun kafin zaɓen 2019 muka ga wanda ya fi cancanta, muka ba shi dama. Yanzu kuma yana yin abin da ya dace. Wasu mutane kawai ne ke yada jita-jita cewa ni nake tafiyar da gwamnati ko nake da kwangiloli. Babu gaskiya a cikin hakan.”

Kwankwaso ya yi nuni da cewa a tsarin su na siyasa, idan gwamnati ko gwamna ya tambayi shawara, sai kawai a ba shi.

Ya tabbatar da cewa amma babu wani wanda ke tsoma baki cikin ayyukan yau da kullum na gwamnatin jihar.

Alaƙar Kwankwaso da ‘yan majalisa

Sanata Kwankwaso ya kuma bayyana cewa tsakaninsa da sauran ‘yan majalisar jam’iyyarsu, babu tursasawa, amma an aika su ne su wakilce su wajen inganta rayuwar jama'a.

Kara karanta wannan

"Ba zan yi sulhu da yan bindiga ba," Gwamna ya shirya daukar jami'an tsaro 10,000

Ya ce tsarin su ya dogara ne kan bayar da shawara da kuma girmama ‘yancin kowa a tafiyar da tsarin mulki wajen cicciba rayuwar mutane.

Ya kara da cewa:

“Ba za su zo su tambaye ni ba, ba za su tambayi Gwamna wanda kananan hukumomi ke hannunsa ba. Mun kyale kowa yana aikinsa. Mun bawa kowa igiya, sai dai ya yi amfani da ita ya gyara kansa, ko kuma ya jefa kansa cikin matsala.”

Kwankwaso ya jaddada cewa manufarsu ita ce tabbatar da ci gaban Kano da zaman lafiya a tsakanin magoya baya, tare da ci gaba da mutunta juna tsakanin shugabanni da mabiyansu.

Baffa Bichi ya ja zare da Kwankwaso

A baya, kun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin Kano, Abdullahi Baffa Bichi, ya sake tada hayaniya kan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da mabiyansa na kungiyar Kwankwasiyya.

Ya bayyana cewa wani babban mutum wanda yanzu ya rasu ya tambaye shi dalilin da ya sa ya hulda da Kwankwaso, inda ya ce “tsautsayi ne” da kuma kaddara ta jawo haka.

Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya kara da cewa wannan babban mutum ya aika masa tawaga har gida, inda ya lallashe shi a kan kada ya tona wa Kwankwaso asiri da wani bidiyo.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng