Kwankwaso Ya Fadi Abin da Yasa Ya Gagari Mayu da Masu Kambun Baka

Kwankwaso Ya Fadi Abin da Yasa Ya Gagari Mayu da Masu Kambun Baka

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya halarci liyafar musamman da kungiyar kananan hukumomi na jihar Kano (ALGON) suka shirya
  • 'Dan siyasar ya yaba wa shugabannin kananan hukumomi bisa kyakkyawan shugabanci da hadin kai da gwamnatin jihar Kano
  • Ya bukaci 'yan Kwankwasiyya su kasance masu hakuri da juriya tare da fadin dalilin da yasa ya gagari mayu a gida da waje

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya fadi dalilin da yasa ya gagari mayu da masu kambun baka.

Ya bayyana jin dadinsa da liyafar musamman da kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta kasa (ALGON), reshen Kano, ta shirya domin girmamarsa.

Rabiu Musa Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso tare da Abba Kabir Yusuf. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanin da Kwankwaso ya yi ne a wani bidiyo da hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 19 sun hada baki sun yi magana kan mutuwar sama da mutane 40 a jihar Neja

A wurin taron, Kwankwaso ya yaba wa shugabannin kananan hukumomin jihar bisa kyakkyawan jagoranci da kuma yadda suke hada kai da gwamnatin jihar.

Ya kuma yi kira gare su da su yi shugabanci cikin tausayi da hangen nesa, suna koyi da Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya fara da karamin mukami har ya zama gwamnan jihar.

Kwankwaso ya yaba wa ALGON a Kano

A yayin jawabin nasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce shugabannin kananan hukumomi a jihar Kano sun taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauyi a rayuwar jama’a.

Ya ce hadin kan su da gwamnatin jihar ya taimaka wajen tabbatar da gaskiya, adalci da rikon amana a cikin tsarin mulki.

Kwankwaso ya kuma jaddada cewa nasarorin da ake gani a Kano ba za su samu ba da ba da irin wannan hadin kai da kulawa daga matakin kananan hukumomi.

Rabiu Kwankwaso ya ce ya gagari mayu

A cikin jawabinsa, Kwankwaso ya bukaci 'yan Kwankwasiyya da su kasance masu hakuri da juriya a harkar siyasa, yana mai cewa

Kara karanta wannan

"Kun yi kadan," Gwamna Abba ya aika sako ga masu son hada shi fada da Kwankwaso

“Ba a san waye zai zamo gwamna a cikinku a gaba ba.”

Ya ce a baya babu wanda ya yi tsammanin Abba Kabir Yusuf zai zamo gwamna, amma yau shi ne jagoran kowa a Kano ciki har da shi kansa.

A cewarsa:

“Abin da ya sa muka gagari mayu, ko na gida ko na waje, da masu kambun baka, shi ne alheri da soyayya ga jama’a.”
"Muna barci, (masoya) suna mana addu'a a Ka'aba, muna barci suna mana addu'a a masallatan Juma'a. Muna barci suna mana addu'a a dakunansu suna godiya ga Allah."

Kira ga shugabannin kananan hukumomi

Kwankwaso ya bukaci shugabannin kananan hukumomin da su ci gaba da yin shugabanci cikin tausayi da hangen nesa, suna koyi da Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Rabiu Musa Kwankwaso
Kwankwaso, Abba yayin taron da shugabannin kananan hukumomi a Kano. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a Facebook, Kwankwaso ya nuna godiya ga dukkan wadanda suka taya shi murnar cikar sa shekaru 69 a duniya.

Abba ya yi magana kan alaka da Kwanwaso

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce zai cigaba da zama da aiki tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Kano: Kwankwaso ya kafa tubalin gina jami'ar likitanci a gida, ya godewa Abba

Ya bukaci 'yan Kwankwasiyya da su kwantar da hankalinsu domin babu mai raba shi da tafiyar da suka fara da Kwankwaso.

Gwamnan ya jaddada cewa munafukai daga ciki da wajen Kano za su ji kunya kan yunkurin raba shi da ake da jogoran Kwankwasiyya a siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng