Gwamna Ya Gana da Shugaba Tinubu bayan Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC
- Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu a fadar shugaban kasa da ke Abuja yau Laraba
- Gwamna Mbah ya bayyana cewa tattaunawarsa da Tinubu ta maida hankali ne kan inganta alaka tsakanin jihar Enugu da gwamnatin tarayya
- Wannan dai na zuwa ne mako daya bayan gwamnan Enugu da mukarrabansa sun fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Najeriya – Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya gana da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja ranar Laraba.

Kara karanta wannan
Gwamnoni 19 sun hada baki sun yi magana kan mutuwar sama da mutane 40 a jihar Neja
Wannan ganawa na zuwa ne ’yan kwanaki kalilan bayan da Gwamna Mbah ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Source: Facebook
Gwamna Peter Mbah ya tabbatar da ganawarsa da Tinubu a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a da).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Mbah ya ziyarci Tinubu
Gwamna Mbah ya bayyana cewa shi da Shugaba Tinubu sun tattauna kan ƙarfafa haɗin kai da aiki tare tsakanin jihar Enugu da gwamnatin tarayya.
Ya rubuta cewa:
“A yau, na samu damar ganawa da mai girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu (GCFR), a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.
"Mun tattauna hanyoyin da za mu ƙara ƙarfafa haɗin kai tsakanin jihar Enugu da gwamnatin tarayya domin kawo ƙarin ci gaba da walwala ga mutanenmu.”
“Jihar Enugu za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙasa mai ƙarfi, hadin kai, kuma mai yalwar tattalin arziki.”
Yaushe gwamnan Enugu ya koma APC?
A baya, jaridar Punch ta ruwaito cewa Mbah ya sanar da sauya sheƙarsa zuwa APC a wani taron manema labarai da ya gudana a birnin Enugu makon da ya gabata.
Yayin da yake jawabi, Mbah ya ce shawarar sauya sheƙa ta samo asali ne daga kudurinsa na inganta jihar Enugu da kuma daidaita shirinsa da manufofin gwamnatin tarayya.
Ya bayyana wannan mataki a matsayin “dabarar haɗin gwiwa mai hangen nesa wadda za ta kawo sauyi mai ma’ana” ga jihar Enugu da ƙasar baki ɗaya.

Source: Twitter
Mbah wanda ke tare da tsohon gwamna, Ifeanyi Ugwuanyi, da wasu ’yan majalisar dokoki na jiha da na tarayya, ya ce da zuciya daya suka yanke shawarar shiga APC.
Mako daya bayan haka kuma Gwamna Abba ya taso daga Enugu ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Mbah ya saki baki kan batun Nnamdi Kanu
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna P. Mbah ya ce ya kamata a warware lamarin da ya shafi jagoran IPOB, Nnamdi Kanu, ta hanyar siyasa maimakon dogaro da kotu kawai.
Mbah ya bukaci shugabannin Kudu maso Gabas su haɗa kai wajen neman mafitar siyasa ga matsalar shugaban kungiyar IPOB.
Ya kara da cewa mafita ta siyasa ce hanya mafi dorewa domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Kudu maso Gabas.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

