Dattawan PDP Sun Nuna Yatsa ga Wike kan Rikicin Jam'iyyar

Dattawan PDP Sun Nuna Yatsa ga Wike kan Rikicin Jam'iyyar

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya na ci gaba da fuskantar rikice-rikicen gida wadanda ke kokarin kawo cikas ga babban taron ta na kasa
  • Kungiyar dattawan PDP na Arewa sun zargi ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, da yunkurin ruguza jam'iyyar
  • Ta bayyana cewa yunkurin da Wike da 'yan kanzaginsa ke yi ba zai yi nasara ba domin sai sun yi nadama

​Editan ​Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kungiyar dattawan PDP na Arewa ta caccaki ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, kan rikicin da ya addabi jam'iyyar.

Kungiyar ta zargi Wike da 'yan kanzaginsa da yunkurin ruguza jam’iyyar PDP da kuma raunana siyasar adawa a Najeriya.

Dattawan PDP sun yi zarge-zarge kan Wike
Nyesom Wike da shugaban PDP na kasa, Umar Damagum Hoto: @GovWike, @OfficialPDPNig
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar bayan kammala taron kungiyar karo na 18.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar ADC ta kori mataimakin shugaba da wasu manyan jami'ai 8, an fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dattawan PDP na son hadin kai

Sakataren kungiyar na kasa, Dr. Abbas Sadauki (Dan Madamin Tofa), ya bayyana cewa kungiyar ta yanke shawarar kare hadin kan PDP ba tare da rarrabuwar kai ba.

Shugabannin kungiyar sun sake jaddada cikakken goyon bayansu ga mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Umar Iliya Damagum, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar da labarin.

Sun kuma soki abin da suka kira yunkurin da wasu mambobin jam’iyyar ke yi domin hana gudanar da babban taron kasa da aka shirya a yi a Ibadan, jihar Oyo, a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba.

Dr. Abbas Sadauki ya bayyana cewa babban taron PDP zai gudana cikin nasara.

“Babu wata irin barazana, kazafi ko karya da za su hana gudanar da babban taron jam’iyyar a Ibadan cikin nasara."

- Dr. Abbas Sadauki

Ya zargi wasu daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) da yin aiki tare da wasu 'yan siyasa daga waje domin tada rikici a cikin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Bayan murabus daga PDP, ministan Buhari na kokarin 'hana' gwamna shiga APC

“Wadannan kungiyoyin na cikin jam’iyya da ke nufin kawo cikas ga babban taron kasa, ’yan wasan siyasa ne marasa kima, da aka turo domin kawo rarrabuwr kai."
"Wannan mugun nufin na su ba zai kare a komai ba face shan kunya da nadama."

- Dr. Abbas Sadauki

Wane zargi aka yi kan Wike?

Kungiyar ta kuma yi zargin Wike na kokarin lalata jam'iyyar ta hanyar amfani da mutanen da yake da su a cikinta.

Dattawan PDP sun zargi Wike da yunkurin rusa jam'iyyar
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Source: Facebook
“Abin takaici ne cewa wasu marasa godiya, karkashin jagorancin Nyesom Wike, suna kokarin lalata PDP da sauran jam’iyyun adawa."
"Ko da ta hanyar kotu ko amfani da iko ba bisa doka ba, manufarsu daya ce, su rusa jam’iyyar. Amma ba za su yi nasara ba."

- Dr. Abbas Sadauki

'Dan majalisar PDP ya koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta samu koma bayan bayan daya daga cikin 'yan majalisar wakilan da take da su ya fice daga jam'iyyar.

Hon Ojema Ojotu wanda ke wakiltar mazabar Apa/Agatu ta jihar Benue, sanar da sauya shekarsa zuwa jam'iyyar APC a hukumance.

Kara karanta wannan

LP ta gano hanyar da Peter Obi zai iya kifar da Tinubu cikin sauki a 2027

'Dan majalisar ya bayyana cewa rikice-rikicen da suka addabi jam'iyyar PDP ne suka tilasta masa raba gari da ita.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng