Bayan Murabus daga PDP, Ministan Buhari na Kokarin ‘Hana’ Gwamna Shiga APC

Bayan Murabus daga PDP, Ministan Buhari na Kokarin ‘Hana’ Gwamna Shiga APC

  • Wasu rahotanni sun bayyana cewa Gwamnan Bayelsa, Douye Diri, yana jinkirta sauya sheka zuwa APC saboda rikicin cikin gida
  • Majiyoyi suka ce ana rigimar ne tsakanin shugabannin jam’iyyar, ciki har da Timi Sylva da Heineken Lokpobiri
  • Jagororin APC sun tabbatar da cewa tattaunawa da Diri ta kai mataki mai nisa, suna cewa jam’iyyar a shirye take ta karɓe shi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yenagoa, Bayelsa - Ana ta yada dalilin da yasa Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, yake jinkirta sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Wasu majiyoyi sun ce hakan bai rasa nasaba da rikici tsakanin manyan shugabannin jam’iyyar a jihar wanda ke kara rikicewa.

Ana zargin ministan da kusa a APC da hana gwamna shiga jam'iyyar
Gwamna Douye Diri da ya yi murabus da tsohon minista daga Bayelsa. Hoto: Douye Diri, Timi Sylva.
Source: Facebook

Ana zargin an hana Diri dawowa APC

Rahoton Punch ya ce ana zargin tsohon minista Timi Sylva da Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri na kokarin hana Diri shiga APC.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bi sahun Peter Mbah ya koma jam'iyyar APC mai mulki? Gaskiya ta bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya haifar da tashin hankali a siyasar jihar, inda PDP ke cewa ficewar Diri daga jam’iyyar cin amanar dimokuraɗiyya ce.

Sai dai kuma jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ce tana cikin shirin karɓarsa cikin sirri a birnin Yenagoa da ke jihar.

Wasu manyan jiga-jigan APC sun bayyana cewa shirin sauya shekar Diri ya kusa kammala, suna cewa duk wani rashin jituwa da Sylva da Lokpobiri za a shawo kansa cikin lokaci.

Mataimakin sakataren shirya taruka na APC, Nze Chidi Duru, ya tabbatar da cewa jam’iyyar a shirye take ta karɓi Diri, tana mai cewa APC gida ce ga kowa.

Ya ce duk wani dan siyasa da ke son shiga jam’iyyar yana da cikakken ‘yanci, kuma jam’iyyar bata duba kowa bisa addini ko asali.

APC ta ce tana shirin karbar gwamna cikin sirri
Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa yayin taro a Yenagoa. Hoto: Douye Diri.
Source: Twitter

Martanin APC kan rade-radi kan Gwamna Diri

Sai dai mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Kudu maso Gabas, Dr. Ijeoma Arodiogbu, ya ce jinkirin Diri ya biyo bayan rikici tsakaninsa da mataimakinsa da kuma sansanin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Kara karanta wannan

Shettima zai taso daga Abuja domin karbar wasu manyan 'yan siyasar Arewa zuwa APC

Ya bayyana cewa shirin sauya shekar ya kusa kammala, amma Diri na kokwanto saboda matsin lamba daga wasu na kusa da shi a siyasa.

Rahotanni sun nuna cewa APC na shirin rushe shugabancinta na yanzu a Bayelsa domin kafa kwamitin riko wanda zai bai wa Diri damar zama jagoran jam’iyyar a jihar.

Sai dai tsohon lauya na PDP, Mark Jacob, ya bukaci Diri da ya ajiye mulki saboda ya bar jam’iyyar da ta kai shi kujerar gwamnati.

Ya ce rashin doka mai karfi kan sauya sheka ya sa ‘yan siyasa ke yawo daga jam’iyya zuwa wata ba tare da tsoro ba, cewar Tribune.

Lauyoyi sun magantu kan makomar Gwamna Diri

Mun ba ku labarin cewa lauyoyi sun rabu kan halaccin Gwamna Douye Diri na ci gaba da mulki bayan ficewa daga jam’iyyar PDP ba tare da shiga sabuwa ba.

Wasu lauyoyi suna cewa ficewarsa daga PDP bai sabawa doka ba, yayin da wasu ke cewa hakan na iya sa ya rasa mukaminsa.

Lauyoyi kamar Monday Ubani da Abiodun Olatunji sun ce kundin tsarin mulki bai tanadi cewa ficewa daga jam’iyya na kawo cire gwamna ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.