Tsohon 'Dan Takarar Shugaban Kasa a APC Ya Raba Man Fetur Kyauta ga Jama’a
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ya yi abin a yaba bayan rabon man fetur ga al'umma a Najeriya
- Majiyoyi suka ce Dr. Nicholas Felix ya dade yana raba fetur kyauta ga al'umma wanda hakan ke nuna tausayinsa ga jama'a
- An abbatar da cewa tsohon dan takarar ya dauki nauyin raba fetur din ne a karamar hukumar Oredo, Jihar Edo
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Oredo, Edo - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ya sha ruwan yabo bayan tallafawa al'umma a jihar Edo.
Jigon APC, Dr. Nicholas Felix, ya raba man fetur kyauta ga mazauna karamar hukumar Oredo, Jihar Edo.

Source: Facebook
Jigon APC ya yi abin a yaba
Rahoton Punch ya tabbatar da haka inda ya ce an yi rabon man fetur din ne ta hannun gidauniyarsa, (Dr. Nicholas Foundation).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da ake gudanar da raba fetur din a gidan man Shafa, Felix ya bayyana cewa wannan aiki yana gudana tun 2014 ba tare da wata alaka da siyasa ba.
Mutane da dama da suka amfana sun gode masa bisa wannan alheri, suna roƙon sauran ‘yan Najeriya masu hali su ma su taimaka domin rage radadin wahalar tattalin arziki.
“Mun dade muna yin wannan abu tsawon shekaru yanzu. Mun zo nan ne domin raba man fetur kyauta. Wannan abu ya fara ne tun shekarar 2014 a Amurka.
"Mun yanke shawarar kawo shi Najeriya, kuma babu lokaci mafi dacewa da wannan domin kara kwarin guiwa ga mutane, mu nuna musu cewa har yanzu akwai burin sauyi.
"Na san man fetur abu ne da kowa ke magana a kai tun bayan cire tallafin gwamnati. Don haka mu ka zo domin sanya farin ciki a fuskokin mutane. Kuna iya ganin masu babura da direbobin mota, suna murna sosai, wannan ne maƙasudin aikin."

Kara karanta wannan
Shettima zai taso daga Abuja domin karbar wasu manyan 'yan siyasar Arewa zuwa APC
- Nicholas Felix.

Source: Twitter
Kusa a APC ya fadi dalilin raba fetur
Nicholas ya kara da cewa wannan aiki ba shi da nasaba da siyasa inda ya ce idan lokacin kamfe ya yi za su ga abin da shugaban kasa ya yi, cewar rahoton The Sun.
Ya kara da cewa:
“Lokacin kamfen idan ya yi, za mu ga abin da Shugaban Kasa ya yi. Ba kamfen muke yi ba, kuma babu siyasa a nan.
"Mun yi haka a Ibadan a 2018; mun sake yi a nan Benin a 2019 da kuma 2024. Mun kuma yi a Etsako a Jihar Edo, haka ma a Jihar Neja da Abuja a watan Yuli. Don haka muna yawo da wannan aiki ne domin taimaka wa mutane.”
2027: Jigon APC ya magantu kan nasarar Tinubu
Kun ji cewa 'dan APC da ya nemi tikitin shugaban ƙasa, Nicolas Felix ya caccaki haɗakar ƴan adawa a inuwar jam'iyyar ADC.
Felix ya bayyana cewa duka ƴan siyasar da suka haɗa kai ba za su iya ja da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a 2027 ba.
Ya yi hasashen cewa Shugaba Tinubu zai yi nasara a zaɓe mai zuwa da ƙuri'un da ba su gaza miliyan 15 ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

