Adawa Ta Ci Karo da Matsala, an Kona Sakatariyar ADC Ana Shirin Babban Taro

Adawa Ta Ci Karo da Matsala, an Kona Sakatariyar ADC Ana Shirin Babban Taro

  • Miyagu sun kona ofishin jam’iyyar ADC bayan kai hari a ranar da ake shirin rantsar da sababbin shugabanni
  • Wutar ta lalata kujeru, rumfuna da wasu sassan ginin ofishin da ke titin Basiri, Ado-Ekiti da ke jihar Ekiti
  • Jam'iyyar ADC ta yi tir da harin, tana kira ga jami’an tsaro su kama masu laifi tare da gargadin ‘yan daba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ado-Ekiti - Wasu miyagu sun cinnawa sakatariyar jam'iyyar adawa ta ADC a Najeriya wuta wanda ya jawo asarar dukiyoyi.

Ofishin jam’iyyar ADC da ke jihar Ekiti ya kone kafin rantsar da sababbin shugabannin jam’iyyar a matakin jiha.

Matasa sun kona ofishin ADC mai adawa a Ekiti
Jigo a jam'iyyar adawa ta ADC a Najeriya, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

An farmaki ofishin ADC mai adawa a Najeriya

Wannan lamari ya faru ne yayin da ake shirin fara taron inda ‘yan daba suka kai hari suka kona rumfuna da kujeru, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kusa a APC ya ba Shugaba Tinubu shawara kan yajin aikin ASUU

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi suka ce yayin harin, wuta ya kona wani bangare na ginin ofishin jam’iyyar da ke titin Basiri, Ado-Ekiti.

Kadarorin da suka lalace sun hada da rumfuna 1000 da ke dauke da kujeru, da wasu sassan ginin da suka kama da wuta.

Rahoton The Nation ya ce yan jam’iyyar sun bayyana harin a matsayin na siyasa, suna kuma kira ga jami’an tsaro su binciko wadanda suka aikata laifin.

An kona sakatariyar ADC a Ekiti
Ofishin ADC ta aka kona da shugabanta, David Mark. Hoto: African Democratic Congress HQ.
Source: Facebook

Asarar da aka jawo bayan kona ofishin ADC

Yayin da ake jiran isowar shugabannin jam’iyyar daga Abuja don rantsar da sababbin shugabanni na jihar, magoya bayan ADC sun taru a wajen ofishin suna nuna damuwa.

Wasu daga cikinsu sun yi kira ga ‘yan siyasa da ‘yan daba da su guji aikata abubuwan da ka iya tayar da hankalin jama’a a jihar.

An tattaro rahoto cewa rumfunan da kujerun da aka kona an dauko su haya ne domin bikin rantsar da sababbin shugabannin jam’iyyar a matakin mazabu, kananan hukumomi da na jiha.

Kara karanta wannan

Rigima ta kunno kai a jam'iyyar hadaka, an dakatar da mataimakin shugaban ADC na kasa

Sa’o’i kadan bayan ofishin jam’iyyar ya kone, ‘yan daba suka sake taruwa suka farmaki wurin inda suka tarwatsa shirin da ake yi tare da kai hari kan shugabannin jam’iyyar da magoya bayanta.

An lalata motoci da babura da ke wurin, ciki har da wani babur mallakar ɗan jarida, yayin da rumfunan da kujeru suka lalace baki ɗaya ba tare da yiwuwar gyarawa ba.

Martanin da ADC ta yi kan lamarin

Sakataren ƙasa na ADC, Mista Rauf Aregbesola, ya iso wurin tare da tsauraran matakan tsaro, inda aka ci gaba da rantsar da sababbin shugabanni.

Da yake magana da manema labarai bayan kammala takaitaccen bikin rantsarwa, tsohon ministan ya la’anci harin da kakkausar murya.

Ya bayyana harin a matsayin abin kunya da ya ce hakan barazana ce ga dimokuraɗiyya.

ADC ta dakatar da mataimakin shugabanta a Najeriya

A baya, kun ji cewa majiyoyi sun ce rikici na neman sake barkewa a jam'iyyar hadakar yan adawa watau ADC yayin da ake ta shirye-shiryen zaben 2027.

Jam'iyyar ADC reshen jihar Cross River ta dakatar da Mataimakin Shugaban Jam'iyyar na Kasa (Kudu maso Kudu), Dr. Usani Usani.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: ACF da Afenifere sun aika sako ga sojojin Najeriya

ADC ta kuma yi fatali da nadin Jackie Wayas a matsayin mataimakiyar kakakin ADC na kasa, ta bukaci uwar jam'iyyar ta sake nazari.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.