Gwamna Ya Bi Sahun Peter Mbah Ya Koma Jam'iyyar APC Mai Mulki? Gaskiya Ta Bayyana

Gwamna Ya Bi Sahun Peter Mbah Ya Koma Jam'iyyar APC Mai Mulki? Gaskiya Ta Bayyana

  • Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya musanta labarin da wasu ke yadawa cewa ya fice daga jam'iyyar LP zuwa APC
  • Kwamishinan yada labarai na jihar Abia, Prince Okey Kanu ya tabbatar da cewa Gwamna Otti ba shi da shirin barin LP
  • Ya yi zargin cewa wasu yan siyasa ne suka kirkiro wannan labari na karya domin dauke hankulan jama'a daga nasaorin Otti

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Abia - Gwamnan Jihar Abia, Dr. Alex Otti, ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa cewa ya bar jam’iyyar LP ya koma APC mai mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya fallasa dalilin da ya sa gwamnoni ke tururuwar komawa APC

A cikin ’yan kwanakin nan, wasu rahotanni da ke yawo a kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa Gwamna Otti ya sauya sheƙa daga LP zuwa APC.

Gwamna Alex Otti na jihar Abia.
Hoton Gwamna Alex Otti na jihar Abia yana jawabi a wurin taro. Hoto: Alex C. Otti
Source: Facebook

Gwamna Otti ya bar LP zuwa APC?

Sai dai jaridar Vanguard ta tattaro cewa a wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Abia, Prince Okey Kanu, ya fitar, ya bayyana labarin a matsayin karya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya zargi wasu ‘yan siyasa masu son kawo rudani da kirkiro wannan labari domin dauke hankulan jama'a daga irin nasarorin da gwamnan ke samu tun da ya hau karagar mulki.

Kwamishinan ya jaddada cewa har yanzu Gwamna Otti na nan a cikin jam’iyyar LP kuma bai sauya daga matsayinsa na mamba mai cikakken biyayya ba.

Gwamnatin Abia ta soki yan adawa

Okey Kanu ya kara da cewa wannan jita-jita ƙoƙari ne kawai na wasu ‘yan adawa da ke son karkatar da hankalin jama’a daga ainihin cigaban da ake samu a jihar Abia.

A cewarsa:

“Gwamna Alex Otti yana nan daram cikin jam’iyyar LP, wacce ta bai wa mutanen Abia damar zabensa cikin ƙwarin gwiwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Gombe ta toshe kofar satan yara, ta ceto 59

"Mai girma gwamnana nan kan bakarsa ta mayar da Jihar Abia gida nagari, dawo da gaskiya da riƙon amana, tare da tabbatar da romon dimokuraɗiyya ya kai ga kowane ɗan jihar.”

Abubuwan da gwamnan Abia ya sa a gaba

Kwamishinan ya tuna wa jama'a kalaman Gwamna Otti a makon da ya gabata a shirin “Governor Alex Otti Speaks to Abians” na watan Oktoba, cewa ba shi da shirin canza jam'iyya.

Ya ƙara da cewa:

"Gwamnatin Otti na bin tsari na gaskiya da adalci, da ƙarancin ɓarnar kuɗi, ci gaban tattalin arziki, inganta matasa, da dawo da amincewar jama’a ga gwamnati
"Waɗannan su ne ginshiƙan da jam’iyyar LP ta gina kanta a kai, kuma Gwamna Otti ba zai taɓa barin waɗannan ƙa’idodi ba saboda wani dalilin siyasa.”
Gwamna Alex Otti na jihar Abia.
Hoton Gwamna Alex Otti a fadar gwamnatin jihar Abia Hoto: Alex C. Otti
Source: Facebook

Prince Okey Kanu ya roƙi jama’ar jihar Abia da su yi watsi da wannan jita-jita, yana mai cewa wasu gurbatattun yan siyasa ne ke neman dauke hankalinsu, in ji rahoton Punch.

Otti ya gargardi masu shirin magudin zabe

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Abia , Dr. Alex Otti, ya yi gargaɗi mai tsanani ga wasu ‘yan siyasa da ke da niyyar yin magudi a zaben jihar.

Kara karanta wannan

Bayan gwamnoni 2 sun fita, gwamnan PDP ya kawo karshen jita jitar zai koma APC

Gwamna Otti ya bayyana cewa ya samu bayanai cewa wasu yan siyasa sun lashi takocin kwace jihar Abia daga hannunsa a zaben 2027 ta kowane irin hali.

Ya ce nufin Allah da kuma ra’ayin jama’ar jihar Abia ne kawai za su yanke hukunci kan wanda zai lashe zaben mai zuwa, ba makirci ko amfani da karfin siyasa ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262