Shettima Zai Taso daga Abuja domin Karbar Wasu Manyan 'Yan Siyasar Arewa zuwa APC

Shettima Zai Taso daga Abuja domin Karbar Wasu Manyan 'Yan Siyasar Arewa zuwa APC

  • Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya na ci gaba da kokarin karfafa kanta gabanin babban zaben da ke tafe a shekarar 2027
  • Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe ya halarci taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar reshen jihar Filato wanda ya gudana a Jos
  • A wurin taron, APC ta kaddamar da kwamitin karbar masu sauya sheka domin tarbar wasu manyan yan adawa da suka bar jam'iyyunsu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Plateau - A shirye-shiryen zaɓen 2027, jam’iyyar APC ta jihar Filato ta shirya karɓar sababbin mutane da suka sauya sheƙa daga jam’iyyun adawa.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP da sakatarenta na ƙasa sun samu sabani kan takardar da aka aika wa INEC

Bisa wannan dalili ne, jam’iyyar APC ta kafa kwamitin karɓar masu sauya sheƙa ƙarƙashin jagorancin Pam Dung Gyang.

Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe.
Hoton shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe a wurin taron masu ruwa da tsaki a Jos, jihar Filato Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

Rahoton Leadership ya nuna cewa shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ne ya sanar da hakan a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Jos.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shettima zai karbi masu sauya sheka

Ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da kansa zai karɓi manyan ’yan siyasa da suka sauya sheƙa zuwa APC.

Wadanda za a karɓa a APC sun hada da tsohon Sanata mai wakiltar Filato ta Arewa, Barista Istifanus Gyang, da tsohon mai ba Gwamna Caleb Mutfwang shawara ta siyasa, Hon. Latep Dabang.

Tsohon sakataren kwamitin kula da ’yan gudun hijira (IDPs), Janar John Sura (mai ritaya) tare da dumbin magoya baya na cikin wadanda Shettima zai yi maraba da zuwa APC.

Yadda aka fara gudun PDP a Filato

A gefe guda kuma, jiga-jigan PDP a jihar Filato suna ci gaba da ficewa daga jam’iyyarsu, saboda rashin gamsuwa da tsarin shugabanci, in ji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

A kai kasuwa: APC ta yi watsi da 'yunkurin sauya shekar' gwamnan Filato

Wani babban jigon PDP, Nde Isaac Wadak, ya aika da takardar ficewa daga jam’iyyar zuwa ga Shugaban PDP na mazabar Kabwir Pada a ƙaramar hukumar Kanke.

A cikin takardar ficewarsa, Wadak ya nuna takaici kan yadda akidu da manufofin PDP na asali suka lalace a halin yanzu, yana mai cewa:

“Na shaida yadda ƙimar jam’iyyar PDP da akidun da aka kafa ta a kai ke rushewa. Aminci da gaskiya suna mutuwa, yayin da gurbatattun mutane da yan jari hujja ke cin karensu babu babbaka."
Tutar APC.
Hoton tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Getty Images

Wadak, wanda tsohon Babban Sakataren Ma’aikatar Kuɗi ne, ya ce yana cikin “Redemption Team” na tsohon gwamna Jonah Jang, kuma ya taka rawar gani wajen nasarar Gwamna Caleb Mutfwang a zaɓen 2023.

Ya ce shawarar barin PDP ta fito ne daga lamirinsa da abubuwan da ya yi imani da su, domin jam’iyyar PDP ta fara zama mara amfani a siyasar jihar Filato.

APC ta rufe kofa ga gwamnan Filato

A wani labarin, kun ji cewa jagororin APC a Jihar Filato sun bayyana cewa ba za su amince Gwamna Caleb Mutfwang na PDP ya dawo cikin jam'iyyar ba.

Kara karanta wannan

Zamfara: APC ta fadi gaskiya kan kafa kwamitin sauya shekar gwamna Dauda Lawal

Shugabannin APC na jihar Filato sun jaddadacewa Gwamna Mutfwang ba shi da wurin zama a cikin jam'iyyar, don haka gara ya ci gaba da zama a PDP.

Wannan matsaya na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da rade-radin sauya shekar wasu gwamnoni daga PDP zuwa APC.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262